Labarai

Innalillahi Wainna ilaihirrajiun Wani Matashi a Katsina Ya Kashe Abokinsa da Maganin bera Don Kawai Ya Mallaki Motar shi.

Innalillahi Wainna ilaihirrajiun Wani Matashi a Katsina Ya Kashe Abokinsa da Maganin bera Don Kawai Ya Mallaki Motar shi.

A ranar Talatar nan ne rundunar ƴan sanda ta jihar Katsina ta gabatar da wani mutum mai suna Laminu Saminu ɗan asalin ƙaramar hukumar Mani da laifin kashe wani abokinsa jami’in rundunar tsaron farin kaya ta Sibil difens (NSCDC).

Kakakin rundunar SP Isah Gambo ne ya gabatar da mai laifin ga manema labarai a shelkwatar ƴan sandan da ke Katsina.

SP Gambo ya ce a ranar 26 ga watan Satumban da ya gabata, Laminu Saminu ya kashe abokin na sa mai suna Sunusi Bawa bayan da ya ziyarci gidansa da nufin duba shi ya ga ko lafiya tunda ya kira wayarsa har sau 11 amma bai ɗaga ba.

Marigayi Sunusi Bawa yana da muƙamin mataimakin Sifuritanda na rundunar Sibil difens da ke Katsina kuma ya je ne gidan abokin nasa da niyar ya ziyarce shi inda anan kuma abokin nasa ya kashe shi ya binne gawarsa a rijiya.

Muna masa Addu’a Allah Yaji kanshi da rahama shi kuma Allah yasa ayi masa Hukunci dai dai da abinda ya aikata. Mun gode da Ziyartar wannan Shafi namu wanda yake kawo maku labarai da dumi duminsu.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button