HEEDAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL
Yau da safe nanny ta shirya heedayah sch da kyar dan har kuka take ita barata sch ba yau zata zauna da daddy'nta a gda sanda daddy yasa baki sannan ta yarda aka kaita. Tare suka isa dasu don moha da sauri yakarasa ya sameta ta gaishe shi yake tambayar ta ya jikin daddy takasa cewa komi class nasu heedayah suka wuce sanda akayi ringing bell na 8:00AM sannan ya wuce class nasa. Around 9:30AM su mummy suka shirya zuwa asibiti inda suka hadu da dr ahmad suka gaisa sannan yafara aikin tests din da yakamata yayi within an hour ya gama ya mika wa mumy, hannunta na kyarma ta amsa ta bude taga positive atake idanunta suka cike da hawaye amman tayi kokarin hadiye kukanta dan tasan du tashin hankalin data ke ciki bekai wanda daddy ke ciki ba, daddy yace "positive ko?" Mumy ta gyada masa kai ta riko hannunsa tare da fada masa "we are in this together" dr ahmad yayi gyaran murya yace "in shaa Allah karku damu ciwon beci jikinsa ba, yana 1st stage ne so there is possibility he can survive it, zan muku recomending seatle grace hospital dake washington, Allah bada lafya" mumy tace "ameen mun gode se anjima" da kyar daddy ya mike suka fice driver ya dawo dasu gda, dady na zaune a parlour mumy na gefensa tana waya da PA'n dady kan yazo ya karbi passports nasu yamusu booking flight ya amsa da "yes ma'am lafya?" Mumy tace "in kazo zaka sani" ta katse wayar. Door bell aka danna nanny ta je ta bude alhj lawal ne ya karaso suka gaggaisa yake gaya wa daddy kan jiya wani abokinsa na san siyan mota TUNDRA so ya kaisa gun motor sale na daddy nd yabasa acct number'n daddy ma sauran su jira alert kawai, mumy tayi godiya sosai haka daddy ma, bayan like 15mins alert yashigo wayan daddy, mummy na dubawa taga har abokin nasa ya turo kudin 9 million. Daddy yace "a gaskia samin frnd kamar ka a zamani irin tamu ta ynxu da wahala u've proven urself that zaka iya kula min da business koda bayan raina nd for that nagode" alhj lawal na washe baki yace "ahh bakomai"can azuciya kuwa cewa yake "keep on trusting me zan dau asaran dayafi 9mil dan arzikin ka yazamo nawa, bawani abokina da ya siya motarka ni na siya" mummy ce tayi breaking mai tunani "bari nanny ta kawo maka abinci mana" yace "a'a am full" daddy yace "inda zaka iya min wannan abu dan uwa" alhj lawal yace "mefa alhj? Zan ma komai musamman a condition da kake ciki ma ynxu" daddy yce "akoi wani meeting da zaayi ne daman a abuja, colours industry zasu saida 3% na shares nasu..." Ya tsaya yin tari sannan ya cigaba "naso zuwa amman a gaskia hakan ba me yuwa bane dan nan da 4-5 days zani washington a dubani a can" alhj lawal yace "ayya Allah bada lafya alhj ,in shaa Allah i'll try my best zan maka komi mude Allah baka lafya" alhj s.u yace "toh nagode Allah biyaka, meeting din will be held in 3 days time so prepare pls" alhj lawal yace ba matsala alhj anything for you, am very grateful daka bani wannan dama and in shaa Allah bazan baka kunya ba" alhj s.u yace "ba komi nine da godiya" hira kadan suka taba alhj lawal yace zaya tafi mumy ta rakasa sannan ta dawo ciki. "Gaskia wannan abokinka nada kirki sosai habibi Allah kawo dalili ka masa wata alherin kaima" dady yace "ameen" karan door bell again suka jiyo nanny ta bude PA'n daddy ne ya gaishesu cikin girmamawa yakuma tambayi ya jikin daddy? mumy ta amsa da "da sauki" takuma masa bayanin komi aciki harda dalilin su na zuwa washington din, shide addu'a kawai yatayi Allah bama daddy lfya.
Fitan alhj lawal ya zarce gdan alhj ismail ya wuce garden ya tura me gadi daya ma alhj magana, kafin alhj ismail ya fito alhj lawal ya barbada maganin da malaminsa ya basa acikin wata jug daya ga ruwa a ciki, bayan 7mins alhj ismail ya karaso da fuskarsa a daure ya zauna alhj lawal ya gaishe sa ya amsa tare da cewa "alhj lawal in har kasan maganan banzan da kake min for the past days kazo yi dan Allah kayi hakuri katafi, dan baraka taba samun hadin kai a guna ba" alhj lawal yayi murmushi sannan yace "ko kadan dan uwa Allah ya ganar dani nima, in shaa Allah baruwa da arzikin alhj s.u ynxu ma daga gdansa nike, nanemi gafararsa kuma ya yafe min har yace ma zanyi representing nasa a wani meeting da za'ayi a abuja nanda kwana uku" alhj ismail yace "dakata karka raija min wayo mana" alhj lawal yace "wallahi ba karya ba ai baran rantse akan karya ba in kuma baka yarda ba gashi kirasa kaji, i know it'll be difficult for u to believe me but either ka yarda ko ba ka yarda ba nagano gaskia nima ynxu arziki nufin Allah ne kamar yadda kafadi min a baya, daman sharrin shedan ne ba komi ba" ya zuba musu ruwan dake cikin jug din acikin glass cups dake gabansa ya mika wa alhj ismail sannan yace "toast!" Alhj ismail kallonsa kawai yake amman be yarda dashy ba suka dan buga glass na ruwan sannan suka danyi sipping kadan, alhj lawal kam be sha ba dake yasan meyasa a ciki. Alhj ismail yace "in har abinda kafada min gaskia ne to nagode wa Allah da ya amsa addu'ata yasa ka gano gaskia, Allah yabamu sa'an cin nasara akan shedan" alhj lawal yace ameen, a zuciyarshi kuwa dariyan mugunta kawai yakeyi***
Heedayah na dawowa from sch ta wuce dakin dady yamata sannu dazuwa tabasa peck a goshi sannan ta tambayesa “daddy ya jiki?” Ya amsa da “da sauki my princess, ure prayers keep me moving, nogode ko?”tayi masa murmushi sannan tayi hugging mumy ta wuce dakinta, tana fita mumy ta fashe da kuka, dady yace “mekuma na kuka my dear? Kukanki na sake kashe min guiwa kince we are in this together but is like ure giving up already” mumy tace “ko kadan habibi wallah heedayah kawai ke ban tausayi zamui tafiya in 4-5 days time and open day nasu monday kasan bareyi muje ba, nd heedayah will never understand koda she’ll ma, bansan taya zan fara fada mata ba” takuma fashewa da wata erin kuka daddy yace come here tatashy ta karaso gunsa yayi hugging nata tareda cewa “everything will be fine in shaa Allah”
[10/10, 12:59 PM] ????????????Salma????????????: ????????????????????????????????????
HEEDAYAH!
????????????????????????????????????
1⃣2⃣
written by miemie????
Yau ma kamar kullum nanny ta shirya heedayah sch, tare suka iso da baby suka wuce class nasu heedayah take tambayar heedayah ya jikin dady’nta? Heedayah ta amsa “da sauki” amman kwata kwata kamar ba heedayah me surutun da baby tasani ba, she’s so quiet nd calm ynxu don moha na isowa shima yawuce class nasu heedayan suka gaisa se 8:00AM suka bar class nasu heedayah. Auntinsu ma tayi noticing, heedayah bata concentrating sosai a class a koda yaushe cikin tunani take bata masan me ake koya musu ba, hakan kuwa ba karamin ta mata da hankali yake ba, during break ta kira heedayah tata gaya mata kalamu masu dadi masu kwantar da hankali kan kar ta damu her dad is gonna be fine, heedayah tadanji dadi, ahaka har aka tashy heedayah bata wani yi surutun kirki ba, mal idi yazo ya dauketa a mota ma se surutu yake mata ita kuwa amsarta daga “eh” se “a’a” ahaka har suka isa gda ta wuce dakin dady kamar jiya tabasa peck a goshi tayi hugging mumy sannan ta wuce dakinta ta canza kaya ta sauka kasa taci abinci takuma haurawa sama dakinta dan yin home work nata, tana cikin yi mumy tayi knockin sannan ta shigo ta zauna kan kujera tace “my princess zomuyi wata mgn” heedayah ta taso ta zauna kan cinyar mummy, mummy tace “kinsan daddy baida lafya ko?” Heedayah ta gyada mata kai, mumy ta cigaba “nida daddy zamui tafiya saturday ko sunday zamu kai daddy asibiti dr ya dubashi” heedayah tace “that means baraku zo min open day na on monday ba knan mummy?” tagama maganar idanta cike da hawaye mummy tace “don’t cry sweetie, in muka dawo zamu miki nd kinga babansu muhammad ma ai ze iya miki ko heedayah ta?” Ta sa hannu ta goge mata yar hawayenta, heedayah tace “ni banason babansu muhammad yamin, na hakura baran je sch ba ranan, in kun dawo zakumin ba? Promise?” Baki na rawa mumy tace “promise” heedayah tadanyi murmushi tace “ina zakuje nd yaushe zaku dawo mumy?” Mumy tace “kinsan washington DC dake united states?” Heedayah ta girgiza kai da alaman a’a mumy tayi murmushi tace “but am sure auntinku ta gaya muku inda white house yake ko?” Heedayah tace “laaaa se ynxu na tuna white house gdan mr president is situated in washington DC in america” mumy tace “excellent my princess to can zamuje da daddy dr yaduba shi, me kkeson in siyo miki?” Heedayah tace “ni toys nakeso dayawa da manya manyan teddy bears wanda suka yini a girma” mumy tayi dariya sannan tace “in shaa Allah zan siyo wa princess dina. One thing, my heedayah baraki koma islamiya ba? Kinga fa rabuwan ki da islamiya tun primary 2, yi hakuri kifara zuwa kinga se kiyi wa daddy addu’a ya warke da wuri ya je miki open day ko?” A lokaci daya mood na heedayah ya canza dan in akoi abinda ta tsana ynxu befi islamiya ba dalilin kuwa shine kan dukan dawani malami yataba mata wai dan ta taho da babyn wasa aji tun daga ranan heedayah tace barata sake zuwa islamiya ba duda dady yaci mutuncin malamin dan har police station sanda sukaje but still heedayah tace ita barata sake zuwa islamiya ba, shi kuwa daddy yace abarta tadan huta kunji dalilin rashin zuwa islamiyar heedayah knan. Heedayah tace “ni mumy baranje islamiyan nan ba malaman islamiya are wicked suna dukan mutum kinga auntinmu na sch bata dukan mu, ni baran je ba zanyi wa daddy addu’a a gda” mummy tace “heedayah kin taba ganin wanda bai zuwa islamiya? Naji bakison zuwa islamiya zan nemo miki malami yana zuwa yana miki a gda aikinga that way bare miki duka bako?” Heedayah ta gyada kai mummy tace “sekiyi concentrating kinji mumy’s princess? Now finish ur assignmnt” tamata peck a goshi sannan ta fice**
[10/10, 12:59 PM] ????????????Salma????????????: ????????????????????????????????????
