HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 6

  Musaddik be aminta da shawarar ba duba da gidajen da Muhammad din ya fito, amma haka ya kafe akan bakansa, shiyasa ma kawai Musaddik din ya kyale shi amma fa kullum cikin masa korafi yake.

   Bangaren aikin sa zai iya cewa yana cikin yan gata da sai abinda suka zaba da inda suka zaba zasu zauna, kasancewar gaba daya k’asar babu in da kakan shi mahaifin Ammi zai nemi alfarma ba’a masa ba, sannan gefe guda mahaifin sa yayi sunan da zaka yi mamaki sosai.

  Duk da hakan be daina aikin sa ba, sai dai babu wani matsi ko takura tun ma be kai matakin captain ba, balle yanzu da yake da rank me girma.

“Kinsan me?” 

Yace yana gyara kwanciyar sa sosai, sanda Musaddik ya murda handle din dakin ya shigo bayan yayi knocking ya bashi izinin shigowa.

“Ya Iman Abba na kira.” Marwan ya fad’a mata yana tsaye a gefen ta, hannun sa ta riko shi kuma yace

“Yaya Iman ki gaida min da Abba, idan kin dawo ki kira ni please, zan fad’a miki wani abu.” Murmushi tayi me sauti yana jiyo ta

“Ok bye.” Ta ajiye wayar ta rik’e hannun Marwan din suka fito a tare..

“Yaushe Abban ya dawo?”

“Be dade ba, yana falo yana cin abinci.”

“Owk.” Tace suna karasawa.

” Abba barka da gida.”

” Barka da Uwata, na dawo ban ganki ba, da zan fita ma ban ganki ba, shiyasa nace ya kira min ke.”

” Ina wajen Gaji Abba.”

” Eh haka maman ku tace, amma ai na ganki dai ko?”

K’asa tayi da kanta Mama ta karbe

” Tafi son zaman chan yanzu ai.”

” Kuna shan hira da Gaji kenan ko?” Yace yana murmushi

” Ko kuma tafi jin dadin tayi wayarta a chan ba, ko ‘yata?”

Maman tace cikin son a sako zancen Moh, shiru kawai Iman tayi Abba ma ya girgiza kansa kawai

“Allah ya kyauta, kinci abinci dai ko? Nasan ki da wasa da cikin ki.”

” Naci Abba.”

” Toh karbi nawa ki kara, nasan ba da wani yawa kika ci ba.” Ya tura mata plate din gabanta

“Maza kirawo min zeenatu Marwan.”

Gaban Mama ne ya fadi, ta zamo daga kujerar tana sakin salati a ranta. Tana gyara daurin dankwalin kanta ta shigo falon, ta zauna a kusa da Iman ta gaida Abban.

“Abinda yasa na kiraku ke da yar uwarki, akan maganar yaran da suke zuwa wajen ku ne, duk da shi wanda yake zuwa wajen Uwata bansan shi ba, inaso ki sanar dashi yazo yaga Yaya kafin ya cigaba da zuwa.”

Abincin da ta diba ta hadiye da k’yar gabanta na dukan uku uku.

“Ke kuma…” Ya nuna Zeenat

“Ki kawo wani daban ba yaron nan Bashir ba, ki sake dubawa a cikin sauran ki nemo wanda ya dace da nasabar gidan nan, me Halin Girma mutumin kirki, kinji na fad’a miki.”

Waro ido tayi cikin tashin hankali ta kalli Abban

” Hakan shine abunda ya kamata muyi a matsayin mu na iyaye, dan haka kiyi hakuri.”

Tashi yayi, ya kalli Iman da tayi tsam a wajen, ya juya ya kalli Mama yayi mata alama da ido sannan yace

” Na fita!”

Da k’yar Mama ta bud’e baki tace

” Adawo lafiya.”

” Allah ya kiyaye Abba.” Iman tace yana kokarin fita

” Amin.” Ya amsa kafin ya fice gaba daya.

Wani kallo Mama tayi mata, tayi kwafa ta mike sannan ta kalli Zeenat da ta soma kuka wiwi tace

” Ki same ni a daki.”

Kamar wadda zata fadi saboda kuka haka ta tashi, ta kusan fadowa Iman din aka, a ranta tana jin babu abinda zai hana ta auren Bashir, duk tashin hankalin da za’a yi sai dai ayi shi, amma babu wanda zai hanata abinda zuciyar ta take so.

***Cikin wani yanayi bayan ya gama jin komai ya gaida Abban da ya fito, yayi masa adawo lafiya sannan ya juya zuwa wata hanyar ya fasa shiga dakin. Idan har abinda yaji gaskiya ne, wannan me zubin yan boko haram din aka bawa damar turowa kenan, ba zai taba yarda yayi biyu babu ba, ba aiki ba Iman, shi zai fara isa wajen Yayan idan yaso ayi wacce za’a yi, yasan ba zasu taba hanashi ba, domin shi ya chanchanta ba wani bare ba, da ba’a san daga ina yazo ba.

