HALIN GIRMA 10

“Nagode sosai, Ammi ta gode.”
“Ba komai.” Tace tana jin nauyi da kunyar yadda yayi
“Zan tafi, ki kula da kanki kinji? Karki yarda wani ya bata miki rai, kin fi karfin haka, ke din ta daban ce, ta musamman ce.”
“In Sha Allah.” Tace tana jin dadi , a kalla idan tana tare dashi tana jin cewa itama tana da yanci, sannan takai matsayin a so ta.
Ta cikin idon sa yake ta kokarin aika mata da sakon sa, sakon da yake so ya tafi ya bar mata, irin me zafin nan da zatayi wuyar dauke shi daga tunanin ta, sau daya ya samu nasarar aika mata da sakon, ya kuma je a yadda yake so, sai ya marairaice mata fuska yana jijjiga kansa.
“Allah ya kiyaye Allah ya kaimu lafiya.” Tace da sauri ta bud’e kofar kuusa da ita ta fice ta bar shi a ciki, dariya sosai ya saka, ya sake rik’e ledar hannun sa gam gam, ya fice yana jin sa tamkar yana yawo a cikin gajimare.
A kafa yake tafiya rik’e da ledar, iska na kada shi, sam baya jin komai baya ganin kowa sai tsadadden murmushin sa, shi kadai yasan yadda yake ji a lokacin, shi ya saka shi tafiya kawai ba tare da ya neme su ba. A chan bayan layin da suka saba haduwa suna tsaye tana masa mitar kwana biyu be zo ba, hakuri yake bata akan wata tafiya ce ta taso masa Muhammad din yazo wucewa
“Kaga saurayin Iman.”
Tace da sauri tana nuna masa shi. Wani kallo Bashir yayi masa daga nesan kafin yayi saurin juya bayan sa, yayi saurin bud’e motar ya shiga ciki, yayi kamar yana neman wani abu a ciki
“Baby me kake nema? Fito ku gaisa da Malam mana.”
Kin fitowa yayi ya cigaba da bud’e dashboard yana rufewa,
“Assalamu alaikum.” Moh yayi musu sallama yana karewa motar kallo.
A wani yanayi Bashir ya fito bayan nacin da Zeenat din tayi masa, ya diririce ganin Moh din
“Sannu ko?” Moh yace masa yana mika masa hannu
“Sunana Muhammad, kaifa?”
Yace masa, a sakale Bashir ya miko nasan hannun kamar me tsoro cikin rada rada yace
“Bashir.”
“Yayi Bashir, sai anjima.” Ya wuce ba tare da yace komai ba. Dariya Zeenat ta saka
“Shi wannan din kika ce shine zai auri Iman?” Yace da sauri
” In Sha Allah, baka ga sun dace ba? Ko baka ga yanayin su daya bane?”
” A haka yake tun zuwan sa gidan kuma?
“Babe me ta faru?”
“Noo noo babu komai.”
“Naga duk ka damu ne, me ya faru?”
” Ah babu komai, kawai na ganshi haka haka ne.”
“Dan ma baka ganshi sanda ya fara zuwa bane, tab!” Ta sake kwanshewa da dariya
“Abun mamaki.” Ya furta ba tare da ya sani ba.
“Abun mamakin gaske , mutum kamar wani mahau.”
“Keee.” Yace mata yana zaro ido, sai kuma ya waske da sauri
“Bari naje, ya kamata mama tayi tayi ya shawo kan Abba ina so na turo manya.”
“Ka turo kawai, ka bar komai a hannu na, bbu me min auren dole, wanda nake so zan aura babu me hanawa.”
“Toh shikenan.”
Sallama sukayi ya tafi itama kuma ta koma gida, tana shiga ta tarar da Abba a compound, ya tasa ta a gaba ransa a bace.
***Wani kallo da Maman tayi wa Iman lokacin da ta shigo ya saka ta shan jinin jikin ta, ta wuce bayan ta gaishe ta bata amsa ba, ta ajiye jakar ta sannan ta fito ta shiga kitchen ta sha ruwa ta dora ruwan abinci sannan ta fito falon, tana tsaye ya hade ran ta sosai, ta tsaida ita
“Uban waye ya baki izinin ajiye min wankin da na sakaki? Ka tafi?”
“Ubanta ne!” Abba da suka shigo tare da Zeenat yace, da sauri Mama ta juyo sukayi ido biyu dashi
***Ba karamin matse kaina nayi ba saboda na cika alkawari, kuyi hakuri babu yawa
[ad_2]