LabaraiMarashi

Hukuma ta yi ram da wani gardi, Musa, mai basaja da sunan mace wurin warwarar kudin attajirai

A ranar Juma’a, 17 ga watan Yunin 2022, ma’aboci amfani da kafar sada zumuntar zamani, Musa L Maje ya je hannun hukuma bayan an gano shi ne ke amfani da suna da hoton Zahra Mansur.

An samu bayanai akan yadda ya dinga tatike samari masu dukiya wadanda su ka dinga tura masa kudade makudai tsawon shekaru 3, sai a ranar Juma’a dubunsa ta cika.

Kamar yadda wani ma’aboci amfani da kafar Facebook, MB Buhari ya bayyana a shafinsa, ya fara ne da cewa zai bai wa jama’a labari, daga nan ya ci gaba da cewa:

Batun yadda Musa L Maje yaje hannun hukuma.

“Wani matashi ya dinga damfarar mata har da maza. Shi ne mai amfani da suna Zahra Mansur a Facebook.”

Kamar yadda ya shaida:

“Wani abokina ya ga wani guntun bidiyon wata budurwa a wayar Musa. Musa ya dauki bidiyon ne ba tare da budurwar ta sani ba. Ba wani bidiyo marar kyau can bane, kawai dai kanta a bude yake.

“A ranar Talata ya sanar da ita cewa ya ga bidiyon a wayar Musa. Ta yi matukar razana. Sai aka sanar da mu. Hakan yasa muka yanke shawarar kawo karshen halayyarsa da taimakon jami’an tsaro amma shi bai sani ba.

“Mun nemi budurwar ta kira shi ta sanar da shi cewa tana Kano kuma tana son ganinsa. Musa ya yi matukar jindadi don ya dade yana son haduwa da ita. Saboda haduwarsu ta farko basu dade tare ba. Sai yace duk ya kosa su kara haduwa.

“A ranar Talata da dare muka hada mishi shirin ta waya. Mun je har Kano ranar Laraba da safe don ba ma son a samu matsala. Muna isa budurwar ta kira shi.

“In yanke muku zance, mun yaudareshi har wurin ‘yan sanda akan cewa zamu je amsar wani abu ne. Muna isa aka yi ram da shi. Ya yi matukar mamaki.

“Yan sanda sun bukaci bidiyon a wurinsa wanda ya musanta komai. Bayan bincike wayarsa tas aka ga bidiyon. Anan ne Musa ya hau kuka yana neman gafara. Amma ba mu saurare shi ba aka ci gaba da binciken wayarsa.

“Daga nan ne aka ga hotunan tsiraicin mata da yawa a wayarsa. Mun ga fuskoki mabambanta na ‘yan matan Facebook na arewa. Abin bai tsaya nan ba, har sai da muka gano shi ne mai amfani da sunan Zahra Mansur a Facebook. Yana ta damfarar mutane da sunanta.

“Abinda zai ba ka mamaki shi ne yadda ya ke ta da carar maza masu kudi suna tura masa kudi. Da za mu kira sunaye da an samu babbar matsala. Yanzu haka yana hannun ‘yan sanda kuma ba ma son kiran sunan wata wacce muka ga hotunanta. Amma na san yanzu suna ganin wannan wallafar.

“Su yi mana godiya akan cetonsu da muka yi. Budurwar da ta yi masa dabarar sunanta Basira Saminu, Najib sai ni kaina da muka yi aikin tare. Har yanzu ina. Cikin mamaki.”

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button