***

Tashi zaune yayi zaune bayan ya ajiye wayar, ya kalli Musaddik da ya zauna a gefen sa

“Ya akayi ne?”

“Na shigo kana ta waya”

“Eh wallahi, ni da Wifey ne.”

“Wifey kuma? Yaushe kayi aure ba labari?”

“Bana son iskanci, kasan wa nake nufi ai.”

“Toh ai sai kace aljanar ka da ka nacewa, amma kace wifey bayan bamu shafa fatiha ba.”

Jefa masa dan pillow din da yake kusa dashi yayi

“Dan iska, ka jira ka gani ai.”

“Wai karo maka yaran ka akayi ne? Naga gate din naka ya sake cika ga wani uban iyayi kamar basu san mutum ba?”

“Sai hakuri kawai, ya ake ciki ne?”

“Normal, shiru ne ko ina, ya ka baro su Ammi?”

“Lafiya lou wallahi, Bubu yayi min maganar aure ai, nace zan zo musu da magana in less than a month, kafin nan mun gama daidaitawa da Wifey.”

” Ya zakayi toh idan aka ce ka turo?”

” Shine matsalar wallahi, amma zan san yadda zan dai.”

” Toh Allah ya sa muji alkhairi angon Fatima.”

” In Sha Allah.” Yace yana dafe saitin heart dinsa, dai-dai lokacin kiran ta ya shigo wayar, yayi saurin dora hannun sa akan baki alamun Musaddik yayi masa shiru, wurga masa pillow da ya jefe shi dashi yayi ya fice yana cewa

” Ka same ni a kasa idan ka gama zan kalli laliga.”

Da kai ya amsa masa yana kara kiran a kunnen sa

” Nagode sosai da kika kirani, na zata ba zaki kira ba.”

” Haba! Zan kira ai.”

” Nagode sosai, bari na kira ki toh.”

” A ah ba komai, muyi magana akwai kati kar a cinye maka naka kai kadai.”

Murmushi yayi me sauti

” Kinga kuma 200 nasa dazu har ta kusa karewa, bari na fita sai na sake siyo ko na 100 ne sai na kiraki.”

” Allah ba sai ka fita ba, ga sanyin nan da ake yi ma.”

” Shikenan Nagode.”

” Me kikayi a wajen Abba.”

” Abinci naci.”

” Iyeeeee, yar gata! Har abinci abba ke baki? Allah sarki ni.”

” Kaima ai dan gata ne.”

” Ni din? Tab ni ba dan gata bane, gashi ke har abinci Abba yake baki, niko kin ganni a dan shago na sanyin nan duk a kaina zai kare, babu me tausayi na ya bani abinci.”

” Allah sarki.” 

Tace cikin tausayawa, da ace sun saba sosai da tace yazo ya karbi abinci, ta hada masa har da abin rufar ta idan yaso ita sai ta samu wani wajen Gaji, amma ba zata iya ba, sai kawai tayi shiru tana tunanin ta yadda zata fad’a masa Abba yace yazo ya samu yayansa.

“Dama… Dama…Abba ne yace.”

“Me?” Yace cikin zakuwa

“Wai ka fara zuwa ka samu Abba (Baban yayansu) ka nemi izinin zuwa kafin ka cigaba da zuwa.”

“In Sha Allah zanzo, yaushe ake samun sa a gida?”

“Kamar da yamma haka zuwa bayan Magriba.”

” Ok in sha Allah zanzo, nagode sosai da wannan karamcin na Abba, duk da ni din ba kowa bane, amma har aka bani wannan damar, nagode Sosai.”

” Ni dai dan Allah ka daina cewa kai ba kowa bane, a islamiyya an fad’a mana, babu wanda yafi wani sai wanda yafi tsoron Allah.”

” Haka ne, wai kinga ina nufin ni din ba kudi ne dani ba, amma…”

” Kudi ba sune farin ciki ba ai, wadatar zuciya itace mutum, dan Allah ka daina wannan maganar kana sani jin wani iri.”

“An daina ta daga yau, ba zaki sake ji ba, kiyi hakuri idan na bata miki rai.”

” Babu komai.”

” Yawwa, kiyi min murmushi naji toh.”

Shiru tayi

” Kinji mana, pleaseee.”

Yace sai kuma yayi saurin daidaita kansa ganin zai zarme da yi mata shagwaba har ta ranfo wani abu

“Nayi fa, ai baka gani na.”

“Tam shikenan, idan naje na nemi izini wajen Abban mu, zanzo na gani a zahiri.”

“Uhum.” Tace tana jin zuciyar ta na sake nutsuwa dashi, ko ba komai ta samu wani da yake dauke mata damuwar ta da kadaici 

“Bari na barki haka kar na cinye miki kudi…”

“Goodnight, sweet dreams of meeeee.”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button