HEEDAYAH!
????????????????????????????????????
1⃣3⃣
written by miemie????
4 days later** su mummy duk sun gama shiri dake yau zasui tafiyan flight nasu na 7:00AM ne, alhj lawal kuwa har yaje yayi representing dady nd the meeting was a success yaci dady yamasa godiya sosai. For 2 days kafin tafiyarsa abujan kuma yake zuwa gdan alhj ismail yana sa mai maganin da malaminsa yabasa cikin ruwan sha, a ynxu haka har ya fara controlling alhj ismail amman ba sosai ba tho befara masa maganan cin arzikin alhj s.u ba, yana jiran se in sun dawo frm washington din tukuna. Heedayah kuwa taki fitowa daga dakinta se kuka take zubawa se can dasu mumy zasu tafi sannan suka haura sama har da daddy da bai da lafyan ma, mumy tayi iya suratanta heedayah taki bude kofa sanda daddy yasa baki shima da kyar sannan ta tashy ta bude tayi hugging daddy tana ta kuka me tsuma zuciya, mumy batasan sanda tafara kuka ba itama ji take kamar su tafi da heedayah amman sch nata kuma fa? Da kyar sukasa heedayah tayi shiru suka sauko kasa, tasake hugging mummy da daddy sannan suka shige mota tamusu Allah kare ta ruga ciki da gudu balcony straight ta wuce ta na kallonsu daga sama taga mumy nata zuba bayani wa nanny, nanny na gyada kai tana gama mata maganar ta shiga mota nanny tana musu waving hand har motarsu tabar gdan. Wani sabon kuka heedayah ta soma ta dawo ciki ta wuce dakinta se kuka take zubawa pillow'nta sanda yakusa jikewa da hawaye nanny tashigo ta aza ta kan cinya tana bata hakuri da kyar ta rage kukan nanny tace "ynxu ki kwanta kiyi bacci in kka tashy anjima sekiyi breakfast mukaiki shopping ko? Mummy tace ko shoprite kkeson ki siye zaki iya siya" heedayah bata ce komi ba nanny ta kwantar da ita ta rufeta da bargo sannan ta fice, ahaka har heedayah ta koma bacci se around 10:45AM ta tashy tayi brushing ta sauka qasa tayi breakfast nanny tamata wanka suna kokarin fita don moha ya danna door bell nanny ta bude masa ya gaisheta ta, ta amsa da fara'arta "ai ynxu ma zamu fita shopping da heedayah, ko zaka bimu?" Don moha yace "toh muje" "heedayah! Yi sauri ki taho mutafi ga don moha ma yazo" heedayah na saukowa ta gaishe da don moha suka shiga mota suka wuce shoprite tun heedayah na qin sakewa da don moha har tasake dashy sukata shopping kamar ba gobe komi yagani seya dauka mata ahaka har suka gama nanny ta bibbiya suka dawo gda aka sauke don moha sannan suma suka wuce gda, nanny tasa mal idi yakai kayan dakin heedayah sannan tafara shirya mata saura a wardrobe a yayinda heedaya ke zaune a parlour tana kallon cartoon network dake ba a basu assignmnts ba kasancewar zaayi open day ran monday*** can dare around 10:00PM mumy ta kira nanny tamata ya gaijyan hanya tace "alhamdulillah, ina princess dina?" Nanny ta kira heedayah ta bata wayar mummy tace "mumy's princess ya kke?" Heedayah tace "lafya se ynxu kuka isa?" Mummy tace "eh nanny ta kaiki shopping din kuwa?" Heedayah ta amsa da "eh ina daddy?" Mummy tace yagaji yana bacci amman yace in gaishe ki that he's missing you" heedayah tace "i miss you both, daxu nayi sallah nace Allah bama daddy na lafya" mumy tace "yawwa good girl in shaa Allah ur daddy is gonna be fine ynxu kije ki kwanta kinji? Its getting late, seda safe ko muny's princess, blow me a kiss" heedaya tace "muahhh goodnight mummy" ta kashe wayar.
Ahaka heedayah tayi spending weekend dinta ba mumy ba daddy don moha ne kawai ke dibe mata kewa. Ran monday kuwa bataje sch ba dake ba me zuwa mata open day. A rana se sunyi waya da daddy da mummy sama da biyar har su daddy sukayi sati a can sannan suka fara maganan dawowa dake dr ya kuma yin tests din yaga ALS disease dinne da daddy amman 1st stage ne kawai kamar yadda dr ahmad yafadi, yakuma buqaci mumy da daddy dasu kwantar da hankalinsu evrythng is gonna be alright ya daura daddy kan medication sosai da alluarai yakuma ba ma mummy numbansa in case in wani abu ya kuma samin daddy in suka dawo gda 9ja mumy tayi godiya sosai. Bayan 2 days su mummy suka dawo 9ja duk sun gaji around 12:00AM na dare suka iso mal idi, nanny harda heedayah ma sukaje daukosu frm airport heedayah tayi missing parents nata sosai haka suma ahaka har suka iso gda kamar su cinye junansu a mota mumy nata mamaki har 12:00AM amman idan heedayah biyu.
Toh masu karatu THE BATTLE IS YET TO START, TIGHTEN UR BELTS!
[10/10, 12:59 PM] ????????????Salma????????????: ????????????????????????????????????
HEEDAYAH!
????????????????????????????????????
1⃣4⃣
written by miemie????
Yau da safe around 6:00AM nanny tazo tada heedayah sch but taqi, ita atapir barataje sch ba harda kukanta amman nanny taki barinta dake mumy kwata kwata batasan wasa da sch haka sukata drama a daki amman heedayah taki sanda ta kai karan heedayah gun mummy daddy yace "eh a barta ta zauna tunda na yau ne kawai" omo zokuga murna gun heedayah harda yi wa nanny gwalo sallah kawai tayi takoma bacci se to 10:00AM ta tashy nanny tamata wanka tasa wata leggings iya guiwanta nd top nata ta wuce dakinsu daddy tayi hugging nasa sannan ta gaishesa haka tayi wa mummy ma, mummy ta dauko wasu katti kattin leathers ta mika ma heedayah "ga tsarabarki" heedayah se xumudi take takasa settling gu daya tayi nan tayi can se bude bude take a yayinda mummy ta dauko magungunan daddy kuma zata kai masa dan yasha, heedayah tafiya take bata kallon gabanta dake da baya take tafiyan kafin mummy tace meh heedayah ta bugeta drugs din duk suka fadi a kasa na fashewa suka fashe wata erin ihu mummy tasaka sanda nanny ta karaso dakin itama. Heedayah duk ta kidime a take tafara kuka, kasa fadin komi mumy tayi can tafara magana "shiknan heedayah kin gama dani da daddy'nki bansan kuma a ina zan samu magungunan nan ba a nan 9ja, kwata kwata banso zaman ki agda ba, ga erin abinda nake gudu ai bakida ido ne kalli abinda kka sa nayi anan? Mtsw get out!" This is the first time mummy ta fara yi wa heedayah masifa "kekuma nanny kin tsaya kina kallona baraki tattara gun bane?" (Da anga mummy ansan acikin frustration take magana), nanny ta shiga tattara broken glasses din, heedayah kuwa duk ta kidime kuka kawai take har takai bakin kofa daddy ya kirata "zo my princess" tana kuka ta karaso kan gadon "am sorry daddy I didn't mean for it" ta fashe dawata erin kuka daddy yasoma lalashinta "I know u didn't my princess bar kuka kinji? Ya isa" heedayah tace "mummy is mad at me, kiyi hakuri mummy bada gangan na bugeki ba" ta fice dakin da gudu ta wuce dakinta, mummy duk setaji wani iri nan da nan nanny tagama tattara wurin ta fice itama dakin heedayah ta nufa taje tana bata hakuri cikin kuka heedayah ke magana "nanny ina kinsan ba dagangan na buge mummy ba ko?" Nanny ta gyada mata kai heedayah ta cigaba "then why is she mad at me?" Kuka takeyi sosai nanny na bata hkuri** can a dakin daddy kuwa daddy bece wa mumy komai ba haka itama can daddy yyi magana dake yaga mumy bata da niyar yi, yace "my dear go nd tell heedayah sorry, bada gangan ta bugeki ba bakiga yadda ta rikice ba, she's sorry for what she did" mumy tace "habibi ni kaina banji dadin abinda na mata ba, wlh frustration ne bansan a ina zan sake samun drugs dinnan ba kuma kasan seda dr yace kar muyi wasa da dosage din" daddy yace "nasani but even still be kamata kimata masifa ba go nd tell her sorry we'll find out a way a sake siyowa ba munada numbern dr inba? so karki damu jeki bata hakuri" ba gardama mumy ta mike ta wuce dakin heedayah tana bude kofan dakin taga "heedayah nata zabga kuka nanny na bata hakuri" ta karaso tama nanny body signal data basu waje nanny ta fice, ko kallon mumy heedayah batayi ba se rera kukanta takeyi a hankali, mumy ta dago fuskarta data jike da hawaye tace "mummy is sorry my princess bar kuka kinji?" Heedayah batace komi ba, mummy ta kwantar da ita a jikinta tana jijiqata "is okay stop crying kinji am sorry, kin yafe wa mummy?" Heedayah ta gyada kai mummy tace "thank you" tabata peck a goshi bayan like 5mins suka koma dakin daddy tare, daddy yaji dadi sosai
[10/10, 12:59 PM] ????????????Salma????????????: ????????????????????????????????????
HEEDAYAH!
????????????????????????????????????
1⃣5⃣
written by miemie????
