HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 18

    A hankali ta bud’e idon ta, tayi saurin rufewa ganin yadda nasa ya sauya sosai.

” Amm.. amm muje kaga su Mamma da yan uwan mummy, sai Gaji da sauran yan uwan Abba ko? ”

” Hmm. ” Yace yana jan ajiyar zuciya

” Tohm bari na kira Musaddik yazo. ”

Tashi yayi tsaye, ita kuma ta dukar da kanta k’asa, murmushi ta samu kanta da yi, tayi saurin katse shi ta sake saukar da kanta dan kar ya gani.

Dawowa su Musaddik sukayi, su Zahra da aka samu sabbin samari suka shiga ciki don sanar da shigowar su Mubamamd din.

   Ta bangaren Gaji aka fara, akayi hotuna sosai da kowa da kowa, sannan aka dawo in da su Mamma suke nan ma akayi musu, sai sauran mstan gidan da jikoki da sauran yan uwa da abokan arziki har ma da makwafta da suka shigo ganin kwaf.

   

***Yadda Zeenat ta koma zaka rantse tayi shekara tana jinya, gyaran gashin ma da aka yi duk ya hargitse kamar ba’a yi ba, ta tada aljanu yafi kala biyar duk da muryoyi kala kala akan suns gargadin in dai aka sake aka kai ta gidan sai sun kashe ta.

   Ko da Mama ta kira Abba ta fad’a masa cewa yayi karya ne, ya kashe kiran dan yana cikin mutane ne, amma kuma sai ya dinga jin babu dadi yana kuma tausayawa Zeenat din sosai, amma ya zai yi? Su suka jawa kansu duk da ba irin muna musu da be yi ba.

   Kayan kitchen su Aunty Maimuna suka dauka, suka kira Bashir din dan ba ma a samu damar zuwa an yi jeren kitchen din ba. Cewa yayi zai aiko a tafi dasu, ba’a dade ba kuwa sai ga wani saurayi yazo a golf irin ta hayar nan, dole suka saka Habib bin bayan su da wasu kayan bayan ya dauko yar kurkura dan yawan kayan kadai sun isa a yiwa wasu amaren biyu amfani dasu bayan Zeenatun.

   Sanda suka shigo unguwar gaban kowa ya hau faduwa, basu gama shiga masifa ba sai da suka ga kofar gidan da aka tsaida, katuwar kwatar dake kwance a kofar gidan ce ta fara tsorata su. Haka suka daure suka fito ya bud’e musu gidan suka shiga.

   Babban tashin hankali sanda suka shiga gidan suka tarar da kayan da suke gidan da Bashir din yace ya saka mata kaya kar ayi komai, su kansu kujerun bayan yadda aka daina yayin su, ba set bane dan babu three seater ko kankantar falon ya hanata shiga ko kuma ba’a yi da ita ba oho.

   Sanda suka shiga kitchen din sai da suka kusa kurma ihu, kwatan kwatan abinda Maman ta siya ba zai shiga kitchen din ba. Babu wanda yake wa wani magana a cikin su, suka saka abinda zai iya shiga kitchen din da ko kitchen cabinets babu, sauran na amfanin suka saka mata a cikin sip dan wannan ba za’a kirashi da wardrobe ba sai da sip???????? ragowar kayan suka juya dasu cike da tunanin yadda za’a kare da Mama. Babu maganar uban kayan turaren wutar da ta siya wajen hadaddiyar me turaren wutar nan*yerwa incense and more.*

     Shigowar su kenan suka tarar ana ta hotuna da Iman, jiki a sanyaye suka wuce bangaren Maman suna taraddadin yadda za’a kwashe. Mama ma jin ance sun dawo ta yi zumbur ta tashi, sai dai tun kan su gama zama ta san da matsala.

   Aunty Maimuna ce ta jata daki tayi mata bayanin komai sai ragowar kayan da tace an loda su a motar Aunty Muhibba dan kar a shigo dasu saboda yan saka ido.

   A k’asa dirshan ta zauna, ta cire dan kwalin ta da take jin yayi mata nauyin gaske saboda yadda kanta ke masifar sarawa

“Amma Bashir ya cuce mu, ya cuci rayuwata, yanxu dan Allah wannan abun kunya da me yayi kama? Na shiga uku.”

Ta jefar da hannun ta gefe,

“Be kyauta ba gaskiya, ha’inci ne wannan kuma, sam be kyauta ba.”

