Hangen Dala 1

Kwalin taliya ne dana indomie,ta farke taliyar taciro guda daya ta karya taxuba,ta ciro miyar nama data saka salima tayi mata daga fridge ta dora saman botikin da take tafasa taliyar donta dumama,cikin mintuna kadan tagama,taxuba tazauna sosai taci ta qoshi,saidai tana cidin taba tunanin su usman,sam bataji motsinsu ba,kodon ta rufe qofarta ne?.
‘Yan halak kuwa tana gamawa saiga usman din yashigo,ta dubeshi sosai,fuskarshi qayau qayau da alama ma ba’a mishi wanka ba,ga jirwayen hawaye nan layi biyu kan fuskarshi
“Umma zanci” ya fada yana kallon sauran taliyar data rage
“Bakaci abinci bane?” Kai ya gyada mata
“Mama bata gama ba,tun daxu nakejin yunwa saita dakeni wai ba yanzu zata dora ba” mamaki ya kamata,wai wanne irin banzan haline mmn ummin ta tsiro dadhi,yaran nata take hadawa suda ubansu take musu horo gaba daya?,wannan ai shashancin banza ne da wofi,su yara me suka sani?,tana qara dasa rashin jituwa tsakaninta dasu bata sani ba,da alama bbn amir ya turasasata zatayi girkin ne,shine ta qulla muguntar qin dorawa da gamawa da wuri,banda haka gidan tunda mmn ummi tazo itama tasamu tsarin gama abinci da wuri saboda yara,haka tsarin mmn amir din yake,itama haka tazo tasamu ta dora akai,amma ace har uku na rana na neman gotawa amma ace ba’a gama girki ba?.
Da wadan nan tunane tunanen ta xuba ma usman abincin,tana zaune bayan tasha ruwa tana kallonshi yana cin abincin a yunwace hannu baka hannu qwarya,nan da nan yagama da abincin,ya nemi ruwa tabashi yasha,saiya bingire yahau bacci.
Ranar wuni tayi sur dakinta babu inda ta leqa,don bata da abinda zatayi a wajen,bata fito ba sai bayan sallar magariba,bayan tayi wanka ta sanya daya daga cikin dogayen rigunan atamfofinta,duk daba kwalliya tayi ba amma tayi kyau,tana ta qamshin turare,ta kama hannun usman wanda sai sannan yatashi a bacci,ya tsula fitsarinsa ta sake masa wanka saboda haka tayi nufin kaishi wajen mamarshi tasauya masa kaya.
Tsakar gidan nasu babu kowa sai hasken wutar lantarki,dayake haka unguwar tasu take akwai lafiyar samun wuta,sukanyi kwana uku da ita,shi yasa take cinikin ruwa da lemonta sosai,banda bikin nan da akayima da tuni ana sintitin zu siya,saidai tana tunanin gobe ko jibi zata koma sana’arta.
Duban tsakar gidan take adan kaikaice saboda yanayin tsaftarsa da tsarinsa bai mata ba,ba’a wani share yake fes yadda take masa ba,hakanan tawuce tana furta Allah ya kyauta,tadaga labule tashiga dakin mmn ummi.
Tana zaune falon tana shafa mai,da alama wanka tagama,ta daga kai fuskarta ba yabi ba fallasa ta amsa sallamar tana ci gaba da shafa manta.
Tana daga tsaye tasaki usman ya isa wajen mamarshi yaxauna yana gaya mata umma ce tayi masa wanka
“Wanne irin bacci kayi haka usman?” Ta tambayeshi tana dubanshi
“Ki barshi da yunwa ba dole yayi bacci ba,da kika hana yara abinci ke aisaiki hada kici” ta fada tana jefa mata harara,don sam ta kasa hadiye takaicinta,ta tsani a cuci yaro,shida bai gama sanin ciwon kansa bama bare na wani.
Dubanta mmn ummi tayi kawai batace komai ba tana ci gaba da shafa manta,itama saita juya tafice daga dakin,tana fitowa tanufi nata dakin tajiyo dariyar rufaida daga soro,saiga bbn amir na biye da ita,riqe take da hularshi,taci kwalliya da qananun kaya.
Sarai taga mmn amir na fitowa,hakan kuwa yayi mata dadi sosai,saboda haka ta tsaya anan tasoma shagwaba tana bubbuga qafafu kan saiya dauketa.
Shi sam baiga mmn amir din ba,saboda haka ya sungumeta,tahau kuwa qyalqyala dariya cikin jin dadi,bai ankare ba saidaya kusa da dakin rufaidan sannan yaga shigewar mmn amir dakinta da rufe qofarta,ya sauke rufaida da hanzari yana fadin
“Subhanallah,ashe matan gidan suna kusa” fuska ta turbune sannan tace
“Su waye matan gidan?,naga nima matar gidance,kuma kawai saboda wasu saika kama ka saukeni bayan baka qarasa dani ba” ta fada fuska kicin kici,cikin nuna fushi tayi gaba tashige dakin,yabi bayanta da hanzari yana kiranta.