Mummy ta kira dr tamasa bayani ya tausaya wa daddy matuqa cuz kafin drugs dinsa su iso jikinsa ze yi tsanani cuz shi ALS disease immediate treatment yake nema sosai, hankalin mumy ya kuma tashy daga karshe de dr ya kwantar mata da hankali in shaa Allah within one week drugs din zasu iso. Acikin wannan sati daya kuwa daddy har ya fita daga kamanninsa ciwon yayi worse sosai da kyar yake magana, tafiya dasuransu duk sanda heedayah taga daddy'nta setaga kamar itace silar tata kuka haka mummy ma. Ana jibi maganin daddy ze iso, daddy yakega kamar he can't make it gani yake kamar ze mutu, alhj lawal da ismail yasa mummy ta kira dake yau wednesday heedayah na sch mumy kuma an bukace ta a asibiti as emergency so dan dolenta ta fita tabar care din daddy a gun nanny. Bayan fitanta da like 20mins su alhj lawal suka iso nanny tamusu sannu dazuwa sannan taje ta gaya wa dady kan yayi baqi yace "ta shigo dasu daki" hakan akayi suka gaishe sa da jiki da kyar ya amsa dake ba karamar wahala magana ke masa ba yafara da cewa "alhj lawal?" alhj lawal ya amsa da "eh alhaji" daddy ya dawo da kallonsa kan alhj ismail sannan yace "alhj ismail?" Shima ya amsa, daddy ya cigaba "kunga de yadda nake ynxu rai a hanun...A..l.lah" ya tsaya yayi tari sosai sannan ya cigaba "ba dan komi na kiraku ba face dan in baku amanar business dina dan gani nake kamar i cant make it" alhj lawal yayi interrupting daddy "ko kadan alhj in shaa Allah zaka samu sauki ka cigaba da kula da business naka da iyalen ka duka" daddy yace "i hope so amman ynxu inaga kamar I cant make it sesa tun kafin in mutu nakeson nabaku amanan business dina cuz ku kadai nakeda wanda zan iya trusting, ko blood brothers dina baran iya trusting nasu as yadda nayi trusting naku ba, so pls ku riqe min amana" yasa hannu a karkashin pillown sa yakasa ciro papers din sanda alhj lawal ya taya sa "yace bani biro" alhj ismail ya miqa masa, ahj lawal harda hawayen munafinci "alhj s.u me kake kokarinyi? Pls karkayi signing papers dinnan zaka yi surviving wannan jarababbiyar ciwon in shaa Allah" alhj s.u yace "dan uwa kai fa kafada mun da abaya zaka kula min da business da iyali ko bayan raina amman is like baraka iya ba ynxu" (duk wannan magana da tari alhj s.u ke yinsu.) Alhj lawal ya goge yar kwallar munfincinsa sannan yace "ko kadan dan uwa koda last breathe dina ne zanyi sacrifising dan naga na rike maka amana" alhj s.u ya sa hannu kan papers din alhj lawal yace "kasa sunan dan uwa na alhj ismail" alhj s.u be kuma cewa komi ba yayi signing akan sunan alhj ismail ya miqa wa alhj lawal ya amsa seya barke dawata dariyan mugunta a lokaci daya. A daidai lokacin heedayah ta dawo frm sch as usual seta wuce dakin daddy sannan ta wuce nata, ta kai kofar dakin daddy knan taji dariyan muguntan da alhj lawal keyi dan yadda ta rude seta kasa gane ko alhj lawal dinne ko alhj ismail amman de tasan acikin dayansu ne, ta bude kofar kuma kwata kwata takasa, idea din bude kofar ma bata zo mata ba can se me dariyan ya fara magana "alhamdulillah finally ranan ya iso, rananda nakeson na mallaki dukiyar ka alhj s.u. I have waited for years, trusting dina dakayi is the biggest mistake dazakayi a rayuwarka, ba kula da family'nka da zanyi, business naka kuwa zan kula dashy sede ba dan in amfanar da family'nka ba a'a dan nawa family'n ne" bakin alhj s.u rawa yake yana magana cikin kuka "a.a.alhj la.w .al me kake fadi? Ashe dama ba sona kake tsakani da Allah ba? Aduk zama na dakai tsakani da Allah na rike ka bansan mena taba maka ba da zaka min wannan abu a rayuwa. Naji ka dauki arziki na kab nabar maka amman dan Allah ka kula min da iyali, 'yata heedayah pls alhj lawal yaja wata tsuka. Daddy ya dawo da kallonsa kan alhj ismail yace "harda kai alhj..." seya hau tari ya kasa karisawa kuka kawai ya hauyi sharkaf sharkaf da hannunsa rike a zuciyarsa. Irin dariyan daxu alhj lawal ya kuma yi sannan ya dau pillow ya danne wa alhj s.u sanda yaga bayya motsi. Yace wa dan uwan nasa "mu tafi" suna fitowa sukaci karo da heedayah a bakin kofa ta hada kai da guiwa se kuka take rapkawa kamar zata cire ranta atake jikin alhj ismail ya dau rawa dake shi ke rike da files din nd daga gani heedayah ta jiyo abnda suka kulla a cikin dakin baki na rawa yace...
[10/10, 1:31 PM] ????????????Salma????????????: ????????????????????????????????????
HEEDAYAH!
????????????????????????????????????
1⃣6⃣
written by miemie????
"Heedayah yaushe kka dawo frm sch?" Heedayah ta dago jajayen idanunta tace "ynxu" alhj ismail yace "toh ya kke kuka ko anty ne tamiki duka?" Heedayah ta share hawayenta tace "a'a na fadi ne a sch damuke wasa" alhj lawal yace "sannu toh wuce daki kije ki huta" ta dau jakarta kamar dagaske tana ganin sun fice ta dawo da sauri ta bude kofar dakin daddy ko kallon direction na daddy batai ba hankalinta na kan cctv (spying camera) dake dakin ne kawai ta haura kan wardrobe ta ballo tana sauka suka hada ido hudu da alhj ismail yace "ke heedayah! Me wannan? Kawo in gani?" Ta zura masa ido ya sa hannu ya wabce cameran yace " so u think u are smart ko? Me kka ji dazaki ciro cctv dinnan? Wani abu kkeson ji?" Heedayah ta girgiza mai kai ya cigaba "to wallah kika kuskura kika gaya ma wani ko mumy'nki kan abinda kkaji munyi ni da baban mustapha" ya daka mata tsawa sanda ta shiga bari "sena pille kanki, kinji ko bakiji ba?" Heedayah baki na rawa tace "naji naji" ya fice, kan daddy'nta ta nufa tana jijjiqa shi "daddy! Daddy wake up pls, ka ma baban muhammad da baban mustapha duka ka kaisu gun police auntinmu tace can ake kai criminals bcuz dey are all criminals daddy wake up muje police station kaji, daddy!" Ina daddy shiru wata erin mahaukaciyar ihu ta sakar "daddy!" Nanny dake toilet sanda ta fito a gurguje "heedayah meke faruwa? Me kke kuka? Bakiga daddy na bacci bane? Kibarsa kinji. Oh har su alhj lawal din suntafi ne" duk wannan tambayoyi heedayah bata amsa mata ko daya ba daga karshe tace "nanny daddy baya numfashi" nanny tace "ke heedayah shegen manyance ne da ke, yaushe kkasan ko mutum na numfashi ko baiyi, common zo muje daki ki canza kaya kuma kukan ya isa" heedayah ta daka mata ihu "am serious nanny zo kiji" nanny ta karaso jiki na rawa tasa hannunta kusa da hancin daddy taji fa ba alamun numfashi salati kawai tahau yi ta jawo telephone ta kira mummy, maganartan ma ba fita takeyi ba "mu.m..my ki taho gda alhj ba lafya baya numfashy" "what?" Abnda mummy ta fada knan nanny ta kashe wayar. "Heedayah gaya mun meya samu daddy? Me kka masa ko haka kka samesa?" Heedayah ta bude baki zatayi magana seta tuna abinda alhj ismail ya gaya mata, ta ja bakinta kum! Tayi tsit "nima bansani ba haka na gansa since dawo na frm sch, nanny do something banason daddy na ya mutu pls" tafashe dawata erin matsanancin kuka bayan 20mins mummy ta iso ba abun ince firewa tayi ba, a gigice ta shigo gdan se dakin daddy tayi kansa tana kuka tana kiran sunansa amman ina daddy bai ko motsi, nan da nan nanny ta kirawo mal idi yashigo ya daga daddy akasashi cikin mota se emergency. Mummy, heedayah, nanny se kuka suketa rapkawa mal idi ma idanunsa duk sun kada.
An hour later dr din yafito mummy tayi kansa tare da jero masa tambayoyi, "dr how's my husband doing? Can I see him now? Dan Allah ya yake? Talk to me pls" dr yace "calm down, ko kece matarsa?" Mummy tace "sure, yes, ofcourse, definately ni ce matarsa" (bata ma san sanda ta jero wannan answers dinba) dr yace "muje office dina" heedayah ta kama sabon kuka ta kankamo mummy itama setabi su da kyar nanny ta jata jikinta sannan mummy suka fice da dr sukayi office nasa yace mata "have a seat pls" mummy tazauna dr yafara kamar haka "nakega ba se nagaya miki ba u already know mijinki is affected by ALS disease ko?" Mummy tace "yes for sure am aware, disease din na stage 1 ne" dr yace "a da knan dan ynxu da mukayi test mungano yakai stage 3" mummy ta dafa kirji "what???" Hawaye kawai ta fara zubda, dr yace "ko kinsan meya samesa ya sume?" Mummy tamasa bayanin abinda tasani, dr yace "ikon Allah there must be some explanations then...ko kinsan mijinki nada hawan jini?" Mummy tace "eh amman kuma da sauki dan ya jima bai complaining ba" dr yace "due to shock da maigidanki ya samu wanda kkace kema bakisan dalilin hakan ba yasa hawan jininsa ya hau sosai wanda yasa sa paralysing ynxu haka am sorry" suuuu mummy ta sulale kasa sumammiya
[10/10, 1:31 PM] ????????????Salma????????????: ????????????????????????????????????
HEEDAYAH!
????????????????????????????????????
1⃣7⃣
written by miemie????
