Hangen Dala 1

“To na gode,Allah ya qara budi”
“Amin amin” ya fada yana sanya kai zai fice daga gidan,duk abinda ke faruwa mamn ummin tana bakin famfo duqe tana wanke kayan da yaranta suka cire,qasan zuciyarta tana jin kamar ra kama mmn amir ta daka,tana ganin duk ita ke daurewa baban amir gindi,har wani durquson goge masa takalma take da tsohon cikinta?,tana masa addu’a?,mutumin da zai musu kishiya aoba masoyinsu bane,kamata yayi su hada kai su yaqeshi harsai ya gaji don kanshi ya janye,amma tafi yarda da zancan hadixa data gaya mata idan ta tona zuciyar maman amir din qila fal take da farincikin za’a yiwa mmn ummin kishiya,tunda kishiya tabiyu tana bin wada kebi mata ne ba matar farko ba.
Tana kallonshi amma qyashi take tace masa a dawo lafiya,har yakai soro wata zuciyar ta tunzurata,donme zai baiwa mmn amir kudi amma ita data aika yara jiya suka gaya mishi ya bata cikon kudin me takalmi yace bashi dashi?,wuf ta miqe ta rufa masa baya.
Dab da zai fita ta rafka masa kira,da mamaki yajuyo yana kallonta,ta qaraso dab dashi fuskarta kamar tasowar hadari hannunta aqugu
“Wannan rashin adalcin da kake gwadamin ya isheni hakanan,jiya jiya nace ka bada cikon kudin takalmina kace babu amma yanzu ita ka narka mata kudi zataje awo,toni ka gayamin a wacce bolar ka auroni ne?” Sakato yayi kawai yana dubanta cike da dimbin mamaki,ta manta lokacin da yake bata ninkin kudin da ake buqata a asibitin,kuma yadauketa cikin motarshi ya kaita yadawo da ita,wani lokaci harda qwalama ta masu ciki amma mmn amir din koda ta nuna damuwa a fuska badai kaji abakinta ba,ta manta sanda take tsiro da ankon qawaye na babu gaira babu dalili ya dauka kudin ya bata ba tare da mmn amir din tace komai ba.
Kafin ya furta komai kira yashigo wayarsa dake gaban aljihu,ya zaro yana duban me kiran,rufaida ce,murmushi ya subuce masa wanda ya tunzura mmn ummi
“Ina magana dakai kayi banza dani kana kallon waya kanamin dariya kamar wata tababba?” Daga kai yayi ya dubeta sannan ya maida kansa kan wayar yana shirin dagawa fuskarsa washe da fara’a
“Baki da amsa ne ai” kafin yakai ga kara wayara a kunne tasa hannu ta warce wayar cikin fushi da fusata tana duba me kiran,dama jikinta ya bata ashe kuwa itace,a cike take da ita dama,wancan kwanakin ranar girkinta data turowa baban amir din saqonni har guda biyu,wayar na kusa da ita tadauka ta karanta,ta mata reply na zagi itama ta maido mata,kafin ta sake maida mata baban amir ya karbi wayar,da sauri ta kanga wayar a kunnenta,kafin tace komai kalaman sun daki kunnenta
“Honeeeyyyyyyy” muryar rufaida ta ratsa dodon kunnenta cikin shagwaba
“Honey din uwarko kona ubanki,shegiya karuwa,masifa annoba,to bari kiji na gaya miki,wallahi sai kinyi danasanin shigowa gidan nan in gaya miki,banza shashasha kawai,ballazaga mebin mazan jama’a” ta qarashe maganar tana barin soron da sauri saboda amsar wayar da baban amir ke qoqarin yi,ta saka sakata a qofarsu ta tsakiya cikin hanzari,ma’ana ta rufe baban amir din daga can soron do ta samu damar cin karenta babu babbaka,wata dariya rufaida tasaki kaman taba kallonta ta tabe baki
“Tooo….yau kuma da haukar da aka tashi kenan?,bari na soma tambaya cikin gawarwarkin daya aje gidan wace ke a ciki,ta farkonce kome bi mata don insan yadda zan ciwa mace uwa dakyau”
“Ta uwarkice,nace ta uwarkice wadda bata ramin kanta saina wani stupid” dariya takuma yi saboda tunda taji ta jefo kalmar bature to ba shakka maryam ce
“Kice dai bama ramin kanmu saina wani,ina cewa kema saura kika tarar shi yasa zan shigo na tayaki muci tare,to bari kiji,ni bana fada a waya,ki tanadi duk wata masifa da bala’i da makamanki da bomabomai saina qaraso gidan,don waya tayimin kadan wallahi,wawuyar mace wanda batasan inda yake mata ciwo ba,saikin gane uwarki bata koya miki komai na game da yadda zaka mallake miji,ki jirayi shigowar rufaida zaki gane komai da babban baqi” daga haka ta kashe wayar qit
“Abu ta kazar uba,ni zata zagawar uwa?,wallahi yau saita gane shayi ruwa ne” mmn ummi tasoma kumfar baki tana banbami tare da qoqarin sake kiranta,cikin haka Allah ya bawa baban amir damar bude qofar wadda sabida sauri sakatar bata gama shiga ba dai dai bata sani ba,yana shigowa yakai hannu ya finciki wayarsa
“Ka bani,wallahi saina rama zagina”
“Bazan bayar ba ki qwata idan kina da qarfi”
“Allah ya isa ban yafe ba wallahi,da ita da wanda ya daure mata gindi,macuci azzalumi,aina haka mukayi dakaiba sanda kaje zaka auroni,Alla ya isa ban yafe haqqina ba,kuma zagina da tayi sai Allah ya mana hisabi dakai” juyowa yayi yana dubanta cikin matuqar bacin rai,zaiyi magana kiran rufaida yasake shigowa
“Kiyi haquri don Allah my rufeee….” Abinda yasona cewa kenan cikin kwantar da murya kana yayi shuru na wani sakanni,wanda hakan yabaiwa rufaida damar jiyo bambamin da mmn ummi wadda ke tsaye a bayanshi takeyi,murmushi yasaki yana cewa
“Yauwa dear….na gode” baiko waiwayeta ba ya saka kai yafice yana ci gaba da wayarsa da rufaidan,wanda tana sane tajanyeshi dama,hannu maman ummi ta dora aka ta zube a wajen,tana jin kamar zata tayar da bori,ita baban amir yayiwa haka?,mutumin dako bacin ranta baison gani shine a yanzu zai watsar da ita yawuce abinsa?.