Aunty Maimuna dake kokarin bata baki ta fad’a duk babu dadi

” Allah ya isa ban yafe ba wallahi,shege macuci. ”

“Kiyi hakuri Yaya Hajara, cuta dai Bashir ya riga yayi mana ita sai dai muyi hakuri, mu lallaba a kai ta idan yaso daga baya idan hankalin kowa ya dauke sai musan abinda ya kamata. ”

Wani kallo tayi mata, kamar ma ta rufe ta da duka take ji

” Sai bayan an kai ta ya gark’ama mata ciki sannan ne kike tunanin zai rabu da ita? ”

” A ah Yaya, kinga wai ai dai yanzu daga daure aure yau ai ba za’a ce ya saketa ba, kinga hakan ai kema zai iya baki matsala da Dr. ”

” Matsala ta nawa kuma? Ni yanzu ya riga ya fita daga kaina, ta yata kawai nake, dole na bata farin ciki ko ta halin Kaka. ”

Shiru kawai Aunty Maimuna tayi dan ba kuma tasan yadda zatayi ta bawa Maman hakuri ba. Aunty Muhibba ce ta shigo, tace maman ta tashi ta gyara jikinta Iman da mijinta zasu shigo. Kamar ta danna ma Aunty Muhibban ashar taji dan dai akwai kunya tsakanin su kasancewar ta matar babban wansu, dole ta tashi ta wanko fuskar ta a bathroom ta shafa mai da yar hoda ta saka kwalli sannan ta fito.

***A zaune take ta tankwashe kafar ta akan dan carpet din da yake jikin gadon dakin, ranta a bace yake tun bayan da ta samu labarin auren da Yarima Muhammad zai, taso ta tada hankalin ta amma Kilishi ta hanata, yanzu gashi tana ji tana gani an daura.

  

“Laila!”

Ta kira sunanta tana daga zaune a gefen makeken gadon ta, da ido ta kalle ta ba tare da ta amsa ba, ta mike tsaye. Sanye take da doguwar gown ja, sai gashin ta da yake a tattare a waje daya da yasha gyara na musamman. 

“Yaushe zaki koma?” Ta ta da tambayar bayan tasan amsar da zata bata. Da ido ta sake dubanta, ranta na sake baci tace

“Na dawo kenan.”

Da sauri ta mike daga gishingid’ar da tayi, ta dauka zata ce mata soon zata koma kamar yadda take bata amsa a ko da yaushe idan tayi mata maganar komawar.

“Kinsan me kike cewa? Ba zaki koma ba? Me yasa?”

“Ba zan koma ba har sai na samu cikar burina. Ni ce na chanchanta da zama a wajen da aka bawa yar talakawa, wadda bata da komai da kowa. Yarima nawa ne ni kadai babu kuma wanda ya isa ya dakatar dani.”

“Har ni?” Tace tana zaro ido cikin mamaki

“Duk wanda yayi kokarin shiga hanya ta, ko waye kuwa, ko da Bubu ne!”

Tsam kilishi tayi a in da take tsaye ta kasa cewa komai. Tana son Laila tamkar yadda take son Kamal,sai da tafi son Kamal ya gaji ubansa akan yadda ita Lailan take so. Sai dai idan taga da gaske Kamal ba zai samu sarautar ba, toh zatayi duk yadda zatayi ta samu Laila ta shiga rayuwar Muhammad din. 

   Juyawa Lailan tayi cikin takun ta na isa, ta bar dakin. Da kallo Kilishi ta bita ta girgiza kai

“Ba zan taba barin ki da tsarin ki ba har sai na ga da gaske plan dina ba zai yiwu ba, wanda bani da shakku, Kamal shine zai gaji  ubansa a ranar da suka shirya bawa dan gatan dan nasu. Maimartaba da kansa zai yi fushi dashi, fushi irin wanda be taba yi ba!” 

Dariya ta saki ta koma ta zauna tana harda kafarta, indai tana numfashi Muhammad ba zai taba sarauta ba wannan alkawari ne da tayi wa kanta. 

****

    A gajiya Bubu ya dawo, shiyasa be samu ganin kowa ba ya shige turakarsa. Tun da wuri Ammi ta shirya tana jiran sa dama,aiko yana dawowa ta tafi dan tana so su karasa maganar da ya fara yi mata ranar basu samu damar gamawa ba

   Har ta karaso ta zauna be bar kallon ta ba, babu wani babban chanji akan sanin da yayi mata a dah da nayi yanzu, jikin ta me kyau ne zaka rantse bata ajiye garkamemen saurayi kamar Muhammad din ba.

“Barka da zuwa gimbiya a fad’ar Ahmadu.” 

Yayi mata kirarin da ya saba mata tun zamanin kuruciyar su. Dariya tayi ta zauna tana dora tray din da ta shigo dashi a saman table. 

“Sannu da zuwa, kun sha gajiya. An rabu da taro lafiya da kowa?”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button