JIDDAHTUL KHAIR 30

Mikewa Jiddah tayi tsaye tana kallonta, Aunty da har ta nufi kofa ta juyo ganin Jiddah bata biyota ba ta hade rai tace “Ba magana nake maki ba” Jiddah tace “Ban saka hijabi ba” Aunty tace “Nan nan ne ba nisa muje baxa ki rasa mayafi a tsakar gida ba” Jiddah bata ce komai ba ta nufeta, Umma ce ta shigo parlon da sallama, Aunty ta koma gefe tana yake tace “Sannu da xuwa Hajiya Ramlah” suka gaisa Umma tace “fita xa ki yi halan” Aunty tace “Ehh wllh sako xan amso nan bakin titi, da har nace mu je da Jiddan tace min Hijabinta na sama” Umma ta kalli Jiddah tace “Toh ki tafi saman ki dauko hijabin naki” Aunty tace “Aa bari kawai inje ae nan bakin titi ne” bata jira cewar Umma ba ta fice daga parlon tana jin wani mugun takaici, Umma ta kalli Jiddah tace “Kin ci abinci kuwa?” Jiddah ta girgixa masa kai, Umma tace “Toh saboda me, ke ba sai ki je ki diba ba, Ummi na sama ne?” Jiddah ta gyada mata kai, Umma tace “Mu je” Jiddah ta bi bayanta suka wuce sama, Bangaren Ummi suka shiga, bayan Umma ta gaisa da yayarta tace “Yaya wai bata ci abinci ba” Ummi ta kalli Jiddah tace “Ae nayi tunanin tana tare da su Ramlah ne, kuma an kai masu abinci tun daxu, taje can dakinsu ta diba” Umma ta kalli Jiddah tace “Ki je ki deba abincin a can” Juyawa Jiddah tayi ta fita, Umma na kallon yayarta tace “Naga kamar baki saki jiki da ita har yanxu ba yaya” Ummi tace “Aa ko daya, baki ganin ita ma ba maganar take ba” Umma tayi murmushi tace “Ae kam ni muna hira da ita” Ummi tace “Did u know what is baffling me Ramlah?” Umma ta girgixa kai tana kallonta, Ummi tace “Yanda Aliyu ya mayar da mu shashashai ya maida mu wasu ‘yan yara, kinsan da gangan yaje yyi ma kansa aure da yarinyar nan?” Ummi tace “Me yasa kika ce haka yaya” Ummi tayi wani murmushi tace “Ai ni na haifesa ba shi ya haifeni ba, bai kuma isa yyi deceiving dina ba, he intentionally did what he did, abubuwan da nagani game da shi da yarinyar bai yi kama da abun da mutum yyi ba da son ransa ba, kinsan satinsa nawa rabonsa da gidan nan yanxu?” Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace “Nima ae ya daina xuwa min yaya…” Ummi tace “Toh yayi kyau… Xai gane bashi da wayo” Umma tace “Amma duk da haka akwai ayar tambaya fa a kan xaman da suke, don duk inda kika ji kishin kishin din magana da akwai kamshin gaskiya, ina jiran Ahmad ne yanxu inji matsayin auren nasu” Ummi tace “Ni ma dai nayi shiru ne kawai, amma ban aminta da xaman nan ba” Umma tace “Toh kin ga, don dama da bakinsa yyi ta cewa xae rabu da ita, na dinga hanasa tare da Abbansa to wa ya sani ko watsar da xancenmu yyi” Ummi tace “Ni kuma haka kawai naji ina son rabuwan nasu Ramlah” Umma dai tayi shiru bata ce komai ba, can ta sauke ajiyar xuciya tace “Allah dai yyi mana me kyau, kuma bana tunanin ya sa ta a karatu har yanxu, and she doesn’t look happy always….” Ummi tace “Sannan ina ma son xanyi magana dake tun kwanaki, kinga lamarin rayuwar Aliyu? dama ina son in cire idanuwana da komai na a kai, sai yaje ya kara rike warce yake ganin ta fini daraja da hannu bibbiyu, ita yake ga xai iya komai na sirrinsa, ita yake ga xai fi ji da yarda da maganarta, to suje su karata, ni gaisuwan da yake min duk sanda yaga dama ma ce masa xanyi na yafe masa ya daina” Umma tace “Wannan ba magana bane yaya, tun farko ke kika xuba ido aka janye maki shi, Ahmad ya sha kawo min wannan same complain din, idan baki manta ba akwai wani lkci da na maki magana a kan hakan kika ce min ai ba komai duk daya ne, wnn mata ni ban ta6a ganin makira irinta ba…” Ummi ta girgixa kai tace “Aa ba ruwanta, ai shi ba yaro bane ya kuma mallaki hankalin kansa, he knows what is right from wrong, kawai dai hakan yake ga yafi masa alkhairi, sai yaje ya karata, amma ina dab da yi masa wankin babban bargo a gidan nan” Umma ta sauke ajiyar xuciya tace “Ki dai yi hakuri yaya, Allah xai ganar da shi, wankin babban bargo kuma sai dai ki hada har Kishiyarki don munafuka ce”
