JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDAHTUL KHAIR 29

[indeed-social-locker sm_list=’fb’ sm_template=’ism_template_6′ sm_list_align=’horizontal’ sm_display_counts=’true’ sm_display_full_name=’true’ unlock_type=1 locker_template=2 sm_d_text=’

This content is locked

Share This Page To Unlock The Content!

‘ enable_timeout_lk=1 sm_timeout_locker=40 delay_lk=1 sm_delay_lk=4 reset_locker=1 locker_reset_after=1 locker_reset_type=’days’ ism_overlock=’default’ ]

komai ba, lkci daya taga yana bude takardan da gudu ta nufi kofa ta fice daga dakin ya bi ta da kallo ganin babu komai a jikin takardan, mamaki ne ya cikasa ya sake juya bayan takardan that is plain, Bude baki yayi with so much surprise, bai san lkcn da yayi murmushi ba ya rungume hannunsa, so tana da irin wannan wayon ashe, bai bi ta ba sabida yasan xa ma ta dawo ne, ya tafi gefen gado ya xauna, Jiddah ta jingina da kofar parlonsa ta xame kasa tana yarfe hannu, gaba daya a tsorace take, sai jiran fitowarsa take anytime amma har sannan bai fito ba, bin babban parlon ta dinga yi da kallo kamar xata hango makullin kofar, har bayan minti talatin bata gansa ya fito ba, gajiya tayi da xama a bakin kofar, ta mike a hankali tana leka kofar dakin nasa, can dai ta karasa bakin kofar ta leka ciki don kofar ba a kulle yake gaba daya ba, kwance ta gansa waya kare kunnensa, ta juya da sauri ta koma inda take xaune kamar xata yi kuka, har sha biyu saura Jiddah na xaune gefen kofar, bacci ne ya fara damunta, mikewa tayi ta tafi kan kujera ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa, can cikin dare taji ana lalubata, ta mike a tsorace ganin duhu a parlon tace “Wayyo Allah na” Muryarsa taji yace “Ina takardan yake” Jikinta ma rawa tace “Yana cikin hulana” Xata cire hulan ya rigata cirewa ya ga takardan a kanta ya dauka sannan ya saketa ya koma dakinsa ya kulle kofar, har lkcn gabanta faduwa yake ta mike xaune tana bin parlon da kallo don ko alamar haske babu, a hankali ta mike tana neman hanya har ta isa kofa ta murda taji a kulle har sannan, jingina tayi da kofar kamar xata yi kuka, can ta juya ta koma saman kujeran ta kwanta, nan da nan bacci ya sake dauketa, kiran sallan asuba ne ya farkar da Jiddah, ta tattaba lallausan abinda taji a jikinta, kofar daki aka bude da sauri ta rufe idonta don hasken dakin ya hasko parlon, tana ji ya bude kofar parlon ya fita, lkci daya kamshin turarensa ya gauraye parlon, sai bayan kusan minti biyar ta cire duvet din jikinta ta mike a hankali jin xa a tada sallah, ajiye duvet din tayi kan kujeran ta nufi kofa ta bude ta fita xuwa dakinta. Karfe takwas saura Jiddah ta farka daga baccin da ta koma bayan tayi sallan asuba, mikewa tayi ta shiga bandaki sai da tayi wanka ta wanke baki sannan ta wanke bandakin ta fito, tana gama shiryawa ta hau gyaran dakin, bude kofa aka yi ta juya da sauri, calmly yace “Ki sameni kasa” daga haka ya rufe kofar, ta gama abinda take sannan ta sauka kasa, yana xaune parlor yana kallo, agogon wrist dinsa ya kalla yace “Na baki minti talatin ki je ki dafa abinda xa ki ci….”

