HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 14

” Kice manyan mutane ne suka zo? Bani labari Binta.”

” Ai Maman Habib baki gani ba, wallahi manyan mutane ne kamar ma daga wata babbar masarauta, yadda naga mazan gidan nan sun rikice kadai zaka gane ba kananun mutane bane, na zata ma na Iman ne ashe na Zeenatu ne, Baban Walid be min bayanin da zan gane ba kinsan wajen lokaci daya suka zo dukka.”

” Aikuwa sune, kai kice dai manyan mutane ne, masarauta fa? Kai masha ALLAH abu yayi kyau wallahi.”

” Ai Maman Habib ba karamin dace Zeenat tayi ba wallahi, Allah dai ya kaimu bikin nasan za’a ga lefe na ban mamaki.”

” Bari kawaii, sai muzo mu tanadi kyautar girma da zamu fita kunya, na gode da kika sanar dani dan Dr ba lallai ya fad’a min ba muna yar tsama dashi.”

” Ai haka suke, basa fadar cikin su wallahi, itama kuma Gajin ba zaka ji daga bakin ta ba tunda komai suna fad’a mata ai.”

Tabe baki Mama tayi

” Ai ni baki sani ba, so akayi a yi min bakin ciki.”

Sai ta rage murya

” So akayi fa a hana Zeenat auren Bashir din nan, kuma ina kyautata zaton akwai saka hannun Gajin a ciki, toh in ba haka ba yadda Dr ya rikice akan maganar lokaci daya zaki gane zugashi akayi.”

Kama baki Matar Abba Musa tayi

” Allah? Tab ashe an so yi miki tsakiyar da ba ruwa.”

” Ke dai bari, shiyasa na tsaya kai da fata, kinsan mutane basa son ka cigaba ko aga danka ya cigaba ko zai huta.”

” Zahiri, toh Allah ya kyauta, ban yi zaton hakan daga gareta ba.”

” Ai ba laifin ta bane, itama yadda aka dora ta haka zata tafi akai.”

” Eh kuma gaskiya, tunda kinga ai bata cika saka ido akan al’amuran mu ba.”

” Shine, koma waye kansa yayi wa, aure kam babu fashi.”

” Assalamu alaikum.”

 Iman tayi sallama ta shigo, gimtse fuska Maman tayi,ta gaishe su matar Abba musa ta amsa a sake tana tsokanar ta da amarya amarya, murmushin yake kawai tayi tana satar kallon yanayin fsukar Maman, zuwa tayi ta fad’a mata anjima zata tafi wajen dangin Mamanta amma ganin Matar Abba Musa ya saka ta fasa ta wuce kawai daki ta karasa hade koman ta waje daya.

  Bayan tafiyar Matar Abba Musa ne ta fito ta samu Maman a kitchen tana rarrabe kayan da tazo dasu dangin su kuka kubewa da daddawa waje daya

“Mama dama yau zan tafi gidan su Mamana.”

Tsayawa da abinda tayi, tayi ta kalle ta a mamakance tace

“Yau? Yaushe aka yanke  maganar tafiyar taki ban sani?”

“Dama tun ranar da na dawo daga gidan Ya Maryam Abba yayi min maganar.”

“Toh! Shi zai kaiki kenan? Ko turowa za’a yi kije? Ko da yake mutanen da basu damu dake ba yaushe zasu turo? Wannan din ma nasan dan Dr yayi magana ne.”

“A ah tare da Abban zamu je.”

“Kutmar Uba!” Da sauri Iman din ta ja baya dan yadda ta ga Maman ta birkice lokaci daya

” Ni za’a yiwa munafurci? Wato yace zai ganki saboda yaga tsohuwar matar sa ko? Dan an raina min wayo an maida ni wata sakarai. ”

” Dama… ”

” Dallah rufe min baki, wato gani shashasha an dauko raino an bani shine yanzu za’a nuna min bariki ko? Toh wallahi ba zata sabu ba wallahi kinji na rantse, ko ya barki ki tafi ke kadai ko ya hada ki da wani cikin yan uwansa ko Hafiz ne ma. ”

Shiru Iman tayi kamar ruwa ya cinye ta, tana jin sababin da Maman take kanta na kasa ita dai bata ce komai ba,me zata ce ma?

” Bari yazo naji abinda yasa zai munafurce ni wallahi, bayan duk kokaarin da nayi wajen rik’e ki amma sam yanzu baya gani, dan kawai yar matsala ta ratsa tsakanin mu shikenan sai ya rufe ni. ”

” Uwata zo ki wuce, kije waje kina da bako. ” Abba da yazo a lokacin yace yana kallon Maman, sum sum Iman ta fice kafin Abban ya dubi Maman cikin bacin rai yace

” Kin bani mamaki Hajara, ban zaci haka daga gareki ba.”

