HALIN GIRMA 25

Halin Girma 25
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK????????_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK????????_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK????????_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK????????_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
***Ta dade a kitchen din tana jujjuya yadda zata yi, gashi lokaci na tafiya dan har kusan bakwai ce zatayi, barin kitchen din tayi ta wuce ta fara gyara falon, duk da ba wani datti da yayi amma sai da ta sake share shi ta bubbuge kujerun ta tattare komai ta ajiye a gefe har da rigar baccin da ta gani a jikinta dazu. Daga nan ta sake komawa kitchen din kawai ta yanke shawarar tayi abinda zata iya, ta dauki indomie ta dafa da egg sannan ta dafa ruwan tea ta jera musu akan dinning din ta wuce dakin da yake a mazaunin nata da tunanin yadda zata samu waya ta kira gida, ko kuma ta samu hanyar da zata bar gidan dan bata ga alamar Bashir zai kyaleta ta sauki ba.
Tana zaune tana sak’awa da warwarewa aka turo wata yarinya kiranta, kamar ba zata tashi ba, sai kuma ta mike tabi bayanta tana taraddadin abinda zata tarar. Matan jiya ne jere akan dinning din, sai uwar gayyar daga gefe ta hade rai sosai tana mata mugun kallo, tun kafin ta karaso ciki ta hau surfa mata ashar
“Saboda tsabar ke yar iska ce, abinda nace ki dafa daban abinda kika dafa daban ko? Zo nan.”
Kin zuwa tayi, ta k’ame a wajen tana kallon su
“Ji yadda ta tsare mu da ido Hajiya Lay, amma dai yarinyar nan bata da kunya.”
“Ku barta, bata san wacece Layuza ba, zan koya mata hankali.”
Bud’e baki Zeenat din tayi, tace.
“Ke nake aure ne wai ko shi?”
“Kutmelec! Ni kike wa wannan tambayar?”
“Toh ai naga dai iyaye na Bashir suka aura min ko? Me yasa kike nuna kamar ni din me aiki ce a gareki, ni bansan ki ba, bansan wacece ke ba kawai zaki dinga nuna iko akaina ”
“Lallai yarinya, kinyi babban kuskure da har zan fad’a ki mayar, toh dake da Bashir din duk a karkashi na kuke, kuma baki isa ki hada miji dani ba wallahi, kinyi kad’an ace kece kishiyata, dan haka yanzu baki da maraba da me aiki a gidan na, kuma dan ubanki dole kiyi duk abinda nace, na samu labarin komai da yadda auren ya kasance, shegen kwadayi da son zuciyar uwarki dake ya jawo miki, dan haka ki wuce ki yi abinda na saki kafin na taso na yi miki mugun dukan da zaki kasa tashi wallahi.”
” Ai da kawai daidaita mata shegen bakin nan nata akayi gobe ba zata sake fad’a ki fad’a ba.”
” Barta, zata gane kurenta.”
Zumburo baki tayi, ta ki barin wajen ita a lallai basu isa ba, ganin haka ya saka Hajiya Layuza tasowa aikuwa tana ganin haka ta kwasa da gudu bata tsaya ba sai data kai dakin tayi saurin saka sakata tana maida numfashi.
***Tagumi Mama ta rafka, duniyar gaba daya ta daina mata dadi tun bayan da ta tabbatar da babu wani abu da zata iya dan Abba sai da ya sake jaddada mata akan duk wani abu da ya samu auren Zeenat toh ta tabbatar da mutuwar nata auren, ada taso suyi duk wacce zasuyi amma daga baya sai tayi wa kanta fad’a ta hakura ta zuba wa sarautar Allah ido, gashi ta kikkira wayar Zeenat din amma ko da yaushe bata shiga, takanas ta tura Habib ya je har kofar gidan amma sai ya tarar a rufe, abinda ya kara daga mata hankali kenan, ta saka Abba a gaba tana kuka dole ya dauki waya ya kira Bashir din, ya kuma yi mata handsfree dan taji. Maganar an je an ga gidan a rufe Abban yayi masa nan ya shaida masa ai suna family house dinsu sai sun danyi kwanaki zasu dawo gida haka al’adar gidan su take, addua Abban yayi musu daga nan ya kashe yana kallon Maman da tayi tsuru tana ji har suka gama.
“Kin dai ji ko? Ko kuma address din gidan nasu zan baki?”
