Jarumi Jim iyke Ya Musanta Labarin Ke Yawo Akan Ya Musulunta
“Ina mika gaisuwa ta ga daukacin al’umma na ga ya zama dole na fito na yi magana akan wani jita-jita da ke ta yawo a kwana kwanan nan. Ni ba mutun ba ne mai son kula irin waɗannan jita-jitan ba ne saboda ba damuwata ba ce. Amma kuma komai yana da iyaka” inji shi.
“Wata daya da ya wuce a kasar Ghana na yi wani fim game da wani mai kishin addini.Sai aka sami Wani makaryaci ya ɗauki hotuna ya yada a yanar gizo cewar na musulunta. Duk da yake ba ni da wata matsala game da kowane addini, amma ni banida niyyan chanza akida bazan taba chanzawa ba.”
“Ban san meye dalilin son yada wannan jita-jitan ba amma akwai wasu layukan da bai kamata a dinga ketarewa ba. Don haka duk ma wanda ya yada wannan karyan to yadawo ya sake wallafa cewar ba gaskia bane,ba nidai lokacin irin wadannan abubuwa. “
[ad_2]