Dr yakira nurses aka dagata itama aka kaita wata dakin, heedayah na ganin mummy'nta a sume ta sakar dawata irin ihu sanda aka fitar da ita daga asibitin kuka takeyi sosai kamar ba yarinya ba, immediate attention aka bama mummy within 20mins ta farfado ba abin da take furtawa face "habibi na don't go nd leave me" ahaka har tayi gaining back conciousness, kuka takeyi sosai heedayah da nanny ne suka shigo, heedayah ta karasa gun mummy'nta tayi huggung nata tightly tana kuka "mummy ina daddy? Muje mu daukosa mukoma gda mubar wannan asibitin eventually we will all fall sick dan Allah mutafi" tafashe dawata erin kuka me tsuma zuciya mummy ta taso da ita daga jikinta tace "look at me heedayah" da hannunta biyu rike a fuskarta "zamu tafi gda kinji dnt worry bari daddy yadan samu sauki kadan se mutafi stop crying kinji? Bansan inga princess dina na kuka, ure tears are way expensive, kinsan menakeso dake ynxu?" Heedayah ta girgiza kai da alaman a'a mummy tace "kuje gda da nanny kici abinci kiyi sallah, pray for daddy, do ur assignmnts seki kwanta ki huta kinji? Kina tashy nida daddy zamu dawo gda heedayah tace "inason inga daddy, mummy pls ko kadan inason inga daddy na" mummy tace "don't worry ynxu daddy na bacci anjima kadan ze tashy" heedayah tace "promise me mummy" baki na rawa mummy tace "i promise mumy's princess" tabata peck a goshi tace wa nanny "ku tafi" nanny bata ce komi ba takama hannun heedayah suka fice mal idi yayi dropping nasu sannan mumy ta kirasa yakuma dwowa asibitin. Bayan tashin mummy da like 15mins dr yashigo ya dubata yaga shes perfectly fine yace "ki huta madam, Allah bada lafya" mummy tace "ameen dr pls tell me meke damun mijina? How is he? Inason ganin mijina pls he need me by his side" dr yace "calm down ynxu ki huta" mummy ta ta rokon dr da yagayamata meke damun mijinta daga karshe ya karisa gaya mata bebar komi ba, salatin mummy kawai ke tashy a cikin dakin wai ace yau an wayi gary daddy is paralysed, bayida wani amfani kuma again, dashy da babu duk daya ne subhanallah ya Allah kaba ma mijina lafiya. Baki na rawa tace "dr pls kabarni inga mijina, pls" dr yace "muje" da kyar ta mike tabi bayansa suka shiga dakin daddy dr yabasu waje, jiki na kyarma takarasa gun daddy ta dauko hannunsa dake hade da drip ta rike bibbiyu da nata a hankali hawayenta ke sauqa kan hannun daddy se suratai take zubawa tana kuka tagama tayi addu'a ta kwantar da kanta gefen daddy ahaka har bacci me nauyi ya dauketa***
Da maghrib ta farka tayi sallah tasa mal idi kwaso mata essential things da zatayi needing dan kwana a asibiti yazama dole cuz har ynxu daddy beyi gaining conciousness ba. Allah ya so time da mal idi yaje kwaso kayan heedayah na bacci da har nanny zata ta da ita sallah sekuma tace bari ta idar sannan ta tayarda ita yadda Allah yaso su knan, har aka gama diban kayan heedayah batasani ba. Mal idi na tafiya nanny ta kira mumy ta gaisheta da jiki take tambayarta ko ta dafo mata abinci ne? Mummy tace "a'a kibary kar heedayah tayi noticing wani abu zan sa idi ya siyi min" nanny tace "toh shiknan tunda haka kkace, ya jikin daddy'n heedayah?" Mummy tace toh da sauki amman kam har ynxu beyi gaining conciousness ba nanny, i dont know what to do" nanny tata bata hakuri amman wannan abu da abin dubawa aciki, mummy tace "kibary kawai sena dawo se anjima" ta katse wayar. Nanny ta manta da zancen ta da heedayah yin sallah ma gabadai. Se around 10:00pm heedayah ta tashi tayi brushing tayi alwala without anyone telling her to, tayi sallolinta tayi ma daddy addu'a sosai sannan ta zauna tana nazarin abinda tajiyo dazu kwata kwata ta kasa gane waye ke maganar ko alhj lawal ne ko alhj ismail amman dey jikinta yafi bata alhj ismail ahaka tabar tunanin ta sauko kasa tasami nanny a parlour ta karasa gunta tace "nanny ina mummy da daddy?" Kafin ta jira me nanny zatace ta dau hanyar dakin daddy tana kwala masu kira shida mummy
[10/10, 1:31 PM] ????????????Salma????????????: ????????????????????????????????????
HEEDAYAH!
????????????????????????????????????
1⃣8⃣
written by miemie????
Tagama yawonta bata ga masu kamannin daddy da mummy ba, ta sulale a kasan dakin tafara raira kukarta me tsuma zuciya, nanny ta taso ta daga ta, tana lalashinta heedayah taqi yin shiru kuka takeyi sosai har bacci yayi awon gaba da ita tana jan numfashy a hankali nanny ta kaita daki ta rufeta da bargo sannan tarufo mata kofar.
Washegary, around 7:00AM daddy yadan motsa yatsar sa daidai lokacin idan mummy yakai gun da saurin gaske taje ta kira dr suka shigo tare yadan dudduba daddy yace "ma'am mugodewa Allah ur husband has gained conciousness" mummy tana murmushi tace "alhamdulillah" dr ya fice. Mummy ta karso kusa da daddy ta riko hannunsa da hawaye sharkaf a fuskarta tace "welcome back habibi" ta masa murmushi, daddy ya gwada magana amman ina yakasa, anytime yace zeyi mgn its becoming hard, atake mummy tafara sabon hawaye tana sharewa suna zubowa, haka daddy ma hawaye yake da kyar ya mata murmushi, mummy tasa hannu ta goge masa yar hawayensa tareda gaya masa "everything is gonna be fine in shaa Allah, try not to talk" tabasa peck a goshi. Tashi tayi ta dauko wayarta dan kiran nanny bugun farko nanny ta daga suka gaisa mummy tace "princess dina fa, tatafi sch?" Nanny tace "da kyar" mummy tace "Allah sarki my poor heedayah, ki hado mana breakfast ga daddy nan ya farfado" nanny tace "toh toh alhamdulillah kiban hour daya" mummy tayi hanging. Kiran dr dinsu tayi na washington DC sanda tayi 2 missed calls sannan ya daga a na uku ta gaishesa yake bata hkr akan delayance din maganin bada ga wurinsa bane mummy tace "ba komai gbe ne ai" yace "ya jikin me gidan?" Nan mummy tabasa labarin komi ya mugun tausaya wa daddy da mummy matuka ya ce ta kwantar da hankalinta ze hado mata wasu maganin in shaa Allah mijinta will get better duda it will take long process ne, yagayamata tips dayawa mummy tayi godiya in return ahaka sukayi sallama (duk wannan zance da turanci sukeyi.)
A sch heedayah kuwa ba wanda take masa magana kullum tana cikin tunani abin ba karamin tama antinsu hankali yake ba ace yar yarinya kamar heedayah amman ta zauna se aukin tunani gashy anytime ta tambayeta meke damunta setace mata rashin lafyan daddynta ne kawai amman aunty kam tasan for sure there must be something, har don moha sanda anty ta tambaya amman shima yace mata besani ba cuz heedayah is avoiding him bata masa magna ynxu yayi yayi da ita amman ina taki so ze bata space, daga karshe anty tayanke hukuncin kiran mummy. Bayan an tashy frm sch mal idi ya zo daukan heedayah acikin mota tace masa ita karya kaita gda gun parents nata takeson zuwa tata masa bori sanda ya yarda daga karshe suka zarce asibiti mummy tayi mamakin zuwan heedayah da unifirm wato ko gda ma bataje ba balle taci abinci nan danan ta kira nanny, nanny tace ita batasan da zuwansu bama akadawo kan mal idi aka suburbudesa sosai. Heedayah ta fashe da kuka "mummy wato ure not happy to see me? Haka jiya kka min karya kkace zaku dawo gda da daddy nata jiranku bakuzo ba, ba damuwa mal idi take me home" tatashy mummy ta riko hannunta "not at all my dear, kema kinsan kanki mummy will not lie to u like that, inason in gaya miki wani abu nd inason kibany mind naki kijini da kyau. U see, daddy is in a critical condition, Heedayah! Daddy baya magana ynxu yayi paralysing" ta fashe da kuka, heedayah tace "mummy? Me paralysing? Kibar kuka pls mummy nima zanyi fa" Mummy ta share hawayenta "daddy baya iya magana, ko tafiya heedayah" hannu heedayah tasa a kunnenta "nooo mummy wasa kke min, my daddy can talk nd walk noooo" tabar gun a guje ko ya akayi bata manta dakin daddy ba oho dan heedayah batada mantuwa dakinsa ta wuce straight kafin su mummy suce pim. Tana shiga ta hango daddy'nta a kwance kan gado da hawaye na bin fuskarsa tasa lock a kofar takarasa kansa da gudu tafadi a kanshi "daddy nooo pls daddy u promise to always stand by my side, kace u'll never leave me, remember? I want my daddy, plss dady" kuka takeyi sosai daddy naganinta amman ba abinda ze iyayi se hawaye sanda tayi kuka sosai sannan ta dago jajayen idanunta ta share hawayenta, ta share na daddy tace "daddy listen to me I promise sena rama maka abinda baban muhammad yamaka, zanje in tambayi antinmu me mutum yake karantawa ya iya kama criminals nd I promise sena kamasu na kaisu prison har su mutu a can" (ji yadda heedayah ke magana kamar ba yarinya ba). Su mummy suna isowa dakin taga a rufe mal idi yafara kokarin budewa tace "let her be" suka nemi gu suka zauna se kuka takeyi a hankali.
Alhj lawal na zaune a parloun gdnsa da files na gdaje, filaye, companies, na alhj s.u agabansa ya sakar dawata dariyan mugunta sannan yadau wayarsa ya kira alhj ismail bugun farko ya daga ya gaishesa alhj lawal yace "bar duk abinda kakeyi kazo I need u now!" Baki na rawa alhj ismail yace "yes alhj gani nan zuwa yi hakuri pls." Kamar kyaftawan ido sega alhj ismail a gdan alhj lawal ya durqushe ya gaishesa alhj lawal yace "hau kujera ka zauna magana zamui nd inason kbani hnkalinka dan abu zansa kamin nd banason failure"
[10/10, 1:31 PM] ????????????Salma????????????: ????????????????????????????????????
HEEDAYAH!
????????????????????????????????????
1⃣9⃣
written by miemie????
