Hangen Dala 1HAUSA NOVEL

Hangen Dala 1

“Amma kamar fa fushi ake dani,tunda kwana da kwanaki ko kallona ba’ayi” a hankali ta daga kai ta dubeshi
“To meye damuwarka tunda kana da sabuwar tauraruwar da idan ta kalleka koda ban kalleka ba ta isar maka?” Dariya sosao ta kamashi amma ya danneta,wato kishin dai,kishi kumallon mata,idan yataso sai an amayar dashi,kai ya kada
“Ko kusa ko alama babu wata tauraruwa da zatayi dai dai dake halima,ke din ta dabance,yadda kika zama ta farko a zuciyata da rayuwata haka kike ta farko har yanzun,matsayinki bazai taba dai dai dana kowanne mace ba,kece kika fara sanin waje jibril,ke kika fara shiga rayuwarsa,kikasan dukkan wani sirri nashi,kika zauna dashi a yadda yake tun a lokacin,tota yaya matsayinki zaiyi daidai dana wata?,ummm?” Sosai taji wani sanyi yana sauka cikin zuciyarta,bata taba tsammanin cewa har yanzu tana da wannan matsayin da martabar a zuciyar jibril ba,ta dauka tuni an mata overtaking komai nata daga gareshi,ashe batasan akwai wata qima daraja da martaba da ita kadai ta mallaketa ba daga wajensa
“Sarautarki ta dabance ai halima” dole murmushi ya qwace mata,ta dinga jin wani nishadi da farinciki yana ratsata.

Sai da sukayi sallar la’asar anan sannan suka baro gidan zoo din.

A hanya ya dinga tambayarta me takeso?,to kusan bataga abinda takeso din ba harsai da suka baro hanya sosai sannan taga rake tace tanaso,ya tsaya ya siya mata mai yawa kuwa sannan suka wuce gida.

Bayan ya aje motarshi a muhallinta tana gaba yana biye da ita riqe da ledar raken,dai dai sanda zasu shiga dogon soron dazai kaisu ga tsakar gidansu amarya rufaida ta rako nata baqin zata juya sukayi kacibus,tabi mmn amir da kallo wadda ke tafe a nutse,sanye da doguwar rigar atamfa budaddiya sosai,kanta yafe da mayafin daya dace da atamfar,qafarta plate shoes ne sai qaramae jaka ta maqalewa a hannu data sanya wayarta da tarkacen magungunanta.

Ta ganeta sarai,amma banda bbn amir dake bayanta riqe da leda niyya tayi tayi shigewarta da sunan bata gane wacece ba,ledar hannunsa tabi da kallo,wani baqinciki na tokareta,wato saboda ya raina mata wayo daga cewa zaikai mata kudi shine yaje yayi zamansa harya buge da riqo mata leda kamar wani almajirinta?,dukka kwalliyar datayi da tanadin datayi masa saidaya goge ya salance?,ganin irin kallon datake musu yasa ya mmn amir yin sallama wadda ra maidota hayyacinta,saita dan dake tana amsawa ciki ciki,saidai fuskarta babu fara’a sam.????️‍????️????️‍????️ *HANGEN DALA*????️‍????️????️‍????️
_Ba shiga birni ba_

©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso ????

*BABI NA TARA*

 

Dukkanin idanun rufaida nakan bbn amir tana dubanshi,ranta a bace yake sosai saboda bata tsammaci zai mata haka ba,ta yaya zaice mata zaije yanzu yadawo amma kawai saita ganshi da matarshi?.

Saita maida kanta ga mmn amir tana qare mata kallo,wannan baqar matar ma zatafi mata sauqin gamawa aiki,saita zarce da qaremata kallo,saidai bayan baqin bataga wani abu na kushe tattare da ita ba,duk da cikin dake jikinta yasauya wasu daga cikin halittarta,amma mmn amir din black beauty ce ciki ya sanyata baqi,tana da idanuwa da hanci mai tudu na wani siriri mai tsini bane can,cikin dai yasanyashi budewa,duk da cikin jikinta batayi wata qiba ta azo a gani ba,duk da ta qara kauri,bata tsaho hakanan ba gajeriya bace,tana da yalwar gashin gira.

“Sannu amarya” mmn amie ta fada saboda yadda taga rufaidan ta xuba mata idanu,saita dan basar sannan murya ciki ciki tace
“Yauwa sannu” ta fada kamar batasan fuskan mmn amir din ba,bata kulaa ba hakanan bata damu ba tasoma qoqarin rabeta tawuce tana cewa
“Ya kwanan baqunta?”
“Lafiya lau” tasake fada ckki ciki,batako waiwayo ba ba bare tasan meke wakana tashige cikin gida abunta.

Da sallama tashiga tsakar gidan,tana iya jiyo surutun yaran daha dakinta,dakin mmn ummi labulenta na asake kamarma babu mutum cikin dakin.

Sunajin muryarta yaran gaba daya suka fito suna mata oyoyo
“Kuyi haquri karku kayar dani” ta fada tana murmushi itama,sau tari yaran sukan debe mata kewa da sakata walwala,sun shiga ranta sosai har takan damu da lamuransu fiye dana jama’ar gidan,da yaranta dana mmn ummi kusan dukansu kamarsu daya,hakanan tana musu kallon yaranta,shi yasa kome zatayi musu tanayi ne kamar ita ta haifesu bata banbantasu da natan.