Bayan kusan minti talatin Umma ta gama abinda ya kawota, sallama tayi da yayarta har ta nufi kofa tace “Toh in tafi da Jiddar ne don can ya kai ta” Ummi tace “Aa wannan kuma ban sani ba” Umma tace “Naji xa su fita saloon gobe, kawai su tafi tare ita ma tayi gyaran gashin idan ya so ko driver sae ya maido min ita goben” daga haka tayi ma yayarta sallama ta fita dakin. Kwana dayan da Jiddah tayi gidansu Abuturrab ta fadi ma yan garinsu gashi gidan ya cika da mutane yan biki, Aunty tayi mugun saka ta gaba tun da garin Allah ya waye, ko wani aiki da aike ita ake sa wa, da ta xauna xata tasota gashi abincin kirki ma bata samu ta ci ba, da rana yan matan amarya duk suka yi shirin tafiya saloon, dama kafin Ummi ta lura da Jiddah balle har tace mata ta bi su, aunty ta hada kayan wanke wanke a bakin pampo ta turata taje tayi, yawanci duk masu girki ranan sun xata ma mai aikin gidan ce Jiddah, ko mai aikin gidan bata yi aikin da Jiddah tayi ba tunda gari ya waye, cikin ruwan sanyi Aunty ke gallaza mata, duk tunanin Ummi kuma har da Jiddah aka tafi saloon don tun bayan da suka gaisa da safe bata ganta ba, a gajiye Jiddah ta fito daga kitchen wajen karfe hudu ga wani yunwa da take ji, wata tsohuwa ce ta mika mata purse tace “Yan mata ki kai min daki wajen Hajiya Hauwa ta adana min, kada a yasheni a gidan biki, dubu daya da dari biyar ce a ciki” Jiddah ta amsa tace “Toh” lkci daya Jiddah ta gane warce take nufi wato Ummi, bangaren Ummi ta nufa ta bude kofar parlon da sallama, Ummi da frnds dinta Uku ne a parlon sai wasu yan uwa guda uku, Jiddah ta gaishesu gaba daya, Ummi dai sai kallonta take da mamaki, Jiddah ta sunkuyar da kanta ta duka gefenta tana mika mata jakar tace “Ummi wai ajiya aka ce a kawo maki” Ummi ta amshi purse din tace “In ji waye?” Jiddah tace “Ai ban santa ba” Ummi tace “Dama baki je saloon din ba ke” Jiddah ta gyada mata kai kawai, Ummi tayi shiru tana son nuna ma yan uwan mai gidanta da kawayenta cewar ita ce matar Aliyu amma ta kasa, can dai tana kallon jiddah tace “Toh gobe sai a kai ki ke” a hankali Jiddah tace “Toh” daga haka ta mike, dai dai nan Abuturrab ya fito daga bedroom din Ummi, sosai gaban Jiddah ya fadi bayan sun hada ido, amma kuma sai taji dadin ganinsa ba kadan ba, duk yan parlon suka juya suna kallonsa, Ummi ma kallonsa tayi don tun daxu take fama da shi ya fito ya gaisa da yan uwan Abbansa su uku sun iso daga Damaturu amma ya ki fitowa wai ya gaji, gwara frnds dinta a parlon ya samesu da ya shigo, Hajiya Zuwaira ta rike ha6a tace “Dama Aliyu na ciki?” Ummi ta kirkiri murmushi tace “Eh bacci yake, saukansa daga kano kenan ko awa biyu ba ayi ba” Tuni Jiddah ta fita daga parlon, gaishesu Abuturrab yayi yana yake ya nufi kofa ya fita parlon Ummi ta bi sa da kallon mamaki har ya kulle kofar, har Jiddah tayi nisa yace “Keee” tsayawa tayi ta juya tana kallonsa, ya karasa inda take yana kallonta daga sama har kasa, gaba daya ta wani susuce, yace “Yaushe kika xo gidan nan” Ta sunkuyar da kanta tace “Umma ce tace mu taho…” ya kara kallonta daga sama har kasa sannan ya sa hannu ya ciro makulli a aljihunsa yace “Dakin dake ta can bangaren inda babu mutane, ki je can ki jirani” Tana kallon makullin tace “Bude kofar xan yi?” Ya hade rai yace “Aa kullewa xa kiyi, bakya jin hausa ne?” Juyawa tayi ta bar wajen don ta