HALIN GIRMA 6

*HALIN GIRMA* 6
*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*
_ASSALAMU ALAIKUM BEAUTIFUL PEOPLE!! ZAFAFA BIYAR FAMILY????????????????❤️_
_MUNGODE DA ZABIN LITTAFAN ZAFAFA BIYAR. ALLAH YA KARA BUDI YA KUMA BAR ZUMUNCI_
_KAMAR KO DA YAUSHE, WANNAN KARON MA MUNZO DA KOKON BARAR YOUTUBE CHANNEL DIN YARON MU, SUDEIS MASOYI KUMA MAKARANCI, MAHADDACIN ALKUR’ANI MA GIRMA_
_WANNAN KARON MA DAN ALLAH A TEMAKA ADANNA WA CHANNEL DINSA KARARRWA DOMIN KASANCEWA DA MU A DUK SANDA MUKA DORA FEFAN BIDIYON SA, A TALLAFA A KALLA A KUMA DANNA MASA SUBSCRIPTION. HAKAN NA KARAWA SUDEIS KWARIN GWIWAR SAKE DAGEWA YA KUMA KARA KAIMI WAJEN YIN KARATUN SOSAI. MUNGODE KWARAI????????????❤️_
_GA CHANNEL DIN DAKE YOUTUBE NAN????????_
https://youtube.com/c/sudaiskura
_Sudais is a young boy who has passion in recitation of the Holy Qur’an at a very young age._
_Please help him grow his YouTube channel by subscribing and liking his videos to encourage the little boy. Jazakumullahu khairan????????_
***
Girgiza kai ya hau yi da sauri da sauri.
“Habib aiki na, innalillah wa inna ilaihi rajiun.”
“Me ya samu aikin naka?” Mama ta matso da sauri tana rik’e shi
“Wai sun dakatar dani, babu wani kwakkwaran bayani kawai wai daga sama ne.”
“Innalillah wa inna ilaihi rajiun, zo ka zauna, rik’e shi Habib ya zauna.”
Zaunar dashi Habib yayi, yayi saurin dauko masa ruwa ya mik’a masa
“Sha ko zaka ji sauki a zuciyar ka, ba wani abu bane babba in sha Allah, wata yar matsala ce zasu gyara da yardar Allah.”
Jujjuya kansa yake ya kasa magana, shi kadai yasan hakan me yake nufi, shi kadai yasan yadda yake ji a halin yanzu, tabbas idan suka hana mishi aikin nan sun yi masifar cutar sa, akan me? Me yayi haka da ya chanchanci wannan hukuncin? Bayan irin kokarin da yake ganin ya rik’e aikin sa, tsawon lokacin da ya dauka kafin ya samu aikin, da irin wahalar da yasha kafin ya kawo matsayin da yake, sai yanzu? Daga sama ta ka kawai ace an dakatar dashi? Innalillah wa inna ilaihi rajiun. Ya sake maimaitawa.
“Kalle ni nan Khalil, karka ce zaka daga hankalin ka akan abinda kasan baka da iko dashi, kayi hakuri ka kwantar da hankalin ka, in sha Allah ba wata matsala bace, kaji?”
Gid’a mata kai yayi kamar karamin yaro, ya kwantar da kansa yana jin kamar ya zubar da hawaye saboda bacin rai. Shiru sukayi kowa yana jimamin abinda ya faru, ya ma manta da abinda yake shirin aikatawa. Shigowa Zeenat tayi dauke da wasu manyan ledoji,uwar ta bita da kallo bata ce komai ba.
“Daga ina kike?” Habib yace yana bin hannun ta da kallo
“Bashir ne yazo.”
Kallon Mama yayi, yaga ta dauke kanta
“Mama fa Bashir din nan naji wasu maganganu akan sa marasa dadi, ya kamata a duba sosai kafin a barta tana fita wajen sa.”
“Bana son maganar nan yanzu, dame zamu ji? Da abinda ya faru da Khalil din ko da naka zancen?”
Tsuke bakin sa yayi be sake cewa komai ba, ya tashi ya bar falon ma,
“Me ya samu Uncle Khaly din Mama?”
“Babu komai, ki wuce ki bani waje uwar yan magana.”
Da sauri tayi gaba da ledojin ta, ta shige dakin uwar ta rakata da kallo kafin ta sauke ajiyar zuciya tana tuna abinda ya faru daren jiya ita da Abban su.
***
“Ya ake ciki da yaran nan?”
“Name fa?”
“Akan maganar yaran da suke zuwa wajen su, Yaya yayi min magana akai yace ya kamata asan abinda ake ciki, kindai san tsarin gidan nan ba’a wani daukar dogon lokaci ana zance.”
“Eh toh, ita Iman akwai wani wanda yazo.”
“Zuwan sa biyu kamar ko?”
“Ashe ka sani?”
“Eh ina sane da komai ai, kinga alamun zasu dai-dai ta ne? Naga zuwan nasa biyu dududu.”
