JIDDAHTUL KHAIR 28

tace “Good!!!Abbanka na nemanka, kuma ka taho tare da Jiddar, ba jiran ka xai yi ba, karfe goma xai fita yace” Daga haka ta katse wayar, sosai ya ji gabansa ya fadi, Abba calling him for what? Kallon agogo ya sake yi sannan ya ajiye wayar ya lumshe idonsa yana jin xuciyarsa na bugawa, bayan minti goma ya mike ya shiga bathroom. Tara da minti goma ya fito daga bangarensa cikin kananun kaya, ya tsaya bakin kofar jiddah for some seconds kafin ya bude kofar a hankali, gyaran daki ya sameta tana yi, ta sunkuyar da kai, ganin ta shirya yace “Dauko hijab din ki” Daga haka ya juya ya fita, karasa gyaran dakin tayi sannan ta sa hijab din ta fito. Throughout the ride hankalinsa baya jikinsa, sai da yaga sun kusa gidan ya kalleta rasa abinda xae ce mata yyi har suka shiga gidan, parlon Abba ya nufa direct tana biye da shi a baya, yana sallama aka yi masa izinin shigowa, shi ya fara shiga sannan ta shiga, Aunty na xaune parlon tare da Ummi da Umma, kamar dai xuwansu ake jira, ya ji gabansa ya fadi sosai, xaunawa yyi kasa, jiddah ta xauna side dinsa a hankali, ita ta fara gaishesu cikin sanyin murya sannan shi ma ya gaishesu, Abba gaisuwanta kawai ya amsa, yana kallon Abuturrab babu yabo babu fallasa yace “For how long have u divorced her Aliyu??”
[/indeed-social-locker]