Labarai

Ina samun kai na cikin farin ciki a duk lokacin da nake tare da ke – Suleiman Isah ga matar shi Baturiya

Suleiman Isah ya bayyana yanda ya kasance cikin farin cikin kasancewa tare da matar shi Janine.

Matashin ya bayyana farin cikin sane a ranar bikin zagayowar ranar haihuwar matarsa.

Ya bayyana hakan ne a shafin sa na kafar sada zumunta wato Facebook

Matashin nan dan Najeriya mai shekaru 24 dan asalin jihar Kano, Suleiman Isah, ya wallafa rubutu a kafar sada zumunta na yanar gizo a kokarin da yake na taya matarsa Janine Sanchez Reimann murnar cika shekaru 48 a duniya.

Da yake bayyana hakan a shafin sa na Facebook, cikin nuna farin ciki Suleiman Isah ya daura kyawawan hotunansu shi da matar tasa wanda a hoton kadai za a fahimci yanda suke matukar kaunar junansu.

Inda yake bayyana ma duniya cewar fa matar sa daban take da sauran mata, tayi musu zarra, ya kara da cewa yana matukar sonta, kuma yana alfaharin kasancewan su tare.

“Ina taya matata murnar zagayowar ranar haihuwar ta, wacce soyayyarta ce take sani nishadi da farin ciki a ko yaushe. Sweetheart, ina alfaharin kasancewan mu tare. Ina Son Ki ya rubuta.

Suleiman Isah, wanda ya cika shekaru 24 a watan Oktobar shekarar da ta gabata, ya auri ba’amurkiyar matarsa mai shekaru 48 inda aka yi gagarumin biki wanda aka gudanar a garin Kano a ranar 13 ga Disambar shekarar 2020, sun hadu shida matar tasa ne a shafin sada zumunta na Instagram.

Daurin auren ya samu halartar ‘yan Najeriya da dama ciki har da tsohon sanatan jihar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani.

Suleiman Isah da matarshi Janine

A shekarar 2020 aka daura auren Suleiman Isah da Janine

Idan ba a manta ba a watan Janairun shekarar data gaba ta ne aka samu labarin ba’amurkiya Janine Sanchez Reimann ta biyo jirgi ta dira garin Kano dan kawai tazo ta hadu da masoyinta Suleiman Isah, zuwan na ta ya haddasa cece-kuce a kafafen sada zumunta inda mutane suke ganin cewa fa wannan mata tayi wa wannan yaron tsufa domin kuwa akwai tazarar shekaru 24 a tsakaninsu.

Hausawa sukace “SO”hana ganin laifi, shi dai wanan saurayi son da yake ma wannan mata ya hanashi ganin aibunta inda yafito ya bayyana wa duniya cewar fa shi yana son ta a haka, duk wanan cece-kuce da akeyi bai hana cigaba da shirye shiryen auren da Sulaiman yake shirin yi da baturiyar ba, wanda daurin auren ya samu halartar al’umma da dama.

Sai muce Allah ya kara dankon soyayya.

Daga LabarunHausa

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button