“Toh idan bashi ba waye? Babu kowa ai.”
“Khalil din fa?” Yace yana mata kallon mamaki
“Wai Dr bar maganar Khalil din nan, ba da gaske yake ba wallahi.”
“Ana wasa a maganar aure ne Hajara?”
“Shi dai yayi, gwara a tsayar da magana akan wanda yazo din dan da alama ba da wasa yazo ba.”
“Toh shikenan, Zeenatu fa?”
“Eh ita ai Bashir ne dama.”
Tashi yayi tsaye yana girgiza kansa
“Ban yarda ba sam, ban amince da yaron ba, binciken da nayi akansa be min dadi ba, kamar ance min ma kuma yana da mata duk da hakan ba zai hana a bashi aure ba, sai dai na samu labarin bashi da hali me kyau gaskiya, a wani labarin ma ance min har zaman prison yayi, sai ki fad’a mata nace banda Bashir ta kawo wani.”
Hankalin ta a tashe tace
” Amma baka ganin sharri akayi masa? Don a hana a bashi?”
” Akan me za’a masa sharri? Akan wanne dalili kenan?”
Ya tsare ta da idanun sa, sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, tsoron yadda za’a kwashe da Zeenat din take domin ta san yadda ta saka Bashir din a ranta, gashi babu laifi yana mata hidima sosai, hakan ya saka Maman sake yarda dashi da yar ta ta.
“Bari na shiga ciki Anty.” Khalil yace yana mikewa, ta daga masa kai kawai ya wuce ya barta tana cigaba da tunanin yadda zata bullowa al’amuran.
***Tana zaune a falon Gajin tana tunanin abinda ya faru tsakanin shi da Uncle Khalil, wayarta dake saman cinyarta tayi kara, ta kalli wayar ganin bakuwar number ya saka ta tashi, ta wuce zuwa bedroom din Gajin ta daga tana zama a gefen gadon ta
“Assalamu alaikum.” Tayi sallama cikin muryarta da tafi komai tafiya dashi, lumshe idon sa yayi ya bud’e a hankali ya amsa sallamar ta ta
“Wa alaikisalam…”
“Ina wuni?” Ta gaishe shi jin muryar sa
“Lafiya lou Mi Love, na barki lafiya?”
“Alhamdulillah.” Tace a kunyace ganin shi kai tsaye yake maganar sa.
” Kina jina Zahraaah na? ”
” Na’am?” Tace tana mike kafafunta
” A zahirin gaskiya ba da wasa nazo ba, da gaske nazo neman auren ki ba kuma naso a dauki wani dogon lokaci in sha Allah, ni din dai ba wani bane kin dai ganni, bawan Allah ne me neman amincewar Fatima Zahra, ina fatan zaki bani dama dan Allah!”
” Hmm…” Ta sauke ajiyar zuciya maganganun sa na taba ta, me zata ce toh? Da gaske take jin ya kwanta mata duk da taga alamun ba wani shi nne dashi ba, amma sai taji yadda yake abu kai tsaye ya birgeta sosai, babu karya straight kawai yake maganar sa, bayan haka da gaske take son matsawa daga wajen Mama, ko ba komai ta samu yanci itama.
“Baki ce komai ba?”
“Allah ya shige mana gaba, Allah ya zaba mana abinda zai zamar mana alkhairi gaba daya.”
Wani irin dadi yaji ya shige shi, ya rufe idon sa, ya dau yan sakanni yana jin sonta na sake ruruwa a zuciyar ta, yana tuna tsawon lokacin da ya dauka yana dakon soyayyar ta, a lokacin da shi kansa be san me ake nufi da so din ba.
Mahaifiyar sa ‘ya ce ga sarkin Kano kuma shi jika ne a gidan, hakan ya saka yake da alaka me karfi da garin na Kano duk da mahaifin sa da mahaifar sa Adamawa-Yola ne, rayuwar sa bayan ya tasa yayi ta ne tsakanin Kano da Adamawa, shiyasa babu in da be sanin a Kanon ba, yake kuma jin kamar yafi zama comfortably a Kanon, musamman da bashi da son hayaniya sosai sai nan din yafi zamar masa peaceful wajen hutawar sa.
Akwai ranar da ya fito shi da abokin sa Musaddik, suna tafe a mota hanya ta biyo dasu ta area din su Fatima, a lokacin ya ganta duk da lokacin ba ta kai yanzu ba, be kuma taba jin abinda yaji akanta, shiyasa ya nace a lokacin suka yi ta bin ta har suka ga gidansu, suka kuma yi tambaya akan ta da komai. A lokacin yaso ya shigo da karfin sa, sai dai wani labari da ya samu ya sauya masa tunani da shawara, ya kuma yanke ma kansa shawarar da yake ganin itace zata daga masa darajar ta, a ranar da gaskiya ta bayyana.