"Ko kana da labarin alhj s.u na asibiti?" Alhj ismail ya gyada kai, alhj lawal ya cigaba "toh kasani bara muje dubansa ba, daga mu har iyalan mu bawanda zeje dubansa, kaji ai?" Alhj ismail zeyi mgn knan alhj lawal yace "ko bakaji bane" alhj ismail yace naji, alhj lawal yayi yar murmushi sannan yace "zan baka files na gdan alhj s.u dayake ciki ynxu kaje ka siyar" Alhj ismail ya zaro ido sannan yace "kar mu masa haka pls mun kwato campany nasa da sauran filaye ai ya ishemu ba se mun sai masa da gdan dayake ciki ba, for goodnake sake su koma ina?" Alhj lawal ya buga table "ni nake ma magna kana kin ji?" A zuciya yace "lallai se malam ya dado min wanga magani" jiki na rawa alhj ismail yace "yi hakuri i'll do as you say" alhj lawal ya miko masa file din gdan yace "goodluck, you can go now" alhj ismail na ficewa alhj lawal ya zarce side na matarsa ya sameta kwance kan gado tana kallo suka gaisa yake ce mata ta shirya zasu je duban alhj s.u bai da lafya, tace "ayya ai banda labari barin kira mumyn heedayah" ya ce "toh kiyi sauri" yana fita takira mumy'n heedayah suka gaisa ta tambayeta ya jikin daddy? Mummy tace "da sauki" umman mustapha (matar alhj lawal) taba mummy hakuri kan rashin zuwan da tayi cuz bata san daddy baida lfya bane ynxu zata kira maman muhammad (matar alhj ismail) ta sanarda ita halan su shigo tare ma ahaka ta katse wayar. Ta kira maman don moha suka gaisa take fada mata, maman don moha ta tausaya wa mummy matuka tace itama zata shigo anjima sukayi sallama, alhj ismail mijinta taje tasamu yana zaune a garden take gaya masa kan zata fita anjima zataje gaishe da daddy'n heedayah da jiki ko zamuje tare ne?, alhj ismail yace "ba inda zakije" tamasa rokon duniya ya hanata haka takoma ciki amman de tasa a bayan mind nata se taje koda bada izininsa ba, ace duk yadda suke da mummy'n heedayah mijinta ba lafya yace barataje dubanta ba ai ba ta kyauta ba.
Alhj lawal, dansa mustapha da matarsa na hango a asibitin da akayi admitting daddy da manya manyan ledoji guda 2 a hannun matarsa, yasa ta kira mummy, mummy ta musu kwatancan dakin suka kariso suka gaggaisa kowa yaga daddy seya tausaya masa harta alhj lawal dinma beji dadin ganin amininsa a condition haka ba amman ya ya iya da son zuciya, umman mustpha ta tambaya "ina heedayah ne banganta ba?" Mummy tace "ai bata jima da barin nan ba" umman mautapha tace "ayya ashafa min kanta" bayan like 15mins da zuwansu alhj lawal yace "zasu tafi" a daidai lokacin daddy ya tashy daga yar baccin da yakeyi yana ganin alhj lawal jikinsa ya soma rawa mummy suka rasa meke faruwa, shide alhj lawal yaja baki yayi kum dake yasan dalilin hakan, mummy duk ta kidime tarasa nayi can tace bari taje ta kira dr, alhj lawal yace "kar ta damu magana alhj ismail keson masa sesa jikinsa ke rawa" ya karasa gun alhj ismail da har ynxu jikinsa rawa yakeyi yace "dan uwa try not to talk nagane me kake nufi, Ina company dinka dake abuja neko? Nxt week zan shiga abuja in shaa allah in kula maka dashy kaide Allah baka lafya kawai, sannu" yadawo da kallonsa kan matarsa yace "mutafi ko?" suka aje wa mummy ledojin tayi godia sosai ta musu rakiya sannan ta dawo ciki. Data dawo ta karisa gun daddy tana nuna masa ledojin da alhj lawal yakawo se yaba hankalinsa take, shiko se kokarin magana yakeyi yace mata "karta amsa, alhj lawal munafiki ne" amman ya kasa, mummy kuwa tace "try not talk yace zeje maka company din ya duba ai nasan alhj lawal da kirki he won't let you down" Haka har dare yyi maman don moha batasamu daman zuwa ba dake alhj ismail a gda ya wuni ranan, can dare ta kira mummy ta gaishe ta sannan tabata hakuri kan bata samu daman fita yau ba amman in shaa Allah gbe zata zo, mummy tace "ba komai, Allah kaimu" maman don moha tace "ya jikin maigidan?" Mummy tace "toh da sauki nakega gobe ma za'a sallamemu cuz gbe maganinsa zasu iso" maman don moha tace "ahh alhamdulillah in shaa Allah zan shigo kamin ayi discharging naku din, Allah bashi lafya" mummy ta amsa da "ameen nagode se da safe" tayi hanging.
Heedayah na zaune akan study table nata da assignmnts nata a gabanta amman ko kadan hankalinta bai gun har nanny tashigo dakin bata sani ba, "heedayah!" Nanny takira sannan ta dawo hankalinta, nanny ta kariso kusa da ita tace "heedayah ki rage tunanin daddy'nki in shaa Allah ze samu lafya ba kina mishi addu'a ba?" Heedayah ta gyada kai can setace "nanny can I trust you?" Nanny tace "sure my heedayah wani abu ne?" Heedayah tace "nanny daddy'n don moha ne yasa daddy ya dena magana da motsi" nanny ta zaro ido waje "heedayah! Ya kke magana haka? Daddy'nki ba frnd na daddy'n don moha bane, mesa ze masa mugunta?" Heedayah tace "nanny believe me" tayi tayi da nanny ta saurareta amman ina nanny taki sauraronta dan ita kwata kwata maganan bekama kwakwalwarta ba ace yadda alhj ismail ke son daddy ne za'a ce ze masa haka? Gaskia karya ne. Ahaka ta taya hedayah tagama assignments nata tayi sallah sannan ta kwantar da ita.
[10/10, 1:31 PM] ????????????Salma????????????: ????????????????????????????????????
HEEDAYAH!
????????????????????????????????????
2⃣0⃣
written by miemie????
As usual yau da safe nanny tashirya heedayah sch 7:30AM yamata a sch. Sannan nanny ta fara shirya wasu mummy breakfast to 9:00AM tagama tayi wanka tadan kimtsa gdan mal idi yyi dropping nata a asibitin tagaishe da mummy sannan taciro breakfast din tayi serving nasu, mummy naci tana bama daddy ahaka har suka koshi. Around 10:30AM alert yashigo wayar mummy na delivery na maganin daddy nan da nan ta aika mal idi yaje ya amso yana dawowa batare da bata lokaci ba mummy taje yiwa dr magana kan yayi discharging nasu ga maganin da sun iso sede kash dataje dr bai nan so dan dolenta ta dawo dakin tana jiran dawowarsa, wayarta ce tasake ringing maman don moha ke kira ta daha suka gaisa tamata kwatancan dakin daddy nan danan tashigo daman tana kusa da gun suka kuma gaisawa ta tausaya wa daddy sosai ko 10mins batayi ba tace zata tafi ta ajiye wa mummy wata katuwar leda itama, mummy tayi godiya sosai tace "ki gaishe dasu muhammad da daddy'nsu" maman don moha tace kinga har na manta ba wlh dady'nsu baijin dadi ne sosai sesa besamu ya fito ba" mummy tace "ayya shima! Toh Allah basu lfya" maman don moha ta amsa da "ameen se anjima zan wuce office se waya ake tamun zan biyo tanan ma kafin inwuce gda in natashy frm work" mummy tayi murmushi sannan tace "kekam baki gajiya wallah, ai zuwanki ynxu ma yayi sosai Allah biya, har kin manta yau zaayi dischargibg namu ai dr din yafita amman yana dawowa ze sallamemu" maman don moha tace "toh shknan Allah bama alhj lafya, ni na tafi" mummy tace "ameen mungode". Dr na dawowa ya sallami su mummy tare da musu fatan alheri, mummy ta biya bills din suka dawo gda. Nan nanny tashiga hada lunch mummy kuwa ta yi ma daddy wanka ta sa masa light jallabiya ta feshe sa da turare sannan ta zaunar dashy kan wata hadaddiyar wheelchair nasa data masa ordering from ali express ta jasa zuwa parlour takaisa ta bakin kofa yana dan kalle kalle sannan ta wuce daki hado masa maganinsa she's very careful dan kar maganin yakuma fashewa yana gama sha nanny ta sauke abinci mummy tabasa yaci sannan tayi wanka itama pes! Lokacin daukan heedayah nayi ta dauko mayafinta taje daukota, heedayah tayi murnan ganin mummy'nta sosai classmates nata har mamaki abin yabasu heedayah da ta kwana biyu bata dariya ji yadda take wage baki yau, se surutu heedayah kema mummy acikin mota ahaka har suka isa gda tafito tana shiga parlour taga daddy'nta zaune kan wheelchair nasa kamar wanda zakace taso ya mike, ta karisa gunsa da gudu tayi hugging nasa tightly "i miss you daddy" murmushi kawai daddy ke iya yi. Da daddare su mummy duka suna zaune a parlour ta tashy ta wuce dakin heedayah taga batta nan amman taji motsi a bangida ta jawo kofar tana juywa suka ci karo da nanny, nanny tace "mummy'n heedayah akoi maganar danakeson miki" mummy tayi murmushi "nima ai nanny zo muje dakina" suka wuce, mummy tace "wai nikam dana barki ranan da daddy'n heedayah meya faru ne?" Nan nanny tayi wa mummy narrating duk abinda tasani bata bar komi ba amman de ta boye wa mummy part din da heedayah ta gaya mata, mummy tace "toh fa bari heedayah'n tafito muji daga bakinta" bayan 3mins heedayah tafito ta sauko kasa nanny tace mata "kije mummy na kiranki tana dakinta" heedayah ta amsa da "toh" ta wuce dakin mummy, tna shiga ta karisa gun mummy, mummy ta zaunar da ita kan cinya tace "mummy's princess nikam rananda muka kai daddy asibiti meya samesa? Nanny tace min ke tasamu akansa kina kuka, meya faru kke kukan?" Duk sanda heedayah tace zatayi magna seta rika tuna abinda akhj ismail yagayamata nacewa ze pille kanta in tafada ma wani abinda taji, mummy tagano heedayah batason tafadi abinda tasani ta riko fuskarta tace "trust me kinji gayamun duk abinda kka sani kinji my princesd?" Heedayah tace "ni mummy all I know is daddy'n don moha ne yasa daddy yadena mgn da tafiya"(but takasa gaya mata abubuwan dataji daga abakin alhj ismail) mummy ta zaro ido "heedayah! Kinsan me kke fadi kuwa?" Heedayah tace "eh mummy shine, dagaske ba karya nake miki ba" mummy tace "toh shknan jeki sami daddy a parlour thank you for telling me" heedayah na fita mummy tafara safa da marwa acikin dakin "tabbas yaro bai qarya inyafadi abu it might be yaji ne ko ya gani but why is it hard for me to believe heedayah? Taya? Alhj ismail zeyi wa daddy haka, kai gaskia a'a dan a iya zaman da mukayi da alhj ismail da alhj lawal, alhj ismail ma kamar yafi son daddy akan alhj lawal, toh! Ko ba son tsakani da Allah dama yake masa ba? Kaii nooo son tsakani da Allah ne bt kuma akoi abin lura anan, meya hana alhj ismail zuwa gaishe da daddy?" Wata zuciyar tace mata "ha'a ba matarsa ta gaya miki baida lafya ba? Ai barata miki qarya ba"
[10/10, 1:31 PM] ????????????Salma????????????: ????????????????????????????????????