“A ah.” Tace a sanyaye tana mikewa. Cigaba da aikin gabansa yayi dan be ga dalilin da zai saka ta tada hankalin ta ba, bayan sun riga sun aurawa Bashir din basu da ikon bibiyar in da duk zai kaita.
***Zuwa yamma masarautar ta cika sosai, duk wanda Ammi ta gayyato sun hallara, yan mata ne kyawawa masu aji suka fi yawa sai manya tsirari wanda Ammi ta barsu sai ranar nadin dan kar ya zama an takure mutum, Ba’a dau lokaci aka shiga gabatar abinda ya tara su, saboda a ranar su Mamma suke so su wuce. Tsarin daban ne da duk wani taro da akayi na bikin, Muhammad da be niyyar attending ba, amma ganin abinda ya faru ya sakashi shiryawa cikin shigar da yasan zai burge Iman dinshi, wanda be san iya adadin yan matan da suka sake faller masa ba a ranar. Yana zaune kusa da ita daf ya dan karkace yana fuskantar ta, yana mata magana k’asa-kasa, tana jin sa sarai amma ta fuske dan ta gama gane shi so yake suyi abin da zata sha kunya dan taga kamar shi be san kunya ba sam. Daga nesa ba zaka gane yanayin da suke ciki ba, zaka dauka yanayin zaman nasa na mulki ne, sai ka matso sosai zaka gane kan abun. Shigar da Laila tayi a wajen ta kusan fin ta Iman din, babu laifi Allah ya hore mata kyau ba kad’an ba, dan sanda ta shigo wajen sai da gaban Iman ya fadi ganin uwar kwalliyar da taci kamar wata dawisu, kai tsaye wajensu ta nufo tana tafiya tana karkada kowanne lungu da sako na jikin ta, kamar bishiyar da iskar rani ke kadawa haka ta dinga karkada jikin ta har ta karaso wajen fuskar ta a washe ta matsa daidai saitin Capt Muhammad ta rankwafo tana nunawa camera man sign din ya dauke su.
Da ido Muhammad yayi masa alamar idan ya dauki hoton sai dai wani bashi ba, sum-sum ya bar wajen hakan ya bata wa Laila rai tace
“Capt wanne irin wulakanci ne wannan?”
“Baby kinga waccar da ta shigo yanzu?” Yayi kamar be ji ba, ya matsa jikin Iman din yana nuna mata wata,
“Kanwar Ammi ce, itace Aunty Fatima.”
“Ok wadda ka bani labarin ta ko!?”
“Yea ita.”
“Allah sarki, she’s nice.”
“Sosai.” Sai ya sake kai fuskar sa jikin ta sosai
“Baby perf din nan akwai kamshi, i just love it, yayi dadi.”
“Thanks dear.” Tace tana smiling
Bakin ciki ne ya tuke Laila, tayi saurin barin wajen kafin zuciyar ta, ta buga. Tana barin wajen sukayi wa juna murmushi.
A gajiye suka koma cikin gidan bayan an gama taron, su Mamma sun jima da tafiya dan haka part din Ammi aka maida ita, daga nan Ammi ta saka mutane da yawa suka yi mata rakiya zuwa nata part din da ta riga ta tare tun a jiya ba tare da Ammin ta sani ba, sai gobe za’a rakata wajen Bubu idan ta huta shi ma baya nan yau sai goben zai dawo.
Masu kula da bangaren da duk wani abu da ya shafe ta Ammi ta nuna mata, suna isa kuwa suka shigar da kayan su dakunan su dake bayan part din suka shigo suka fara aikin gyara shashen, suka gama suka saka masa turaren wuta sannan aka jere musu abinciccika masu rai da lafiya. Sai da suka tabbatar babu wani abu da zata bukata sannan sukayi mata sallama suka tafi.
A gajiye take sosai amma kuma dole tayi wanka dan sosai Mamma ta jaddada mata muhimmanci wanka da gyara jiki, cire kayan jikin ta tayi, ta zari towel daya ta daura ta nufi toilet din, wanka tayi ta hado da alwala ta fito tana sharce kanta. Wayarta ce tayi kara ta dauka tana dubawa, Mommy ce ke kiranta, tunda aka fara bikin basuyi magana ba, sai dai ta jisu da Mamma suna yi, zama tayi tana daga wayar dadi na cikata