” Dama ai haka ne, duk abinda mutum yayi ba gani za’a yi ba musamman aka ce da ba naka bane, amma ai Allah ya gani. ”

” Bakya tsoron Allah kuwa in dai haka ne, har kece zaki ce Allah yana gani? Kina tsoron haduwar ku kuwa? Bayan wahalar da kika bawa yarinyar nan har kina da bakin magana? ”

” Wahala? Ita tace maka na bata wahala kenan ? Oh shine ka shirya zaka kaita wajen uwarta kenan bayan na gama cin wahalar ta, duk abinda nayi baka gani ba. ”

” Kiki tsoron Allah, na gano duk irin rikon da kika yi wa Ummi, kinci amanata kin ha’ince ni, Ashe ke din fuska biyu ce dake ban taba sani ba.”

” Da yake yanzu hankalin ka ya koma wajen tsohuwar matar ko, ko nace tsohuwar karu… ”

 A wani irin bacin rai ya daga hannu zai Kai mata mari, fasawa yayi yaji kamar an rik’e  hannun zuciyar sa na tafasa, ba ya cikin mazan da zasu daki matar su,baya kuma fatan hakan duk da irin yadda Maman ta bata mishi rai.

“Dukana zakayi Ibrahim? Dukana? Akan na fadi gaskiya, waya san auren da kukayi na gaske ne ko kuwa? Tunda mu dai babu wanda ya shaida, shine zaka dauki hannu ka dake ni akanta ko?”

Ji yayi kansa yana sarawa, be taba tunanin tashin hankalin mAman ya kai haka ba, juyawa yayi da nufin barin kitchen din amma sai yaji ta rik’e masa riga ta baya

“Wallahi ba zaka je wajen ta ba, wallahi ba zan yarda ba.”

Tsoro ne ya kamashi jin ta daga murya sosai, da sauri ya fizge rigar sa ya daga kafarsa wajen ficewa daga gidan ma gaba daya, ba zai biye mata ba, har a jisu a gidan abinda zai zamar masa abun kunya a wajen yan uwan sa .

  Shashen Gaji ya wuce da ya hango Iman tsaye da Musaddik a chan wajen gate din. Sako ya kawo mata daga Muhammad ya juya ita kuma ta koma cikin gidan.

  Tana shiga Mama dake tsaye a falo tana huci ta fisgota, saura kad’an ta fadi amma ta tsaya akan kafarta, kallon Maman take a tsorace dan bata dauka abin nata ya kai haka ba 

“Zan ga uban da ya isa ya fita daga gidan nan wallahi, wato kece munafukar kina so ki hada uwarki da ubanki ko? Toh wallahi baki isa ba na gama cin wahalar ki.”

Matsawa baya tayi ganin kamar dukanta Maman zatayi, kamar daga sama sai ga Habib kaamr an jeho shi, yayi saurin shiga tsakani yana wa Maman magana, 

” Lafiya Mama? Me tayi?”

Bata jira amsar Maman ba ta yi saurin ficewa.

   Abinda Abba ya guda sai da ya faru, magana har gaban gaji, mama ta dage ba zai tafi ba shi kuma yace bata isa ta hana shi ba, haka sukayi ta kai ruwa rana karshe ya je da kansa ya dauko kayan Iman din ya bawa Habib ya saka masa a mota sannan suka tafi tana kallo ta cigaba da haukanta.

***Jingina tayi ta rufe idonta a lokacin da suka shiga jirgin, karon ta na farko kenan shiyasa take jin tsoro tsoro amma ta dake dan da wuya kaga abinda zai sa kaga weakness dinta, rashin tsaron da ake fama dashi a k’asar ya saka Affan yi musu booking flight kawai zuwa Abujan dan ba zai yi risking tafiya da Iman din a hanya irin wannan ba. Lokacin ma da Moh yaji labarin tafiyar tata sai da yaji tsoro Allah yasa ba a mota zasu ba, dan har ya gama shirya yadda zai siya musu ticket din kawai ya aikawa abba amma kuma baya so a san shine sai kuma tace masa a jirgin zasu, hakan ya saka shi samun relief. Tafiyar su Dubai ya saka basa waya sai dai chatting dan kar tayi saurin gano shi. Da zata tafi ya saka Musaddik kai mata dubu biyar a cikin envelope, sai da ya jinjina kudin kafin ya aika, kyautar sa ta farko kenan amma sai yake jin kunyar kai mata, tana bukatar manya manyan abubuwa a wajen sa amma akwai sauran lokaci.

   Tunawa da tayi da envelope din ya sakata cirota a cikin handbag dinta ta bud’e, murmushi tayi ganin kudi ne sai wani dan karamin note an rubuta I love you da shape din heart a k’asa. Sosai taji dadin kyautar tayi ta kallon note din tana jin dadi sosai. 

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button