HALIN GIRMA 24

Daga nan sai suka wuce bangaren Aji da Hajja, amma a mota saboda tazarar dake tsakanin bangarorn biyu, sosai taga karamci da girmamawa dan Adam, Hajja kamar ta goye ta saboda murna, ta dinga tsokanar ta da ta kwace mata miji da rana tsaka, murmushi kawai Iman din take, hakan ya janyo suka dade sosai a bangaren har zuwa sanda taji sallamar sa, ta dago suka hada ido sanda yake shigowa ciki, jamfa da wando ne a jikin sa kalar sararin samaniya, ya tsaya iya kar guiwar sa, kansa sanye da hula me kalar duhu, yayi kyau sosai, da sauri ta janye idon ta kunyar abinda ya faru daren jiya na hasko mata, murmushi yayi me kyau ya karaso ya zauna kujerar dake fuskantar ta. Hajja dake nade a saman wani cushion me laushi ta tabe baki tana dubanss
“Saboda rashin kunya shine ka biyo bayanta ko?”
“Toh ya zanyi? Kin rik’e min ita kin hanata tafiya.”
“Ah lallai, shine ka biyo baya kazo kaga ni, toh ba zan cinye ta ba ai.”
“Kai yar tsohuwar nan kin fiye rikici wallahi, kishi ne nasan yake damunki ba wani abu ba.”
Dariya tayi tace
” Ai na bar mata kai tuntuni, kuje ku karata nima Amadu na ya ishen.”
A tare duk suka yi dariya, ya kashe mata ido daya tayi saurin dauke kai kamar bata ganshi ba.
” My wife!”
Yayi kiranta a hankali karaf sai a kunnen Hajja, ta banka masa harara ya sosa kai
“Dan nema, kin hadu da aiki kinji Fatima, mijin nan naki bashi da kunya sam, bari kiga na tashi, taso yan mata muje na baki wani abu ki bar wadannan.”
Tashi Amaani tayi tabi Hajjan, suna shigewa yayi saurin komawa kusa da ita.
“Ka ganka ko?”
“Me nayi?” Ya tsare ta da ido yana marairaice fuska
“Gashi nan ka kori Hajja.”
“Rigimar tace kawai fa, mun saba irin haka da ita.”
“Toh ka koma chan ka zauna.”
” Wai kunya ta kike ji? Ko kunyar Hajja?”
” Both!” Tace tana kauda kanta
Murmushi yayi kawai
” Kinsan me? Bubu ya bani kwana hudu na kawo masa gamsasshiyar hujja, idan ban kawo masa ba, zai aura min Laila.”
Sak tayi, duk da Laila ta riga ta fad’a mata amma ji daga bakin sa ya sakata shiga yanayi,
” Karki damu, hakan ba zai faru ba, I promise you that!”
” Allah ya bada sa’a.” Tace a sanyaye
” Zan je Abuja anjima ko gobe da safe zanyi kwana biyu, na dawo”
” Tafiyar ba zata bamu matsala ba?”
” In sha Allah.”
” Shikenan, Allah ya kaimu ya dawo da kai lafiya.”
Tayi shiru tana tunanin yadda zata taimaka masa ta taimaki kanta dan ba zata taba iya zama da Laila ba a yanayin ta.
***Idan tace tayi bacci a ranar tayi karya, tun bayan fitar matar gidan da kawayenta bata sake nutsuwa ba, kuka take tun tana yi da hawaye har ya zama babu hawayen sai suya da zuciyar ta, take kamar zata fito. Da asubar fari taji ana buga kofar dakin amma a hankali, tashi tayi da k’yar tana jin jiri jiri saboda yunwar da ta kwaso ta zare sakatar dakin. Da sauri ya shigo ciki ya maida kofar ya rufe yana kallon ta, matsawa tayi baya tana masa kallon tsana
“Karka matso nan wallahi zan iya illataka, ka maida ni gidan mu wallahi ba zan zauna anan ba.”
“Rage muryar ki dan Allah, kar taji, kiyi hakuri zan yi kokari naga na lallabata ta bar mu, mu koma gidan mu dan wallahi a matse nake, kinsan dai mutum da sabuwar amarya.”
“Wallahi bazan koma ko wanne gida ba, gidan mu zaka mayar dani ka sake ni kuma, ba zan zauna da kai ba na tsane ka.”
Saurin damkota yayi, ya toshe mata baki yana hade jikin su waje daya
“Idan kina daga murya wallahi zamu dade a haka, idan ta gano na sato hanya nazo ni dake duk ba zamu fita ba, yanzu ki kwantar da hankalin ki, ki bita duk yadda tace zan dinga shigowa nan din da asubah tunda bata tashi da asubah sai gari yayi haske sosai.”
Fizge kanta tayi tana masa mugun kallo
“Na tsane ka, na tsane ka Bashir har bansan iya adadin tsanar da nayi maka ba, Allah ya isa cutar dani da kayi, kasan dama kana da mata amma shine ka auro ni, wallahi sai ka sake ni ko na jawo maka abinda zaka dade kana dana sani.”
“Baby!” Yaji muryar hajjajun tasa tana k’wala masa kira, jikin sa ne ya hau rawa yayi hanyar fita hankalin sa a tashe,kafin ya karasa ta turo kofar cikin shigar kayan bacci masu shegen kyau, tayi musu wani kallo kafin ta kama hannun sa tana murmushi
“Kana nan ashe, toh wuce muje ko?”
“Toh;” yace yana yin gaba.
“Ke kuma, ki fito ki fara min aiki kafin gari ya gama wayewa, akwai menu na kalolin abincin da nake son gani kullum a saman dining bana kuma so ki wuce karfe goma baki gama komai ba.”
Ta juya tana karkada mata mazaunanta ta buga kofar. Hawayen bakin ciki ne suka sakko mata, ta share tana shiga dan kurkutaccen bandakin da ke gefen dakin ta dauro alwala da k’yar sboda yadda yake wani shegen wari ta shinfid’a dankwalin ta, tayi sallah akai sannan ta bi ta hanyar zuwa kitchen din dan ta tabbata idan har ta sake muguwar matar ta dawo bata fito ba zata iya nada mata shegen duka babu abinda ya dameta gashi babu me kwatar ta dan shi kansa Bashir din ba abakin komai yake ba.
Menu din ta dauka tana kallo, babu abu daya daga cikin kalolin girke-girken guda biyar da ta iya a ciki, tasan dai tabbas Iman tana yi musu dukka a gida amma ita bata taba ko da sha’awar gwadawa ba, daga indomie sai tea sune kadai take yi, sai yar taliya ko macaroni shima ba kullum ba, duk wani girki me wahala kamar su tuwo da sauran su.
*_ZAFAFA BIYAR 2022????_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*????????????
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*????????
09134848107
[ad_2]