HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 13

“Duk wannan ta tunani ne Yaya Hajara, bamu da tabbas din hakan, kinga dai yadda Dr ya dage ya kamata ace kin bashi dama kinji ta bakin sa akai.”

“Kyale shi kawai, zai sakko ne.”

“Me yace miki?” Ta tambayi Zeenat din tamkar abin be dameta ba.

“Cewa yayi nayi masa alfarma na hakura da Bashir.”

“Ehen kinji? Har ya saukar da kansa a matsayin sa na mahaifi yace yana neman alfarma kema Yaya Hajara kinsan da matsala.”

” Me kika ce masa ke kuma?” Taki amsa atikar ta tambayi Zeenat din.

” Hakuri na bashi.” Tace tana rakubewa a gefen Hajiya da tunda aka fara maganar bata saka musu baki ba sai lokacin

” Gaskiya da kun hakura kun bi zabin Ibrahim, a kalla shi namiji ne yafi mu dukka tunani da hangen nesa.”

” Hajiya toh ya za’a yi? Lokaci ya riga ya wuce bata kula kowa sai shi, yaushe zata fara daga farko kafin ma ta samu saurayin su fuskanci juna a zo maganar aure.”

” Duk wannan me sauki ne akan ka dauki dan ka, ka kaishi inda zai Sha wahala.”

” It’s better to marry late than to marry wrong.” Atika tace tana girgiza kafarta

” Khair in sha Allah, babu abinda zai faru.”

Maman tace a kasan zuciyar ta tana jin tsoron abinda zai je ya dawo, ita kanta ta fara tsoron yadda Abban ya kafe ta tabbata akwai babban dalili, amma kuma ta Ina Zeenat din zata fara? Hasalima bata da farin jinin samarin duk asalin su Iman suke so sai ita maman tayi amfani da wannan a juya mata kansu zuwa Zeenat din dan ba zata iya gani Iman din tayi aure musamman auren babban gida ita kuma Zeenat din na zaune a gida. 

***Da sauri ya karasa part dinsa yana jin kayan na masa nauyi sosai, yau tun safe Bubu ya Aiko masa da kaya sannan ya bukaci ganin sa a kofar part dinsa dan shiga tawagar sa zuwa Fada, haka ya tashi ya shirya ba dan yaso ba ya fita. Tun lokacin sai yanzu ya samu dawowa part din sa, yana shiga ya hau cire kayan yayi wurgi da rawanin yana jin shi sakayau. Allah Allah yake ya samu feedbacks din aikin da ya saka Musaddik sai gashi kuwa ya kirashi adaidai lokacin, dagawa yayi yana rage daga shi sai singlet da boxer kasancewar zafi ya fara hurawa kadan kadan ba kamar kwanakin baya da ake sanyi sosai ba.

“Gani fa ga mutumin ka.” Musaddik yace yana dagawa

“Da gaske? Sharp sharp haka? Ok bari na kiraka Video Call.”

Ya katse sannan ya kira video call, a daidai saitin fuskar Bashir Musaddik ya saka wayar yadda yana dagawa Moh zai fara ganin sa. Yana durkushe tamkar me neman gafara, wata dariya ce ta zowa Moh, yayi murmushi kawai yace

“Oga Bashir barka da warhaka.”

“Dan girman Allah ranka ya dade kayi hakuri, wallahi bansan gidan da kaje Neman aure bane nima naje, wallahi kuskure ne kawai amma kayi hakuri.”

“Ai ba laifi kayi ba Bash, ni hakan yayi min dadi sosai, kuma ina tayaka murna, kaga ni da kai mun zama yan uwa tunda zamu auri yan uwa.”

“Tuba nake ranka ya dade!” Yace yana kasa da kansa

“Dago kanka bash, bafa wani laifi kayi ba, aiki nake so na baka, bana son kuskure ko kadan a ciki, idan har kayi min yadda ya dace akwai babban tukuiwaci.”

“Hakan shi yafi komai sauki a wajena ranka ya dade, fadi ko menene .”

“Yaushe za’a je tambyar maka auren?”

“Gobe ne ranka ya dade, amma idan kace a fasa na fasa wallahi.”

Girgiza kai yayi

” Ba za’a fasa ba, Ina so idan sun je su nemi a saka musu wata daya!”