HEEDAYAH!
????????????????????????????????????
2⃣1⃣
written by miemie????
Da kyar ta iya tayi getting rid of tunanin a mind nata, taje tasamu su daddy a parlour tayi joinimg masu suna kallo amman fa hankalinta ba akan kallon yake ba, around 10:00pm duk sukayi seda safe kowa ya wuce dakinsa. Yau ma kamar kullum nanny ta shirya heedayah sch, atare suka isa da su don moha tana ganinsa ta fara tafiya da sauri dan kar ya mata magana, gudu yayi sannan ya iso ta ya riko hannunta ta wabce tace "muhammad leave me alone" don moha yaji mamaki sosai, "heedayah pls mena miki kke avoiding dina, atleast ki gaya mun menayi nd stop avoiding me dan Allah" heedayah ta watso masa harara "wallahi don moha in baka barni ba i'll report u to the principal's office" takama hanyan tafiya kafafunsa kasa rikesa sukayi ya sulale kasa dakyar yasamu ya tattara kansa yayi class, haka ya wuni a sch ranan so dull ba walwala a tattare dashy. Bayan da aka tashy heedayah taje tasamu aunty'nsu "ma'am what will I study in order to become somebody in the future who can arrest criminals?" Aunty'nsu tace "heedayah why are u asking?" Heedayah tace "i just want to be one" aunty tace "but u said u want to be a doctor, why have u changed ur mind?" Heedayah tace "just cuz..." Sekuma tayi shiru anty tayi murmushi "well to become someone who can arrest criminals u have to go through a law sch..." haka de ta ta ma heedayah bayani daga karshe tace "then u can now decide weather to charge a person or not after becoming A PROSECUTOR" heedayah tamata godiya sannan ta fice tabar aunty cike da mamaki dan a gaskiya heedayah na burgeta sosai kominta daban yake is like she's unique. Bayan anzo daukan heedayah sukata hira acikin mota ita da mal idi har suka isa gda, tayi dakin daddy tayi hugging nasa taga ba mummy a dakin tace "daddy yau na tambayi auntinmu me mutum ze karanta ya iya kama criminals tace min zan je law sch se inzama PROSECUTOR kaga inna zama se in kama daddy'n don moha mukaisa prison ko daddy?" Daddy yamata murmushi ta dau jakarta ta fice sukaci karo da mummy, mummy tayi hugging nata sannan ta wuce dakinta ta canza kaya ta sauko taci abinci. Haka de rayuwa ta ciagaba da kasancewa daddy da family'nsa, mummy batta wasa da maganin daddy jiki de har ynxu gashi nan ba improvement. Don moha kuwa kusan sau uku yana zuwa gdansu heedayah amman taki kulasa har ya gaji yabari hakan kuwa ba karamin affecting dinsa yayi ba, heedayah ma kwata kwata bata jin dadin abinda take masa amman ya ta iya? She can't forgive him for his dad's mistake, daddy'nshi ne yaso kashe daddy'nta, nanny tayi tayi da heedayah ta dena blaming don moha for his father's fault duda they are not so sure daddy'n don moha ne cause din rashin lafyan daddy amman heedayah taki jinta.
*Bayan sati daya,* yau ya kasance thursday heedayah na sch a yayinda mummy ke office tabar care din daddy gun nanny. Alhj lawal da alhj ismail na hango a gdan shi alhj lawal din, alhj ismail yace "yallaboi gashy mun samu wanda zasu siye gdan" alhj lawal yace "ahh to aikinka yayi kyau, ynxu kasan me nakeso da kai?" Alhj ismail ya girgiza masa kai da alaman a'a, alhj lawal yace "zakaje da wanda zasu sayi gdan, gdan alhj s.u ka nuna musu cikin am sure wajen dama ka nuna musu ko? " alhj lawal yace "eh amman yallaboi ai zan tauna mana asiri inna je gdan nasu dan zasu ganni gaskia baranje ba, muba ma wanda ze siyan file din gdan kawai yaje dashy ya nuna musu" alhj lawal yaja tsuka "kaifa baka da wayo Allah, taya zamu basa file din gdan? Ba seya gudu dashy ba, dolenka zakaje da shy kuma..." Alhj ismail ya katse sa "nifa baranje ba alhj" alhj lawal yayi murmushi daman already ya amso maganinsa gun bokansa ya sa acikin ruwan yace "toh shknan ni zanje, ga ruwa kasha ana zafi" ya zuzzuba musu a kofi kowa yakai baki alhj ismail yafara sha alhj lawal kuwa ya makale nasa a lebe kawai, alhj ismail nagama kurbewa bayan like 15mins alhj lawal yace "soo ya yanzun zaka je?" Alhj ismail yace "eh sosai alhj zamuje gdan alhj s.u mu saida gdansa" suka zarce da dariyan mugunta dukansu***
Around 3:00pm su mummy suna zaune a garden dukansu me gadi yazo yacemata tayi baqi tace ya kariso dasu, alhj ismail dawasu maza biyu naga, wanda a kalla dayan zeyi 48yrs dayan kuma 55yrs haka, mummy tamusu sannu dazuwa, heedayah na ganin dady'n don moha tashiga tsoro shiko duk sanda suka hada ido seya mata murmushi, daddy kuwa jikinsa yafara rawa sosai dakyar mummy tayi calming nasa down, da wayo mummy ta kora heedayah ciki amman dan wayo irin na heedayah taqi shiga ciki ta labe daga wani lungu tana jinsu. Alhj ismail yace "ya jikin dan uwan nawa?" Mummy tace "da sauki" da har zata tambayesa ya jikinsa sekuma ta fasa. Ya ja numfashy sannan yace "hajia hafsat" ta amsa da "naam" yace "kinga wadan nan mutane?" Mummy tace "eh mun gaisa ai wani abu ne?" Alhj ismail yace "gdan nan zasu siye ko ince sun riga sun siye sun zo duba ne" mummy ta zaro ido "ehh? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Alhj ismail wata erin banzan magana kake ne? Ta ya zaka siyar mana da gda? Dama du zaman da mukayi dakai ba tsakani da Allah bane? Toh wlh kayi qarya, nd kasani baraka taba siyar mana da gda ba sbd files na gdan ga ba a gunka suke ba suna gun mijina, mutumin banza amman Allah wadar din erin ku wlh kaji kunya mstww, ku tashy kubar min gda or else in kira police suzo su tafi daku wllh kaji na rantse" alhj ismail yayi murmushi sannan yace "me yayi zafi hajiya hafsa? Zamu tafi but tukuna" yasa hannu cikin aljihu ya ciro wata paper ya miqa wa mummy tasa hannu ta karba da full confidence dinta, abinda tagani cikin takardan ne yamun razana ta ba shakka wannan signature din daddy ne akan sunan alhj ismail da shaidar ya mallaka ma alhj ismail gdan nan nasa da yake ciki, da kyar mummy tayi gathering evidence tace "toh se meh? Wannan paper is not real" alhj ismail yace "dont decieve urself maman heedayah ke yar boko ce wanga paper is real tun wuri ku fara tattara kayakinku dan mutanennan suna bani kudi na i have no other option than in fita daku na karfi daga gdan nan" yasa hannu ya wabje paper'n yace da mutanen nasa "mutafi"
[10/10, 1:31 PM] ????????????Salma????????????: ????????????????????????????????????
HEEDAYAH!
????????????????????????????????????
2⃣2⃣
written by miemie????