“Haba mmn ummi,wai sau nawa zan gaya miki wannan?,yanzu meye amfani ko ribar abinda kikeyi,maqota da masu wucewa duka sunajinki?,kafin a tsinewa baban amir sau daya an tsinemiki sau goma koda mala’iku kuwa” harara tayi kaman zata watsa mata saita fasa,cikin qunar rai da fusata tace
“Kome baban amir yayi yasamu goyon bayanki ne,tunda kinsan hannu daya baya daukar jinka,ba yadda banyi dake mutare abinnan ba amma kika qi bada goyon baya,yanzu kinsan muggan kalamai da alwashin da yarinyar takeci a kanmu nida ke?,to nida ke mu shirya kayanmu dukanmu gaba daya saita fitar damu” murmushi maman amir tasaki tana kada kai
“Kome ta gaya miki maman ummi kece kikayi babban kuskure,ina ruwanki da budurwar mijinki?,meye hadinki da ita?,kin fita kusa da mijinki,kin fita daraja koda ba haka bane to a wajen Allah haka ne babu kuma wansa ya isa ya kankare,koda tashigo gidan kuwa karki manta zata jima bata cimma matsayin dake kike kai ba,tunda ko banza kin rigata samunshi,kin rigata samar masa da diya,to me yayi saura?,me zai daga miki hankali?,maman ummi….” Ta kira sunanta cikin nuna da gaske zata furta mata maganar
“Inada yaqinin nafiki son abban amir,na kuma fiki kishinsa” saitayi jagale tana kallonta,magana takeson gaya mata kenan kome?
“Qwarai,ina tare da abban amir tun auren saurayi da budurwa,tun baida wani abun azo a gani,amma daga sanda yasoma neman aure na sanyawa kaina salama,inajin kishinsa kamar na mutu,ina kuka saboda kishi,ina kasa ci in kasa sha saboda kishi,amma dana fuskanci wanda nake abun saboda shi shi jin ransa yake kamar sallah saina sawa raina haquri da dangana,na kawo idanu na zuba akan duk wani abu da zaimin cikin sani ko rashin sani,wanda zumudi da rawar kaine ya sanyashi dama wanda yayi saboda radin kansa,yanzu gashi an wayi gari na barshi da kunyar abinda ya aikatamin a baya,na tsira da mutuncina da darajata a idanunsa saboda ban aikata duk wani abu da zai nuna rashin nutsuwata ba,babbar zubewar girma ko daraje a wajenki na matar gida budurwar miji ta zageki,bari na tambayeki…”shuru ta sakeyi tana dubanta
“Tunda kuke da baban amir har kika shigo gidan nan kin taba kiransa na daga wayar?,kona taba kiranki dai dai da rana daya?,kin taba jin muryata ko ganina?” Kai mmn ummi ta girgiza sannan tace
“Duka ban taba ba,amma Allah yagani ni mmn amir bazan iya koda rabin abinda kikayi ba,wayar dare,kiran dare amma ace duka baki nuna ko daukan mataki ba?,bazan iya ba wallahi,babu wata shegiya data isa ta takani wallahi ko wace saina maida mata,duk wadda ta nunani da yatsa saina karyashi” ajiyar zuciya mmn amir tayi tana kallon mmn ummin,shi yasa a rayuwa duk abinda kasan bakaso kada kayima wani,idan ba haka ba kuwa,watan watarana saiya fado a kanka,sai an maka,sai an ramawa wanda ka cuta ko ka cusgunawa koka zalunta.
“Shikenan,Allah yabada sa’a” ta fada tana miqewa gami da bar mata dakin.