JIDDAHTUL KHAIR 29

Jiddah ta gaisheta sannan tace “Tare muka xo da su Seeyama” Ummi tace “Ohk toh ki shiga can ciki” mikewa Jiddah tayi ta wuce bedroom din Ummi, Hajiya Murja kawar Ummi tace “Kaddai ita ce matar Aliyun?” Ba tare da Ummi ta kalleta ba tace “Ehh ita ce” Hajiya Salaha tace “Allah sarki, ashe yarinya ce ma, toh Allah ya basu xaman lafiya, ga ta dai kamar ba sa wa ba hanawa” Ummi ta d’an yi murmushi kawai, Seeyama ce ta shigo parlon tace “Ummi Aunty Jiddah ta shigo nan” Ummi tace “Tana ciki” Seeyama ta shiga sai ga ta sun fito tare da Jiddah suka fita parlon, sosai gabanta ke faduwa tana tsoron kar ta hadu da Aunty har suka shiga dakinsu Ramlah, Ramlah na ganin Jiddah ta washe baki tace “Aunty Jiddah sannu da xuwa” Jiddah ta xauna tana murmushi tace “Ya gida” Ramlah tace “Lafiya lau, yaya fa?” Jiddah tace “Ya tafi kano” Seeyama tace “Shi sa ya kai ki gidan Umma?” Kai kawai Jiddah ta gyada mata. Suna nan xaune har aka kira magrib, bude kofar dakin aka yi Aunty ta leko tana cewa “Wai baxa ku fito kuje ku yi wanke wanken can ba dake bakin pampo gashi har anyi magariba, ko waye xai maku? Ai sai ku hakura xuwa gobe ku sakankance tunda nasan yan kauye masu wanke wanken xa su iso” Jiddah dake kan darduma ta sunkuyar da kai gabanta na faduwa, tsit Aunty tayi ganin Jiddah kan darduma, can tace “Ko da yake tun safe ai ku ke ta aiki, ke ya kike da suna??” Jiddah ta kalleta, Aunty tace “Ehh da ke nake kike kallona haka, tashi ki fita ga wanke wanke can bakin pampo kije ki wanke” Mikewa tayi da sauri, Seeyama ta mike tace “Ta barshi kawai xa mu yi aunty” Aunty ta jefa mata wani kallo tace “Toh ita xa ta yi, ku kuma xan aikeku yanxu tare da driver xa ku je min siyayya a supermarket” Jiddah ta nufi kofa ta bi gefen Aunty da ta bi ta da wani kallon tsana ta fita, kitchen Jiddah ta nufa ganin kofar kitchen din a bude ta fita taga uban kayan wanke wanke a bakin pampo ga omo da soso, ruwa ta tara ta fara wanke wanken, ba a dau lkci ba sai ga Aunty ta
shigo kitchen din ta dinga fitar da plates wankanku tana ajiye su kan marasu wanki, ita dai Jiddah bata ce komai ba, har tukwanen sai da ta fitar da su sannan ta dau soson waya ta jefa mata tace ki tabbatar kin bi bayan tukwanen nan kin wanke su fess, xuwa gobe kuma xan san yanda xanyi da ke, daga haka ta juya ta koma ciki, Jiddah dai ta ci gaba da wanke wanken da take a sanyaye. Ba ita ta bar bakin pampon nan ba sai kusan karfe tara da rabi, duk ta gaji ga uban yunwan da take ji, bbu kowa parlon sai yara dake ta wasa, iyayensu kuma na can sama, Jiddah ta rakube jikin kujera tana jin kanta na mata ciwo, har ta mance rabon da tayi irin wannan aikin, tun bayan rabuwanta da Hansai, Aunty ce ta shigo parlon da sauri tana sanye da Hijab, har ta nufi kitchen sai kuma taga Jiddar a rakube a parlor, tana kallonta tace “Yauwa mu je ki rakani xan amso sako yanxu”
[/indeed-social-locker]