Suka kama hanya suka fice heedayah ta bisu da kallo, kafafun mummy kasa daukarta sukayi jin kanta kawai tayi a qasa, ba abinda takeyi se hawaye haka daddy ma heedayah ta kariso gun da gudu tayi kan mummy tana gogemata hawaye "bar kuka mummy na" mummy tace "heedayah take ur daddy inside" heedayah batayi musu ba ta tashi taja daddy'nta suka shiga ciki tace "daddy na bar kuka, kar ka kula daddy'n don moha dinnan ya cinye gdan in ana cinyewa ba kana da gdaje dayawa ba semu koma sharada ai ko GRA, bar kuka kaji daddy na?" Tasa hannu ta goge masa hawaye zuciyar daddy radadi take masa sosai kasa rikewa yayi jikinsa ta hau rawa sosai can anjima yabar motsi heedayah ta kwala ihu atake mummy da nanny suka iso parloun "heedayah meya faru??" Kasa fadin komi heedayah tayi se kukan datakeyi tana nuna daddy da yatsa mummy sukayi kansa ta tabbatar da daddy baiya numfashy tana kuka ta dau wayarta ta kira family dr dinsu yace gashy nan zuwa nan da nan ya iso yabama daddy immediate treatment yace "ma'am akoi dan abubuwan dayakamata kuna avoiding inbahaka ba rashin lafyan alhj will only get worse," mummy tace "ina jinka dr," dr yace "ma'am na farko, kudena yawan masa maganganun dazasu ringa tsinka masa zuciya, na biyu kudena yawan sasa kuka, hasali ma duk abinda kukasan baida dadin ji kudena fada masa" mummy tace "toh dr nagode in shaa Allah it won't happen again," dr yamusu fatan alheri sannan ya fice. Can guessroom dake sama mummy ta haura ta shige bangida ta rufe kofar ta ringa kuka kamar ba gobe batasan kuma ina zata sa kanta ba gashy abbanta bayya nan, if only yana raye da shi kadai ze iya cire ta acikin tsaka me wuyan da take ciki ynxu, kwata kawata ta manta daddy nada gdaje bayan wanda suke ciki, haka tata kuka a bangdan can heedayah taji shiru ta shiga neman mummy har Allah ya kawo ta dakin taji karan kuka a bangida ta karasa tana kokarin budewa amman yaqi buduwa, "mummy open the door, pls kibar kukan pls" itama ta fashe da kuka uwa nayi 'yan nayi miemie na gefe tana miqa musu tissue, tausayin heedayah ne yakama mummy sosai dan a 'yar shekarunta bekamata ace tana facing problems da tension haka ba, ta budo kofar heedayah tayi hugging nata tightly munmy tace "is okay my princess kukan ya isa haka kinji? Everythng is gonna be fine jekiyi sallah ki kwanta kinji?" Heedayah ta dago jajayen idanunta tace "mummy wai daddy'n don moha ya ce mufita mubar gdan nan?" Mummy ta share yar kwallarta "waya gaya miki?" Heedayah tace "ni naji da kunne na" mummy tace "heedayah listen to me, kinga banson wannan abu yayi affecting naki, karki kula daddy'n muhammad zamu bar masa gdan ai akoi Allah ko?" Heedayah ta gyada kai mummy ta cigaba "good semuta addu'a Allah kawo mana karshen wannan abu, zan nemo mana new home semu koma ciki ko?" Heedayah tace "ai ba sekin siya mana new home ba mummy, daddy yacemun yana da wani gda a sharada da GRA" se ynxu hankalin mummy yadawo jikinta ta tuna tace "heedayah Allah miki albarka ynxu zo muje daki muyi alwala muyi sallah seki huta ko?" Suka fice bayan sun idda sallah sunyi addu'a sosai mummy tasa heedayah baccin dole amman ina heedayah taki a tare suka koma daki suka sami daddy kwance akan gado da hawaye na gangara akan fuskarsa suka karasa kansa mummy tasa hannu ta goge masa hawayen tace "habibi kukan ya isa kaga dr yace kadena kuka u'll worsen ur situation ya isa pls" ta tashy ta fara duban wardrobe ta inda daddy ke ajiye files nasa taga gun wayam! Ba komi hankalinta ya kuma tashy daddy yafara motsa jiki, heedayah tace "mummy daddy nason yafadi wani abu," mummy takaraso tace "habibi wani abu ne?" Girgiza kai kawai daddy keyi da alaman a'a mummy tace "a'a meh?" Se faman jijiqa kai daddy keyi yana kokarin daga hannunsa amman yakasa sede in aka sa hankali za'a gano gun da yake aje files nasa yake kokarin nunawa, mummy tace "ba files din?" Ya gyada mata kai, tace "toh na ina? Ina ka kai?"Jijiqa kai kawai yake tayi can mummy tace "ko duka files nakan ne babu kaba alhj ismail?" Daddy ya gyada kai a hankali yafara zubda hawaye, wani tokari mummy tajiyo a zuciyarta shiknan nata ya kare kuma, takuma tambayansa ya kuma gyada mata kai heedayah tafara maganan zuciya "in ta haka envelope dana gani a hannun daddy'n don moha shine wanda mumy ke nema knan" mummy tasa hannu ta gogewa daddy hawayensa sannan tace "if only... Habibi if only zaka iya gayamun mesa kaba ma wannan mugun mutumin daka dauka abokinka ne dukiyar ka kab ba tare da kayi shawara dani ba, bansan ina zan kaimu ba ynxu, abbana bayida rai, aikina bawani salary babba bane da har zan iya biya mana kudin haya, innalillahi, sede dan abinda na samu acikin gado na, Ya Allah ka kawo min qarshen wannan masifa" ta soma maganan zuciya "Alhj lawal is my only hope ynxu, dole in kirasa in masa bayani ko ze iya taimaka mun" nan tabar maganan zuci tace "heedayah miqo min wayar daddy da tawa" heedayah ta miqo mata ta lailmo number'n alh lawal a wayar daddy sannan ta dura acikin wayarta tayi dialing ringing sau uku yayi alhj lawal ya daga "assalamu alaikum"...
To masu karatu ko wani munafincin kuma alhj lawal ze kulla se Allah kubiyoni dan ji…
[10/10, 1:31 PM] ????????????Salma????????????: ????????????????????????????????????
HEEDAYAH!
????????????????????????????????????
2⃣3⃣
written by miemie????
Mummy ta tashy tabar dakin, heedayah zata bita daddy ya mata nuni da kai da alaman karta bita ta zauna, haka ta zauna amman hankalinta nakan mummy. Mummy ta amsa sallamar alhj lawal "wa alaikumussalam, ina wuni?" Ya amsa a takaice tamasa bayanin ko wace ita, yace "Allah sarki hjy hafsa, ya jikin me gdan?" Ta amsa da "da sauki, alhj lawal taimako zakamin dan Allah" ta fara kuka, alhj lawal yace "anything for you hjya, ina jinki" mummy ta labarta masa labarin bata bar komi ba alhj lawal yace "incompetence! Karya ne wlh, taya ze sayar muku da gda? Wato dan alhj s.u ya yarda dashy ya bashi amanan arzikinsa shine ze saqa masa da butulci ko? Toh wlh yayi karya kar ki damu hjy hafsa kude ku dage da addu'a nima zan saku aciki in shaa Allah bare siyar muku da gda ba, i'll try to talk to him, ynxu ma zan je gdansa..." Mummy tana kabary ko gbe kaje, alhj lawal da munafirci yana a'a hjy kibary inje ynzu(lol) "ki gaishe da alhj" mummy tace "nagode sosai alhj lawal zeji nima agaishe mun da umman mustapha" ya amsa da "toh" sannan yayi hanging. Nan mummy ta share hawayenta ta koma daki, alhj lawal ya sakar dawata dariyan mugunta yadda ya saba sannan yace "hajiya hafsa knan! Tun ba ayi nisa ba karfin ki ya kare hahahah Allah sarki"*** heedayah tace mummy ina kkaje? Mummy tace "babu alhj lawal na kira da ya taimaka mana..." daddy yafara jijiqa mata kai kamar yadda ya saba mummy tace "...habibi ni bansan me kake nufi ba kuma, alhj lawal dinne bakason mu nemi taimako gunsa?" Daddy ya gyada kai mummy ta cigaba "to gun wa kakeson munemi taimakon? kana gani de ni banda kowa shikadai ne hope namu, ai shi yanada kirki bakaman wancan la'ancaccen dan uwan naka yake ba"**** can dare alhj lawal yayi calling back mummy yake gaya mata ai ba yadda ya iya cuz is already too late, daddy ya riga ya ma alhj ismail signing papers din ko kotu sukaje bara'a sauraresu ba, mummy tamasa godia sannan ta katse wayar jikinta duk ya gama mutuwa ji take kamar tasa hannu a ka tayi ihu amman ta miqa wa Allah al'amarin dan for sure tasan yanada reason din musu hakan. PA'n daddy takira tace masa da ya nemo almajirai suje su wanke mata gdan da abbanta ya bata dake danjuma goje gobe ya amsa da "toh".
Abubuwa sunyi wa mummy yawa kwata kwata tafita daga kamanninta, heedayah kuwa tadena concentrating a makaranta kullum hankalinta nakan daddy'nta da daddy'n don moha ahaka aka sa date da zasu fara exams na third term in one week time, hakan kuwa yayi daidai da time da su mummy suka fara packing dake alhj lawal yakuma tura alhj ismail daya tuna ma mummy suyi subar gdan cuz wanda zasu dauki gda sun riga sun bada kudi. Yau ya kasance wednesday, bayan heedayah ta dawo frm sch suna zaune a dakin mummy suna packing kayakinsu, mummy tayi jugum heedayah ta taba ta "mummy kibar damuwa kinji? Ba muna addu'a ba? Allah ze amsa mana addu'an mu yarama mana abinda daddy'n don moha ya mana ai" mummy ta kirkiro murmushin dole tace "in shaa Allah my little princess kin gaji war haka ko? Bari nida nanny mu gama packing sauran kayan jeki huta kiyi karatu kinji? Kinga kuna exams nd promtional exams ne you have to read" heedayah taqi tace da ita za'a gama haka mummy ta barta se bayan maghrib suka dan huta sannan suka cigaba, sun sha rabin aikin kak gaskia cuz a yanxu hka sauran musu dakin heedayah, dakin daddy da parlour ne sun riga sun gama da kitchen, stores, dakin nanny, guestroom, dinning space.
As usual yau da safe nanny ta shirya heedayah sch. Around 10:15AM bayan mummy tafita aiki wasu armed robbers(manyan barayi) suka paso gdansu heedayah suka ma me gadi dukan tsiya harda buga masa gindin bindiga a ka, nanny tana kitchen tana dan chopping albasa itama aka nausheta a ciki take ta fadi a gun, dakin daddy suka soma shiga suka samesa zaune yana kallon news basu taba sa ba illa drawers da wardrobe da suka shiga budewa suna ciro kudade, can dayan ya lalimo drawern key din motocin gdan, sukayi searching so hard amman sun kasa gano ina mumy ke aje gwala gwalanta dake bata ajewa a gda can banki take kaiwa inda Allah yasota knan, bayan haka suka babballo plasma TV's dake gdan kap da sauran abubuwan showglass sannan suka fice, daya daga cikinsu yaja sumemmiyar jikin me gadi cikin dakinsa. sun kai kusan su shida suka dibi motoci guda shida cike da kayakin da suka sato, kwata kwata mota daya suka rage wa mummy dan iskanci wata baqar honda accord V8 suka fice daga gdan suka bar gate fangalan a bude. Daddy tun yana hawaye jikinsa na rawa yabar motsi shima kwata kwata
[10/10, 1:31 PM] ????????????Salma????????????: ????????????????????????????????????
HEEDAYAH!
????????????????????????????????????
2⃣4⃣
written by miemie????
