HALIN GIRMA11

” Uhum.” Tace dadi na kamata, a kalla ta samu wani da yake son ta sosai, irin soyayyar da ta rasa tun tana yar kankanuwar ta.
” Zan kiraki anjima, ki kula da kanki.”
” In Sha Allah. Ba-bye.”
Fadawa tayi saman gadon tana jin farin ciki matsananci
” Ya Allah ka sa ya zama alkhairi a rayuwa ta, Allah ka tabbatar mana da alkhairi.”
Ta furta tana jin kamar bata da saurin bakin ciki.
***Da karfin sa da kwarin guiwar sa ya isa masarautar su, wannan karon shigar da yasan Bubu yafi so yayi, shigar Manyan kaya da rawani, yayi masifar kyau ya fito a basaraken sa na ainihi, duk wanda yaci karo dasu sai sun kalle shi sun sake kallon sa, kai tsaye bangaren Aji ya nufa, domin wanchan karon be samu ganin Hajjan sa ba, shiyasa ya fara tachan dan tasan sai tayi korafi. Tana ganin shi kuwa ta hau murna, ta rasa in da zata sakashi, mace ce me jin mulki sosai domin mulkin a jinin ta yake dan har tafi Aji, amma kuma a duk abinda ya hada da muhammad bata hada shi da komai da kowa, da kanta take masa komai duk abinda yake so kuma shi take so ko da kuwa kowa ba zai goyi bayan sa ba.
Sai da ya gama mata shagwabar sa son ransa sannan ya gabatar mata maganar auren da yake so aje a nemar masa, murna a wajen ta kamar ta dauke shi ta goye haka taji, karshe ta dinga tsokanar sa da sauran idan amaryar tazo ya manta da ita, da tsohuwar zuma dai ake magani. Da haka ya wuce fada in da yasan zai samu Bubu wanda tuni labari ya riga ya kai masa, ya shirya yana dakon karasowar Muhammad din. Ganin sa ya saka Bubun farin ciki, musamman da ya ganshi cikin shiga irin ta gidan sarauta!
***Abba na zaune ya gama karatun alkur’ani me girma Maman ta shigo, ta zauna a gefen sa yayi kamar be ganta ba
“Dr wai fushin ne har yanzu? Be kamata ace abu irin wannan ya bata maka rai ba, yara hakuri ake dasu.”
Daga mata hannu yayi
“Bana son maganar nan, idan har ba zaki iya tankwara yarki ba, kuma ba zaki nuna mata dai-dai ba, shikenan, abinda kuke so kuka zaba zanyi muku.”
“Allah ya huci zuciyar ka, da anyi auren ma.in sha Allah zaka sauko, musamman idan kaga zaman nasu lafiya lou.”
“Allah ya taimaka.” Yace yana kokarin mikewa
“Dama magana nazo muyi, gida zanje.”
“Allah ya tsare hanya, ya kiyaya” yace kawai cikjn halin ko in kula
“Kwana uku zuwa sati nake son yi.”
“Duk yadda kika ga yayi miki.” Ya karasa ficewa. Kwafa tayi ta mike tana jin haushin sa. Ko me zaiyi ba zata hana Zeenat abinda take so ba, an wuce zamanin auren dole. Zai gaji dan kansa ya sakko.
[ad_2]