” Wata daya!” Ya zaro ido

” Wata biyar nace ko shekara, ban shirya ba wallahi,dan dai bana son na rasata ne.”

” Ba zaka taba rasata ba, ni zan maka komai na auren tun daga lefe har gidan zama zan baka, ni dai kawai kayi duk abinda nace kayi.”

Dukawa yayi jiki na rawa

” Nagode nagode Allah ya kara girma, zanyi duk abinda kace, ba zan yi komai ba sai da sanin ka.”

” Good, yanzu aikin me kake?”

” Buga buga kawai, sai kuma aiken Hajjaju idan ya tashi.”

Dariya sosai Moh yayi, ya hangi tsantsar mutuwar zuciya da son zuciyar a tattare da Bashir din, mikar da yan yatsun sa yayi baya, ya dawo dasu gaba suka bada sauti kafin ya katse dariyar yana zama so serious.

” Abinda nake so kayi min, zaka ji daga bakin Musaddik, bana son kuskure ko kadan, komai Ina so ya tafi cikin tsari , Ina so gobe ka dauki hanyar Katsina, zan aiko maka da sako ka kaiwa Gimbiya Zeenatu, hakan zai sake goge shakku ko wani tunani akanka.”

” Nagode ranka ya dade, nagode nagode.”

” Karka damu, kai dai kayi abinda nace, bana son kuskure ko kadan!”

” Da yardar Allah zaka same ni da bin duk umarnin ka. ”

Daga masa kai Moh yayi sannan yace

” Guy!” 

” Yeah Captain!” Musaddik yace yana matsawa daga wajen da Bashir din yake

“Ka kula dashi sosai dan dan iskan kansa ne, duk da be isa ba, amma dai bana so a samu matsala har zuwa ranar daurin auren, watch him and report anything da be maka ba.”

“Karka damu, babu ma abinda zai faru. ”

” Yau nayi zaman fad’a, kamar nayi kuka wallahi, wannan yazo ya fadi yayi gaisuwa, wanna yazo ya ce makwafcin sa kaza, wannan suzo maganar aure, wannan ta kawo karar mijinta wannan ya kawo karar matar sa, maganar gado, kai abubuwan da mugun yawa, kamar na gudo nake ji, nasan iya zaman da zan Bubu ba zai raga min ba wallahi, har na fara ramewa. ”

” Haka zaka hakura kayi abinda yake so, iyaye dole a bisu ayi musu yadda suke so. ”

” Haka ne dama, shiyasa na matsu nayi auren nan nima na zama me yancin kaina, kasan aure fa yanci yake siyo ma da martaba ba komai Bubu zai dinga matsa min ba da zarar yaga nima na zama dan gari a harkar. ”

” A harkar me? ”

” Harkar auren mana, ina fita daga novice zai yanta ni, kwana kad’an kaji nima ana Daddy, Daddy! Wayyo I can’t wait. ”

” Kaifa yanzu baka da magana sai ta aure ko? Wannan sanyin ne ba komai ba. ”

” Sanyi ai ya wuce kuma, ba zan kara yarda na sake wani sanyin a gauro ba wallahi, haba Malam ai an ji jiki kawai. ”

” Dan air. ” Musaddik yace yana dariya

” Yan air dai, Wa ma ya kaika ne? Gwara ni wallahi kowa yasan uztaz. ”

” Nima haka ai. ”

” Fadawa wanda be sani ba toh. ”

” Toh ai idan har Moh uztaz ne toh tabbas ni sai da shehin malami, kai din? Ina dai tausayin yar mutane da zata shigo hannun tuzuru irin ka wallahi. ”

” Naji karka bata min tunani, jeka zan neme ka anjima bacci zan.”

” Hahaha, shikenan sai na jiki, angon Fatiti. ”

” Musaddik.!!! ” Ya furta da karfi

” Sorry sir, angon Fatima. ”

” Zaka shigo hannu ne wallahi, sai na saka an samin kai frog jump. ”

” Idan wannan ne ai na gaji da yi, a chanja wani punishment din dai Captain. ”

Kashe kiran Moh yayi, yasan ya biye Musaddik sai su cinye lokacin suna abu daya, wurgi yayi da wayar gefe ya kwanta dan rama baccin da Bubu ya katse masa.

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button