Bayan like 30mins da tafiyan barayin, nanny tadan lumshe ido da taimakon table dake tsakiyan kitchen din ta riqe ta miqe da hannunta riqe da cikinta tana ma kitchen din wani erin kallo nan ta tuna meya faru sunan alhj kawai takira da karfi ta ruga a guje dakin daddy tagansa bayya motsi salati ta hauyi jiki na qyarma ta kira mummy a waya tana kuka "mummy ki zo gda, kizo gda, gda ba lafya barayi sun shigo sun mana fashi, alhj baya motsi" ta fashe da kuka... Mummy tace "what!?? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" kasa daukanta kafafunta sukayi ta sulale qasa salati kawai take ta nanatawa har na tsawon mituna uku sannan da kyar ta tashy tabar office dinta a guje key kawai ta dauka ta fice, Allah ne kawai ya kawota gda lafya dan wata erin wawiyar driving da takeyi a bude wangalau tasamu gate na gdanta daidai bakin kofar parlour tayi packing ta fito ko rufe kofar batayi ba hasali ma a kunne ta barta ta shigo ciki da saurin gaske abinda tafara cin karo dashy shine ba TV'nta, tana kai ido kan showglass taga du an kwashe abinda ke ciki hannu kawai tasa kan bakinta ta karasa dakin daddy tasamu nanny a gefe ta rike ciki tana kuka, daddy kuwa na kan wheelchair nasa a sume wayarta ta gwada lalima taji ba alamarta nan ta tuna tabar wayar a office ta kira sunan nanny, nanny tadago jajayen idanunta "mummy har kin iso ki kira likita...wayyo cikina" mummy tace bani wayarki ta karisa ta amsa Allah yaso ma ta haddace numban family dr din, nan da nan ta kirasa ya iso ya duba daddy da nanny yabasu immediate care ba abinda mummy ke shararawa se kuka, shide dr yamata jaje yakuma bata hkr sannan ya fice. Haka har lokacin daukan heedayah yayi mummy bata sani ba se kuka take shararawa can bayan 30mins da tashinsu heedayah ta tuna gashy barata iya fitaba dan haka ta kira driver da wayan nanny kan yaje ya dauko heedayah frm sch batare da ta gaya masa dalili ba, driver kuwa a hanyan dauko heedayah wasu barayi suka tsare sa ni miemie nace wannan barayi sunyi kalan wanda suka kai fashy gdan alhj s.u daxu, suka ma mal idi tsinannen duka sannan suka kwace motarsa suka kara mai, da kyar mal idi yasamu ya lalimo wayarsa upon all dukan da suka masa ahaka yayi karfin hali yakira numban mummy har yagama ringing bata daga ba yakuma mata wata missed call din sannan ya kirata da numban nanny nanne ta daga, ahankali yake maganar "haj..i..ya yan ta'ada kije ki dauko heedayah" mummy tace "whaat!???" Kana ina? Da kyar ya iya cemata "hotoro" tace "toh keep calm, ga ni nan zuwa" nanny tana tambayar ta meke faruwa amman bata ko amsa taba tafita a gigice se hotoro can ta hango mal idi a kasa ta karasa yasamu ya tashy da kyar mummy take tambyarshi ze iya kaiwa har a dauko heedayah? Ya amsa da "eh" amman de da anga condition nasa an san bare iya ba dan jikinsa duk yoyon jini yakeyi sbd gardaman da yyi wa barayin suka shasa sosai, reverse kawai mummy tayi sukayi asibiti akayi emergency dashy tace wa dr din zataje dauko 'yarta a makaranta ta fice, heedayah har tagaji da jiran mummy tafara kuka, tana cikin raira kukanta a hankali mummy tace "am so sorry my little princess yi hakuri am late kinji?" Ta dagota ta riko mata jakarta suka kama tafiya, maimakon su wuce gda se heedayah taga mummy nabin wata hanyar daban dan haka ta tambayeta "mummy ina zamuje?" Mummy tace "asibiti heedayah, barayi sun tsare idi a hanya sun masa duka sun kwace motarki" heedayah tazaro dara daran idanunta tace "mummy! Prado dina?" Mummy tace "eh heedayah, ke akan ki tambayi jikin idi ma motarkice ta dame ki?" Heedayah ta maraice sannan tace "toh ya jikin mal idi?" Mummy tace "bari mu karisa asibitin muji" nan da nan suka isa aka tabbatar mata da cewa mal idi beji internal injuries ba kawai external ne nd anyi treating nasu, nanne mummy ta sauke a jiyar zuciya tabiya kudin treatment nasa da kudin magani sannan suka dawo gda, tun isarsu bakin gate heedayah da mal idi suka sake baki mal idi yace "hajiya meke faruwa?? Gate a bude kuma ba motoci a gdan" mummy bata ce masa komi ba dan haka yaja bakinsa yayi tsit, heedayah kuwa har yoyon miyau bakinta yafara ahaka mummy ta nemi gu tayi parking suka fiffito, mummy tashige ciki dan takaici heedayah kuwa da mal idi se kallon gdan kowan nensu keyi ko zasu ga motocin amman ina! Heedayah ta nemi gu ta zauna can inda ake parking motoci shikuma mal idi ya shiga ciki, hawaye a hankali heedayah ke zubarwa kaman daga sama taga hannu daga dakin me gadi wata ihu ta sakar duk su mummy suka fito suna tambayarta mene? Dakin me gadi kawai take nuna musu da 'yatsarta mal idi ya karasa yaga mal musa me gadi kansa du yana zuban jini salati ya sakar, su mummy sukayi kansa da heedayah mummy na salati mal idi nayi**** Alhj lawal da alhj ismail suna zaune a gdan shi alhj ismail se dariyan mugunta sukeyi ana cikin haka wayar alhj lawal tayi qara ya duba...
[10/10, 1:31 PM] ????????????Salma????????????: ????????????????????????????????????
HEEDAYAH!
????????????????????????????????????
2⃣5⃣
written by miemie????
Sannan ya daga “hello?” Meshi yace “oga sir! Gashy nan mun gama komi motocin suna inda kace muyi parking nasu, anyi kamar yadda kace honda accord V8 kawai muga ragar musu” alhj lawal yace “aikin ku yayi kyau bari ynxunnan zakaji alert” meshi ya amsa da “toh oga sir godiya muke” yayi hanging. Yace ga alhj ismail “the did is done! Komi is in place ynxu acikin motoci guda shidan nan zamu siyar da duka amman zan baka guda daya” alhj ismail yace “kaifa? Baka so ne? Baraka dau dayan ba kaima” alhj lawal yace nafison ka ne dan uwa na, zan baka TOYOTA PRADO (masu karatu ko zaku iya tuna toyota prado’n da alhj lawal ke son bama alhj ismail itace motar heedayah?) Alhj ismail yace “toh nagode dan uwa”, kallonsa kawai alhj lawal keyi yana murmushi yafara maganan zuciya “Allah sarki dan uwa na, motan nan ba abinda zata kara maka illa tsana dan na tabbata duk sanda hjy hafsa da ‘yarta heedayah suka ganka da motan, se sunji kamar su kasheka”****
Dr yace “toh alhamdulillah nasamu nayi stopping bleeding din nd Allah yaso ba internal bleeding ga magungunan nan se yana sha in shaa Allah shknan, Allah sawaqa” mummy tace “toh dr mungode” ta dawo da kallonta kan mal musa tace “Allah sawwaka sannu” yace “ameen” da kyar. Sannan suka fice masa daga daki sukayi site nasu ita da heedayah. Ciwon cikin nannay yadanyi sauki kadan so takoma kitchen tana girki a yayinda mummy ke zaune a parlour tayi tagumi da hawaye nabin kan kumatunta heedayah na share mata, shigowar matar alhj lawal sukajiyo atake suka jiyo tace “hjy hafsa! Dan Allah kar ki gayamun dagaske ne, barayi sun shigo sun muku aika aika?” Daga idanta da tayi taga ba TV’ a parlourn taga kuma an tattara kayaki cikin kwalaye dayawa kamar ana packing nanfa ta sake kidimewa. Ta kira sunan mummy, mummy ta amsa, tace “wai hjy hafsa meke faruwa? Yana ganki haka?” Mummy tace “barayi ne suka shigo mana da safen nan suka tattara motocin gdannan kap daya suka rage sannan suka sassace duk wani abu me kyau da kkasani agidannan, bayan nan suka ma musa da idi duka” “innalilliahi wa inna ilaihi raji’un” abinda umman mustapha keta fadi knan “shine kuma kke zaune a nan baraki kira police suzo ba?” mummy tayi dariyan takaici sannan tace “suzo suyi me? Zasu iya maido min da motoci nane? Ba abibda zasu iya illa investigation na qarya” umman mustpha ta matuqan tausayawa mumy sosai ta taso tayi hugging nata tana bata hkr ta kuma ce mata ta kwantar da hankalinta zatayi wa mijinta mgn in shaa Allah zai taimaketa, mummy tace ba seta fda ba masa bama tabary kawai umman mustapha tayi insisting sannan ta tambayi mummy “wannan kayaki kuma danaga anata shiryasu cikin kwalaye fa? Lafya?” Mummy tace “packing mukeyi…” kafin ta karasa umman mustapha ta katse ta “Pa…meh? Packing kuje ina? Mesa zaku tashy?” Mummy bataso gaya mata gaskiyar zancen ba tace mata kawai zata canza gda ne tunda barayi sun gano nan din, ba yadda umman mustapha batayi da mummy data hakura su cigaba da zaman su ba amma taqi seda azahar sannan tama mummy sallama ta fice. Isarta gda ta zarce dakin mijinta alhj lawal ta irga masa komi takuma buqacesa daya taimaka wa mummy, alhj lawal kamar dagaske yace wa umman mustapha karta damu he’ll try his possible best harda wai dagani wannan barayi turosu akayi, ki gaya ma kawar taki karta damu za’a kai kara police station ayi invedtigation sosai har se an gano waye master mind dake behind all these mess, umma tamasa godiya sosai nan da nan ta kira mummy ta irga mata yadda sukayi da me gidan ta, mummy tadanji sanyi a ranta sannan ta mata godiya ta ajiye wayar ta cigaba da packing kayakinta dake heedayah na karatu, nanny kuwa cikinta na ciwo. Kiran maman don moha umma tayi ta labarta mata abinda ya faru itama ta tausaya wa mummy matuqa atake ta shirya tazo tamata jaje itama ta roki mummy da tayi hkr ta cigaba da zama kar ta tashy amman mummy taki nd itama bata gaya mata mesa zata bar gdan ba dan tasan muddin tagaya mata auren maman don moha da alhj ismail ze iya samun matasala dan cewa zatayi barata zauna da maci amana kamarsa ba wanda ita mummy barata so hakan ya faru ba, ahaka maman don moha ta taya mummy sukata packing kayakin se bayan la’asar ta koma gda taje tasamu mijinta ta gaya masa meke faruwa be wani nuna mata damuwarsa ba kawai de yace mata “Allah kiyaye aukuwan na gaba” itade mama batasan mesa alhj ismail ke behaving haka ba sekace alhj s.u ba amininsa bane (batasan duk ba a hankalinsa yakeyin abinda yakeyi ba, asiri alhj lawal ya masa)
[10/10, 2:22 PM] ????????????Salma????????????: ????????????????????????????????????
HEEDAYAH!
????????????????????????????????????
2⃣6⃣
written by miemie????