Washegari mmn amir din tana zaune dakinta tana karyawa,yauma kamar jiyan bata leqa waje b,bbn amir din yashigo dakin cikin shirin fita kasuwa,ya kasa hada ido da ita saboda abun jiya,bayan sun gaisa yahau kame kame
“Kin zama hajiyar daka ko?,haka kawai kin koramin yara daga gida” kofin da take shirin kaiwa bakinta ta dakata ta dubeshi
“To ko aje a daukosu?” Ta fada cikin gatse gatse,don itasam bata sha’awar yaranma su dawo gidan nan kusa,saboda ta fuskanci take taken rufaidan,ko dazu tana jin ihunta daga daki,shima kuma yasan sarai sunji,abinda yasake sakashi kunya kenan,kuma ba wani abu yayi mata ba,kawai dan tsere ne haka da ba’a rasa ba na sababbin ma’aurata ya kamota shine tasaki wannan ihun,shi kansa abun yabashi mamaki don baikai tayi ihun ba
“Ni na isa,inna fa akai kaiwa su,aita isa damu gaba daya” shuru yadan ratsa don bata sake ce masa komai ba,sai kuma yayi gyaran murya
“Ni zan fita,ko akwai wani abun?” Kaita kada kawai tana ci gaba dashan shayinta
“Shikenan,saina dawo”
“Allah yatsare” ta amsashi a taqaice.
Har yakai qofa sai kuma tasake cewa
“Amm jimana” waiwayowa yayi yana dubanta,shi kansa sai yakejin wani shakka shakkarta yadda ta tsare gida,hakanan vabu wani abun magana da mutum xai tankata dashi,ta ga abubuwa amma kamar bata gani ba,taji amma kamar bata cikin gidan
“Don Allah kome zai faru kayi qoqarin kula da kiyaye tarbiyyar yaranka,don dukkaninsu sun taso,sannan kowanne da irin baiwa da kaifin basirar da Allah yabashi,so kome zai kasance yadinga zama cikin tsari da kiyayewa idanun yaranka” yasan magana ce tayi masa mai harshen damo cikin hikima da fasaha ba tare data kama sunan kowa ba,ya kuma fahimci inda tadosa,donko shidin yasoma wannan tunanin,saiya gyada kai
“Gaskiyane,nakuma gode da wannan tunasarwa uwar gida sarautar mata,Allah yayi albarka”
“Amin” ta amsa can qasan maqoshinta,saiya saka kai yafice daga dakin.
Daga nan dakin mmn ummi yanufa,don dama yakanbi girma girma ne,zaune yasameta itama ga abun karinta ta saka a gaba,saidai bata taba komai ba,sai usman da mubarak dake karyawa abinsu.
Qafarta na dore daya saman daya tana karkadata,kana kallonta sau daya zakasan akwai abinda ke cin zuciyarta kuma tanason ta amayar,da qyar ta iya amsa sallamarsa kamar wadda aka shaqe takuma bishi da banzan kallo,bai wani lura ba harsai daya gama biyewa yaranshi yana yiwa ummi wasa sannan ya dubeta
“Mun tashi lafiya” yasoma gaidata maimakon ita ta gaidashi
“Gashi nan kaga alama”
“To madalla” ya fada a taqaice,tunda yaga yanayinta da yanayin gaisuwarma yasan wani abune kuma na daban,bata rabo da qorafi sam a rayuwarta,kullum cikin matsala daga wancan sai wannan,shi yasa bai fiya jimawa a dakinta ba,hakanan ko ranar girkinta ba wani doguwar hira suke ba idan ba ita taso ba.
Da dafari sanda yake dokinta yana ganin tafi mmn amir iya komai saboda karatunta ya dara nata bai ganin illa da aibun dukka wadan nan halayen nata,saida tafiya tayi tafiya sannan ya tantance tsakanin aya da tsakuwa.
Yana dire ummi yace
“Xan fita,akwai wani abu?” Ya qarashe zancan yana dire mata kudin cefane,da harara tabi kudin kafin ta maida dubanta kanshi
“Wallahi wallahi kana bani mamaki jibril,bansan rainani dakayi dukka cikin matanka yakai haka ba,ku gama tiqa dariyar kaida waccar me zubin karuwan,kashig dakin mmn amir ka kusa kashe minti goma sannan nika shigo a wani tsaitsaye kabani kudin cefane,wato bauta itace aikina ko?” Yaran yaduba,baison wani cecekuce gabansu,wanda wannan dabi’ar mmn amirce takoya masa ita,da fari bai dauki hakan a bakin komai ba,sanda yake ganiyar neman auren mmn ummi yakan iya fadata da fada gaban yaran,koya caccaba mata maganganu,iyakaci tayi shuru,idan sun mata zafi da yawa tayi kukanta ta goge hawaye.