tsayawa tayi tana kallonsa, ganin bata motsa ba ya daga kai ya kalleta, da sauri ta juya ta wuce kitchen din ya bi ta da kallo, indomie ta dafa ta ci a kitchen din ta wanke plate sannan ta fito, ya kalleta ya nuna mata karamin travelling bag dinsa da ya sauko da shi parlor yace “Ki je ki hada kayanki kala biyu da duk abinda xa ki bukata, kar ki bata min lkci, ki saka Jilbab idan xa ki sakko” A hankali tace “Ina za mu je kuma, amma ba jirgi xa mu hau ba ko??” ganin irin kallon da yake mata ta dau travelling bag din ta juya ta wuce sama, kayan nata ta hada sannan ta sauko kasa a sanyaye, Hijab ne har kasa jikinta, ya mike ya nufi kofa ta bi bayansa rike da jakar. Parking Abuturrab yayi kofar gidansu Ahmad, Jiddah ta juya ta kallesa ganin inda suka xo, wani farin ciki taji a ranta, bude motar yayi ya sauka, ita ma ta sauka ta bude back seat ta dau jakar kayanta, ai da ta san nan xa su xo da ta debi kaya da yawa, ganin ya nufi gate din gidan ta bi bayansa da sauri, gaba daya farin cikinta ya kasa boyuwa, sai kallon kofar Maman Abdallah take har suka shiga main parlor din gidan, Umma ta fito daga dakinta ganinsu tace “Aa daga ina haka kuma” Yayi kasa da kai yace “Daga gida Umma” nan ya gaisheta, ta amsa tana kallon Jiddah tace “Sannu da xuwa Jiddah…” Gaisheta Jiddah ma tayi tana mayar mata da murmushin, Umma ta amsa tana tambayarta ya gida, Jiddah tace “Lafiya lau” Umma tace “To kun ma karya kuwa wannan sammako haka?” Abuturrab yace “Eh mun karya, i brought her ahead of the wedding….” Umma da taji dadi har ranta don wnn shine right time da xata fahimci gaskiyan abinda Aunty ke fada tace “To maa sha Allah, that’s very good” Yace “Kudin ankon kuma wa xa a tura ma?” Umma tace “Anko kuma?” Yace “Ummi ce tayi maganan ankon ran Friday” Umma tace “Kyale Ummi, ae ta riga ta mata, har dinki an bada” Yace “Toh Allah ya saka” mikewa yayi yace “Sai anjima Umma, xan wuce kano da yamma in sha Allah, ranan alhamis xan dawo” Umma tace “Toh Allah ya tsare, shi ma Ahmad din ranan laraba xai shigo…” Abuturrab yace “Ehh mun yi waya da safe, haka yace min” Ya d’an kalli Jiddah sannan ya nufi kofa yana ma Umma sallama, Umma tace

“Toh baxa kiyi masa rakiya ba Jiddah?” D’an murmushi kawai tayi ta sunkuyar da kanta, Umma tace “Tashi ki je” a hankali ta mike ta nufi kofa ta fita, cike da kasaita yake tafiyar, ta bi sa da kallo, bin bayansa tayi har suka fita gidan, ya bude driver seat xai shiga sai kuma ya tsaya yana kallonta don makalewa tayi jikin gate, suna hada ido ta sauke nata idon, yace “Kina son wani abun ne” Ta d’an turo baki tace “Umma ce tace in raka ka” ya shafa kansa yace “Idan Umma tace ki shirya ku je can gidan kice mata baki jin dadi baxa ki iya xuwa ba” Tana kallonsa tace “Toh ka tayani gaya mata mana” ya daga kafada yace “Toh ki tafi ni ba ruwana” Daga haka ya bude motarsa ya shiga ya tada yayi reverse, a hankali ta juya ta koma cikin gidan, daren ranan Maman Abdallah na parlon Umma tare da mai aikin gidan suna ta hira, duk sbda Jiddah ta shigo kuma, sai kusan karfe goma maman Abdallah ta bar parlon, duk yan matan gidan na can gidansu Abuturrab, mikewa Jiddah tayi a hankali tayi ma mai aikin sai da safe ta wuce dakin da Umma ta sa ta ajiye jakarta, tuni Umma ta tafi ta kwanta tana tunanin where to start from coz ko kadan bata yarda da Jiddah da Abuturrab ba, Jiddah tayi wanka ta sauya kayan jikinta xuwa na bacci sannan ta kwanta. Washegari monday Jiddah ta taya Huraira mai aiki girkin breakfast, sosai ta sake a gidan ba kamar gidan su Abuturrab ba duk da Seeyama bata nan, Karfe sha daya na safe ta raka Umma kasuwa da driver, basu dawo gida ba sai kusan azahar, Jiddah na sallah ta kwanta don sun ci abinci a restaurant, da yammacin ranan Seeyama da Aisha da Safiyya suka xo gidan amsar ma Aunty sako wajen Umma, Seeyama tayi murnan ganin Jiddah a gidan, Umma tace “Sai ki shirya ki bi su Jiddah, idan na je anjima da daddare sai mu dawo tare” Shiru Jiddah tayi ta kasa ce mata komai, Seeyama tace “Ki tashi sister Jiddah Aunty na jiranmu” Mikewa Jiddah tayi a ssnyaye ta saka Hijab dinta, Driver Umma ta sa ya mayar da su can gidan saboda Jiddah, tun da suka sauka motar gaban jiddah ke faduwa ta dai bi bayan Seeyama rike da handbag dinta har suka shiga parlor, dai daikun baki ne da suka xo biki a parlon, Jiddah ta sunkuyar da kanta ta nufi bangaren Ummi, tana shiga parlon taga mata biyu a xaune, Xaunawa kasa tayi ta gaishesu, duk suka amsa, ba a dau lkci ba Ummi ta fito daga daki, ganinta tace “Daga ina haka, ina Aliyun?”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button