Hangen Dala 1

Daga can dakin mmn ummi kuwa usman ne ya wurgar da cokalin hannunsa yana yarfar da hannun gamida dalilen yawu saboda azabar yaji,mubarak kuwa tuni idanunsa sun hada qwalla donshi yafi usman ma qin abinci mai yaji,dai dai sanda mmn ummi tafito ashirye bayan tayi wankan da masifa ta hanatayi daxu ta dubesu
“A’ah,wannan wanne irin iskancine wannan?,me haka?”
“Yaji umma” usman yafada yana shirin fashewa da kuma,saboda yunwar da yakeji yaso yaci abincin sosai amma babu hali
“Wanne irin yaji?” Ta fada tana zama gefansu,gamida daukar cokalin tayi loma daya ta dandana
“Um,um_um,umum” ta fada tana gyada kai
“Tabdi” ta sake furtawa,ita abun ya mata dai dai,domin kuwa tasamu hanyar cin zarafin rufaida a daren nan,zata qarasa huce takaicinta,saita dauki kwanon abincin tace
“Ina zuwa” fuuu tayi dakin rufaida.
“Garin yaya rufaida abincin nan yayi yaji haka?” Ya jefa mata tambayar yana kallonta,sauke wayar tayi ta dubeshi
“Yafi dadi ai,abinci babu yaji kamar na ‘yan ruwa?”
“Amma dai nasha gaya miki ba’amin girki mai yaji ko?,saboda ulcer da basir,ga kuma yara”
“To nidai gsky haka na iya girki na” kafin yace komai mmn ummi ta bankado labulen tashigo riqe da kwano a hannu
“Wannan wanne irin abincine haka?,bbn amir kaga muguntar da matarnan tashirya ashe ko?,to gashinan dai yara sun kasa ci,babu abinda suke sai kuka,wannan ai mugunta ce da rashin mutunci”.
Da sauri rufaida tamiqe rana aje wayar hannunta
“Ke maryam ki iya bakinki ki kama kanki,kibar ganin ina daga miki qafa wallahi tausayinki nakeji,banason hauka banason dabbanci kinji ko?,banson jahilci da qananun maganganu…..”
Sakin farantin mmn ummi tayi ya tarwatsewa rufaida a daki,ta daki qirjinta tana cewa
“Waye jahilin waye dabba?,wallahi yau saikin gayamin….”
Tsawa bbn amir ya daka musu wadda ta tsaidasu daga yunqurin da kowacce takeyi.
“Waiku wadanne irin mutanene da basu qaunar zaman lafiya sai tashin hankali” cikin raunin murya mmn ummi tace
“Nice bana qaunar zaman lafiya ko ita?,kana gani yautun safe da kalar wulaqancin da takeyi cikin gidan nan amma banga wata cikakkiyar tsawatar mata da kayi ba,yanzu wannan zancan danazo dashi shine rashin qaunar zaman lafiyar?”
“Da kika shigo baki ganni ba zaune?,me yasa baki mutuntani ba kin kawomin qara kigani mezanyi akai?”
“Meko zaka iyayi tariga tashanye ka tamallake ka,sai abunda taga dama takeyi”
“Ya isheni maryam,wuce ki koma dakinki” yafada cikin bacin rai yana nuna mata hanya da yatsa,ta fuskanci yana dab da kaiwa maqura,saboda haka ta juya tana cewa
“Ni duk wanda ya cuceni Allah ya isa wlh,kuma kuyi lokacinku ne,akwai ranar qin dillanci ranar da hajar mai gari ta bata” da wadannan qananun maganganun tajuya ta fice.
Tsahon mintina falon yadauki shuru,saiya dauki ummi yafice,ya direta a qofar dakinsu ba tare daya shiga ba yajuya yafice daga gidan.
Da sauri rufaidan ta qarasa gaban kwanon abincin daya tashi akai tadauki cokalin tayi loma daya,saita hau zaro idanuwa saboda yaji da gishiri,itakanta batasan yajin da gishirin sunkai har haka ba,yaron daya kai mata markden dai yace tarage attaruhun tace haka takeso,yakai mata haka,saita koma tazauna tana jin yadda shinkafar ta tsaitsaya mata a maqogaro tana raba idanu,tare da da tunanin yadda zata nade tabarmar kunyarta.
Can bayan layinsu ya zagaya wajen wani maisaida fura da noni,gefansa kawai mai balangu,ya siya leda daya mmn ummin da yaranta,leda daya mmn amir don yasan bazata iyaci ba itama don bata qaunar yaji,leda daya tashi,yadawo gidan yashiga dakin mmn ummin,tana zaune ita daya,yana iya jiyo motsin yaran cikin dakinta,ya aje ledar yana dubanta
“Maryam,ki fita daga idanuna,banason fitina banason tashin hankali,ki kiyaye tun baki kaini bango ba” daga haka bai saurareta ba yafice yashiga dakin mmn amir.
Fuskarta ba yabo ba fallasa ta amsa sallamarshi,itama yamiqa mata ledar idanunshi nakan farantin dake aje gefanta tarufeshi da wani farantin,da alama itama tadebone ta kasa ci,ya tsammaci zatace wani abu,saidai batace komai ba har ya mata sallama yafito.
