Hangen Dala 1HAUSA NOVEL

Hangen Dala 1

Da wannan tasamu tasha kanshi,komai yawuce,don dama shi bamai daukar dogon fushi bane ko a baya,idan yayi dogon fushi to tabbas ka qureshi ne.

**** **** ****** *****

Washegari hakanan badon taso ba tatashi da wuri ta dafa mishi shayi da chips,kamar xata fadi haka ta dinga ji saboda tashin wurin datayi,haka ta dinga aikin takaici nacin ranta,saboda tariga ta saba a gida bata tashi a irin wannan lokacin,suma sun sani ba’a tashinta sai sanda taci baccinta ta gyatse,ko aiki zaiwa mamanta kanta kuwa ba ruwanta,idan ta tashinma batason aikin wahala,zata karbi aikin da zatayi daga zaune ne,shima idan yadauki lokaci saita kawo wani uzurin da zata aje aikin ta barshi.

Bayan ta sallameshi saida ta koma takwanta din kuwa,bata tashi ba sai bayan goma na safe,yara tuni sun soma jin yunwa,tadora shayi a gurguje ta dora musu indomie,ta jibagata ta sauke sannan tashiga sharan gidan,wanda kafin tagama ta jigata ainun,haka ta dinga qorafi da surutai ita kadai,yaran kuwa duk wanda yayi kuskuren yin wani abu ba dai dai ba zaici gyatumarsa.

Mmn amir ce data fuskanta tayi hikimar tattare yaran a dakinta,don tasan tabbas idan mmn ummi ta fuska ta to yauma sai an raba abun fada,itakuwa sam batason tashin hankali,uwa uba kuma tasan hankalin jibril xai tashi fiye da jiya,abinda ita kuma bata fata kenan.

Haka taci gaba da karbar aikinta harna tsayin kwana biyu,wanda kafin sannan ta jigata qwarai,ta zaci abun akwai sauqi bata tsammaci haka ba,randa zata sauke girki tanason ta huta amma tana tsananin kishin miqawa mmn ummi jibril,babu yadda ta iya haka tasaki mmn ummi ta kama,saidai taci alwashi itama kafin mmn ummin tafita saita baro musu bacin rai.

Tunda gari ya waye ranar da zata karbi girkin take cikin walwala da farinciki,bini bini minti daya biyu kaji ta saki waqa wadda ke cike da habaici da baqar magana,sosai ran rufaida yabaci don ta gama yankewa da ita mmn ummi take,tayi qwafa ta quduri abinda zata mata ta huce yakai sau shurin masaki.

Mmn amir kuwa batasan ma me suke ba,tana kwance abinta tana duba wasu daga cikin litattafan marubuta masu ma’ana,sosai takejin dadin karatun,don tana qaruwa da abubuwa a ciki ba kadan ba.

Bayan yagama shirin fitarsa daga dakin rufaidan,yasoma leqa mmn amir din,tana zaune tafito da duka kayanta tana gyarawa da safen kasancewar bata da wani aikin yi,lemon siyarwar ma ta dakata dayi harsai ta sauka,sai ruwan pure water kawai da take saidawa yanzu,tanason bayan tasauka dinne tasake fadada sana’artata,ta qara wasu kalolin lemon da sauran abubuwan sanyi nasha.

Jin shigowarshi yasanyata fitowa falon nata
Kamar koyaushe suka gaisa ya tattambayeta jiki tace alhmdlh
“Idan nadawo ku shirya zamuje mu dubo hajiya bata jin dadi”
“Ashasha,me ya sameta?” Ta tambaya cikin nuna damuwa
“Ciwon qafarta ne yatashi”
“Ayyah,Allah ya sawwaqe ya bata lafiya”
“Amin ya rabbi” ya amsa yana sanya hannunshi cikin aljihunsa.

Dubu guda yaciro
“Kekam kawaicinki kamar yaso yayi yawa”batasan sanda murmushi ya subuce mata ba,kana tace
“Name fa?”
“Indai ba asibiti zakije ba,ko kin qure da yawa bazaki bude baki kice bbbn amir bani kaza ba,yanzu yadda baki girkin nan baki samun ‘yar biyar da ‘yar naira goma ya kenan?” Murmushi tasaki kawai ta kada kai,babu mutumin da zaice baison ace mishi ungo,to amma idan ya kasance bake daya bace wajen miji,sa’annan bani baninki tayi yawa to babu shakka zakifi kowa baqinji ne a cikinsu,bugu da qari Allah S W T ne kadai baya gajiya da roqo,wannan shine cikakken alfanun sana’a a wajen diya mace.

“Baka ganin ina saida ruwa da lemo?” Ta fada a tausashe
“Ah,kice hajjaju ce nan a gabana” yadda yayi maganar saiya bata dariya
“Duk da hajjajun ce dai ungo amshi wannan ki riqe,don nasan lalurorinku na masu ciki,kar a je a rugurguje ribar da jarin duka” hannu biyu ta amsa zata karba tana godiya saiga rufaida tashigo.

“Idan kagama inada magana” ta fada idanunta akan kudin hannun mmn amir da take niyyar ajewa,wani takaici ya kamata,ai ita datake kan ganiya ita yafi cancanta yadauki kyauta irin haka ya bata,wayasanima ko kullum sai ya bata?,shi yasa baya fashin shiga,kuma dakinta kullum yake fara shiga
“Ganinan zuwa muje” ya fada yana nuna mata hanya,yadda bata kula mmm amir din ba itama saita sake tsumewa,tayi kamar nata ganta ba,tunda aqa’idance ita yakamata tasoma gaidata,na farko ta girmemata a wajen miji,nabiyu kuma har dakinta ta taddata
“Shikenan saina dawo”
“Allah yatsare” ya amsa mata kana yafita.

Yana fitowa sukayi kacibus da mmn ummi wadda aketa gyare gyare tun safe za’a karbi miji,yayin da rufaida ke daga kitchen tana diban abincin kari,saidai duka kunnuwanta na tsakar gidan,gaisawa sukayi itama sannan yamiqa mata kudin cefane,ta amshe cikin walwala ta rakashi da addu’o’i,kana itama yashaida mata zasu duba hajiyan idan yadawo,wani murmushi rufaida tasaki,anzo wajen,plan dinta zai tafi dai dai kenan
“To Allah yakaimu” ta amsa ba tare data tambayi me zasuje yi din ba.

Fitowa rufaidan tayi daga kitchen din,itama gaya mata yayi
“To” tace kawai itama tayi gaba,ganin batayi magana kan nemanshin da tace tanayi ba saiya sanya kai yafice daga gidan,yayin da rufaidan tawuce dakinta tana waqar
“Ahayye sama ruwa qasa ruwa…” Tana wassafa tsiyar da zata tsula anjima.

*kuci gaba da haquri dai,duk sanda kukaji shuru ba shakka wani babban uzuri ne ya kawo tsaikon,sannu sannu bata hana zuwa,jigon ko manufar labarin dai daukar darasi da koyi da kyawawan halayen ciki*…..

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button