HALIN GIRMA 14

Cigaba da rikewa tayi a hannun ta har zuwa sanda zasu sauka sannan ta maida cikin handbag dinta tana jin wani irin feeling, she’s nervous bata san wanne irin tarba zata samu ba. Tana ganin sanda Abba ya dauko waya bayan sun sauka yayi kira.
“Mun sauka.” Taji yace sai kuma yave
“Owk tura min number shi.”
Suna tsaye ya sake duba wayar, number aka turo ta text message ya ciro ta ya kira ya fad’a masa yadda zai gane su kafin ya kashe yana cewa
“Ummi muje gashi chan ma.”
Matse jakar hannun ta tayi, taja akwatin ta zuwa wajen wanda yake nufo su.
“Welcome Sir.”
Yace cikin girmamawa, ba bahaushe bane jikin sa sanye da wasu uniform navy blue an saka number 5 a daidai aljihun.
“Thank you.”
Karbar kayan su yayi ya zuba a booth sannan ya budewa Abba gaban motar ya zauna ita kuma Iman ya bud’e mata baya sannan ya jasu suka fita daga airport din. A daidai wani hotel suka tsaya Abba ya juyo bayan ya kalli Iman yace
“Zanzo da safe in sha Allah, ki gaishe su, idan kina bukatar wani abu ki kirani.”
“In Sha Allah Abba, Nagode sai da safe.”
“Allah ya kaimu.” Ya fice ya rufo kofar ya tsaya daga gefe yana kallo suka bar wajen.
Ta cikin dark tinted glass din motar Iman take karewa garin kallo tana admiring ko ina musamman da dama magriba ta kawo kai dan wasu masallatan suna kokarin fara kiran sallah.
A wani babban gida cikin jerin gidajen Babbar unguwar nan ta Maitama yayi horn, a hankali gate din ya shiga zugewa har ya karasa budewa gaba daya. A gefe daya yayi parking kafin ya gama daidaitawa wasu mata su uku da wasu maza biyu suka fito ta wata kofa suka nufo su dukkansu fuskar su dauke da farin ciki mara misaltuwa.
[ad_2]