Cikin ranshi yadinga ganin qima da martabarta,har kullum kunya sake kamashi take idan yatuna abinda ya aikata mata a baya,sanda yana kan ganiyar neman aure da aurenshi da maryam,yakanji kamar yajawo baya yagoge duk abinda yafarun a baya,saidai babu damar haka,saidai danasani da hausawa ke cewa qeyace.
A baya idan tayi kawaici irin wannan yace munafuncine dason goga masa baqinjini wajen mutane,idan tayi magana yace tacika qorafi duk da ba maganar takeyi ba,duk wanda tayi bata tsira ba,sai a yanxu martabarta take sake fitowa muraran,darajarta take sake yauqaqa a idanunsa.
Wannan karon dakinsa yakoma,yayi shirin kwanciya abinsa kana ybude gurasa balangu da furar yasoma ci.
Baiyi nisa ba taturo qofar dakin cikin kayan barcinta tashigo dauke dai da kwanukan abincin,donta tsara abinda zatayi,dubanta kawai yake takaici yasauko masa,rigar barci ce transparent ana iya ganin pant da bressier dinta,amma ace haka ta ratso cikin gidan zuwa dakunanshi?,yanzu idan wani cikin yaran yaganta fa?.
Sai data aje abincin sannan ta bata rai sosai tana dubanshi,baqinciki biyu,yasiyo abinsa yanaci ba tare daya bata nata ba,sannan ga girkin datasha wahala akanshi baici ba
“Yanzu haka xakamin dear,wallahi na fuskanci an riga da an gama shiga tsakaninmu,randa nasoma girkina na farko ace kaqici ka bige dacin abincin kan titi?”saita fashe da kukan kissa wanda yadinga jinsa har saman kanshi,wannan matsaloli da yawa suke,daga ka toshe matsalar waccar saita waccar ta danno kai?,daga wannan sai wancan?.
Ganin kukan nata nayin yawa yasa dole bayan ya kammala cin abincin yakira sunanta,tadago da hawayen qarya tana dubanshi.
“Gaba daya rufaida kin bani mamaki,yadda na tsammata gaba daya ban tadda haka daga gareki ba,na zaci cewa zan sake samun wani nutsuwar da kwanciyar hankaline daga gareki,sai gashi kina neman bani mamaki,ina shirin ganin abinda ba haka ba daga gareki” fuska tadan yamutsa,saboda babu abinda zancan nasa suke mata sai bata mata rai,itafa arayuwa babu wanda ya taba mata kwatankwacin abinda jibril din yake mata yanzu,donko saurayi magana daya zai gaya mata yanzu ta sauyashi,bata lamunci a dinga gaya mata magaba kai tsaye ba
“Kaman yaya?”
“Kamar yadda nake gani” ya bata amsa shima kai tsaye
“Yanxu duk qoqarin da nakeyi kai baka gani,baka yabamin saima kusheni da kawo matsalolina,duk yadda nake haquri a gidan nan baka gani ba?” Ta fada cikin kuka,don ita harga Allah bata gano laifinta ko daya ba,sai tarin laifinsa dana matansa
“Tunda hakane saika fadi dame dame nake maka”.
Tiryan tiryan ya lissafo mata komai,saidai cikin zuciyarta tsaki take ja kawai,tanason maida masa wata zuciyar na kwabarta,saboda tana lissafe nan da rana ita yau zata amshi kudin ankon bikin qawarta,kuma taji daga bakin qawayenta masu aure,idan kika sake wani abun ya hadaku yana iya hanaki kema abinda kike buqata,saboda haka ta faki idanunshi ta yatsina fuska sannan tace
“Shikenan naji,xan gyara”
“Da dai yafi,saboda na auroki ne don dukkaninmu munason juna,na auroki don dukkaninmu muyi farinciki datarayyarmu da juna har lahira,abu nabiyu,irin wadan nan kayan banaso kina yawo dasu cikin gida haka,saboda yarana da sauran masu shigowa wadanda suke ba hurammanki bane,a qa’ida ta addini bai kamaci ace suna ganinki haka na,bugu da qari tarbiyyar yaran gidan,kinsan yaro da riqe abu da fahimta,bare kusan dukkaninsu sun riga dasun tasa,balaifi zaki iyamin ado dasu sanda muke daga ni saike,don Allah ki lura ki kuma gyara” wani abune yasake tsaye mata a wuya,kusun uba,waime jibril yake nufi ne?,kwalliyarma da zata ringa da qananun kayan zai hanata,abinda taci vuri ta kashewa kudi,aqalla ita kanta batasan nawa ta kashe wajen siyan kayayyakin ba,gaskiya ba zata sabu ba wai bindiga a ruwa,bataga uban wanda ya isa ya hanata shigar datayi niyya ba cikin gidan,wannan shine babban abinda zata daina suyi galaba muraran a kanta,ba shakka dole ta rage mishi son yaran nan ba,idan ba haka ba ita za’a cutar da yawa,kuma akwai dambarwa ba ‘yar qarama ba,amma a fili saita cuno baki
“To naji” kai ya girgixa cikin mamaki,wasu lokutan halayanta kanyi kamanceceniya dana mmn ummi,mmn amir ce mace daya tak dakan saka gwiwoyinta a qasa ta bashi haquri a duk sanda tayi masa laifi.