Da qyar suka barta ta qarasa falonta,tazube kan kujera cike da gajiya,salima na mata sannu da zuwa ta amsa tana dubanta sannan tace
“Me aka dafa yau a gidan,yunwa yunwa nakeji” dan tabe baki kadan salima tayi sannan tace
“Babu abinda aka dafa,suma gari na basu suka siyo da kudin da kika barmin muka jiqa muka sha” cike da mamaki take dubanta
“Gari kamar yaya?,bayan store dinmu cike yake da kayan abinci”
“To mmn ummi dai bata girka komai ba,amarya ma snacks ta baiwa baqinta dasu alkaki na gararta” shuru mmn amir tayi,tana mamakin halayen maryam din duk da baqinta bane,amma daga bisani ta rage wasu da zama yayi zama,shine yanzu takeson dawowa dasu?,rasa abun fada tayi har zuwa wani lokaci kafin tace
“Allah ya kyauta yarufa asiri,tashi kijr kitchen din,ki jawo qaramin gas dina ki dora mana indomie”
“Yeeyy,umma dama yunwa nakeji tun dazu,nagayawa mamana tace naje abba yabamu abincin” cewar usman da bashi da wani cikakken hankali ko wayo,saita dora hannunta saman kanshi
“Ba haka take nufi ba kaji usmanu,yanzu za’a dafa muku indomie kuci” kai ya gyada mata,saita bisu da kallon tausayi,daidai sanda amir yashigo da ledar rake ya aje mata
“Ga kayanki inji abba”.

Jawo ledar tayi gabanta,ta bude ta rarrabawa yaran,itama tadauki wani tasoma sha ko zata rage yunwar da takeji,take kuwa dukkansu suka nutsu,kowa yasamu waje yazauna yasoma shan nasa sunata surutu.

Fuuu rufaidan tayi dakinta,yabi bayanta bayan ya baiwa amir ledan mmn amir din yace yakai mata.

Zaune yasameta kan hannun kujerarta rungume da hannyenta a qirji,ta cika tayi fam kamar zata fashe,dankwalinya gana goshinta,saiya zagayo yazauna kan kujerar da take zaune din,zumbur tayi zata miqe yacafke hannunta,ya kuma jawota ya riqeta gam,cikin fushi da bacin rai tace
“Sakanni jibril,aini wallahi ka bani mamaki,cikin kwana saya tal amma inata ganin abubuwan da ban tsammata ba daga wajenka,babu abu guda daya tal daka iya cikamin shi sai abubuwa kala kala,tun daga dare zuwa wayewar gari,daga wannan sai wancan”
“Haba mana amaryata uhumm?,kiyi haquri ki tsaya ki saurareni,nikaina bansan dukka abubuwan nan zasu taso haka ba,idan kin duba duka lalura ce,ni mutum ne me iyali dole nakula da haqqin kowa nakuma saukeshi,idan kika duba mmn amir kema wataran haka zata kasance akanki,zakiso nayi burus dake naqi bin lamuranki?” Saita kalleshi sosai
“Sai kuma akace ka dauki lokacina duka ka rabawa matanka da yaranka?” Shima sosai ya dubeta,duk da yanason shawo kanta ne amma hakan bai hanashi cewa ba
“Au…rufaida abunma babu kara,matana dai amma yara ai namune gaba daya ko?” Saita dan yatsina fuska tana jin takaici har cikin ra ta
“Sorry,ka fusatani ne,yaranmu to”
“Daga yau ba za’a sake ba kinji,haba amarya fushi baya miki kyau” ya fada yana lakace mata hanci,tanason jibril sosai,dole yasaki murmushi,sannan tashigar da qorafinta nabiyu
“Kuma sannan jibril baka isa da gidanka bane ko kuma dama haka ake zama da yunwa a gidanka?” Fuska yadan tsuke yanajin tambayar banbarakwai,tun tana gida dama yana dan fama da ita kan rashin iya magana,wani lokaci idan tayi wata maganar sai kaji kamar mecin kashi
“Kamar yaya?,wacce iriyar maganace wannan?” Gyara zamanta tayi sosai sannan tace
“Dole na fadi haka,yau babu abinda naci sai snacks da nazo dashi daga gidanmu,koda nayi baqima ka duba kaga abinda nabasu” tafadi taba numa mishi kwanukan da bata kwashe ba a wajen masu dauke da kayan gararta da lemo data bayar aka siyo mata a shagon layin
“Ba’ayi girki ba?,tome yaran sukaci?” Ya fada yana jeho mata tambaya,saita tabe baki wani takaici yana qumeta,wato bata ita ko baqinta yake bama,ta yaranshi yake?
“Oho” ta bashi amsa tana sake tabe baki
“Ina zuwa” ya fadi yana miqewa kana yafice,dariya tasaki tamiqe zuwa cikin bedroom dinta tana cewa
“Allah yasa ta kwabemusu,shegiya naga ta shegen daukan kai yau ai”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button