JIDDAHTUL KHAIR 30

gane dakin da yake nufi babu wanda ke xuwa ta wajen, bata yarda ta kalli kowa ba har ta nufi bangaren ta sa makullin ta bude dakin sannan ta shiga, babban daki ne sosai babu abinda babu a ciki, sai dai abubuwan ciki ba masu hayaniya bane, sannan ba a wani cika kaya a dakin ba, xaunawa tayi kasa ta jinginar da kanta kan babban katifar dakin don gaba daya ta gaji, Bayan kusan minti sha biyar taji an bude kofar dakin ta daga kai da sauri, Shine ya shigo dakin, ya kulle kofa yana kallonta yace “Baki cin abinci ne?” Ta girgixa kai tace “Aiki nake yi shi yasa ban ci ba” Yace “Wani aiki?” Tace “Nayi wanke wanke da safe na share duk tsakar gidan, sannan na taya masu girki wanke naman kaza, wani wanke wanken ya taru na kara wankewa, kuma naje siyo ledan kwasan tuwo sau uku wajen da nisa sosai almajiri ne ya rakani, da na dawo kuma wani wanke wanken ya taru na sake yi, sannan na share tsakar gidan da aka bata….” Katseta yayi yace “Duk wa yake sa ki?” Ta sunkuyar da kai tace “Aunty” Bai ce komai ba, bayan kusan minti biyar yace “Tashi ki shiga bandaki ki hada ruwa kiyi wanka” Mikewa tayi ta nufi bandakin she looks so tired and worn out, ya juya ya fita ya sa ma dakin makulli ya cire ya tafi da shi, a parlor ya tadda Aunty na welcoming din bak’in da suka shigo da mugun fara’arta, ido hudu yayi da mahaifiyar Aneesah, Ya sauke kansa kasa sannan ya karasa cikin parlon ya gaisheta da ladabi bata ko kalli inda yake ba balle tayi kamar ta ji, Aneesah ce ta shigo parlon da jakar kayanta, Aunty ta rungumeta tace “Sannunku da xuwa manyan baki, ya hanya?” Aneesah na murmushi tace “Alhmdlh Aunty don ma dai jirgi muka biyo ai da sauki wahalan” Kofa Abuturrab ya nufa don ko hada ido bai son yi da Aunty, Babu yabo bbu fallasa yaji tace “Aliyu get them something meaningful to eat, kasan sha’anin abincin biki, ba lallai yayi suiting taste bud dinsu ba” Toh kawai Abuturrab yace ya fice daga parlon. Parking Abuturrab yayi bakin gate dai dai lkcn da driver ya sauke su Seeyama bakin gate din, duk suka nufi motarsa, bai amsa gaisuwar da suke masa ba, ya dau leda biyu na abinci yace “Ku kai ma Aunty” Seeyama ta amsa sannan suka wuce ciki, bayan few minutes ya bude motar ya sauka ya shiga cikin gidan rike da leda daya, direct part dinsa ya nufa, ya ciro makulli ya bude kofar ya shiga sannan ya kulle, Jiddah na kwance kan carpet idonta kulle, karasawa yayi yaga bacci take, ya buga katifar kusa da ita, firgit ta mike xaune, ya ajiye ledan hannunsa ya hade rai yace “Baki ce ma Ummi baki ci abinci bane duk yau?” Ta girgixa kai tace “Ban ganta ba tun da safe sai daxu da naje kai mata sako” Yace “Toh wa ya kawo ki gidan nan?” Tace “Nace maka Umma tace in taho tare da su seeyama” ajiye ledan hannunsa yyi ya mike ya koma can karshen katifar ya xauna ya fiddo wayarsa dake vibrate a tunaninsa Ahmad ne don yana restaurant ma ya kirasa, amma sai ya ga akasin haka don Aneesah ce ke kiransa, silencing wayar yyi, Jiddah ta bude abincin da ya ajiye mata ta fara ci.
Mikewa yayi ya fita dakin ya kulle, kiran Aunty ne ya shigo wayarsa ya daga ya kai kunne bai ce komai ba yana tafiya, cike da fada tace “Amma walakancin ka da yawa yake, kasan bakin nan takanas daga Abuja suka xo, ba sai ka tafi ka samesu a masaukinsu ka xauna a nutse ka gaida su ba, amma ka wani gaishesu a tsattsaye ka fita kamar mara gaskiya, ko baka san mahaifiyar Aneesar bace?” A hnkli yace “Yanxu nake tahowa” Tace “Toh suna can uwar dak’ana” Yace “Alright” daga haka ya katse wayar ya nufi bangaren Aunty a ransa yana tunanin har ta huce kenan, or did she have anything in mind to punish him with, bude kofar parlon yayi, ya gaida frnds dinta dake xaune parlon, sannan ya nufi bedroom dinta, sai bayan da aka amsa sallamarsa sannan ya shiga, Mahaifiyar Aneesah na xaune tare da kanwarta sai Aneesah a dakin ga abinci iri iri a gabansu bayan wanda ya siyo masu, xaunawa yayi kasan carpet ya gaishesu da ladabi kansa a kasa, kanwar mahaifiyar Aneesar ce kawai ta amsa masa a dakile, uwarta kuwa sai cin abincinta take, Aneesah dai na xaune kan kujera sai kallonsa take ko kiftawa babu, kananun kaya ne jikinsa da suka yi matukar amsarsa, ga kamshin turarensa da ya cika ko ina na dakin, Kanwar mahaifiyar Aneesah Hajiya Maryam tace “Allah ya sanya alkhairi a bikin” Ya amsa da “Ameen” Ya d’an saci kallon mum din Aneesah dake fama da kaza, Mikewa Aneesah tayi ta fita daga dakin, Bayan few seconds ya mike yayi masu sai anjima ya fita shi ma, Hajiya Maryam ta tabe baki tace “Kaga mutum kamar shi yayi kansa, sannan ga nera, shi yasa Aneesah duk take daga ma mutane hankali, to in sha Allah komai ya kusa karshe ynxu ai” tsaye Abuturrab yaga Aneesah corridor tana jiransa, ya shafa kansa yace “U didn’t tell me tare da su Mumy xa ku xo” Tace “Ehh ai baka tsaya ka gama saurarata ba daxu kace ana kiranka ka katse wayar” Yace “Ohk, kinci abincin?” Tace “Bayan leda biyu ka siyo me xan ci a ciki?” yace “Ehh ai banga Hajiya ba i only saw u and mum” Ta tabe baki tana gyara siririn gyalenta, ya rungume hannunsa yace “Toh
yanxu ya xa ayi?” Tace “Xuwa xa mu yi ka siya min abincin” Ya d’an yi shiru sai kuma yace “Toh ki jirani wajen motar xan dauko makulli a dakina” Tace “Ohkk” daga haka ta fara tafiya, ya bi ta da kallo sannan ya sauka xuwa dakinsa, makulli ya sa ya bude kofar xai shiga yaji muryar Aunty tana kiransa alamar tana biye da shi a baya, da farko niyyar kulle dakin yyi da makullin amma sanin xata yi suspecting abu sai ya fasa ya shiga dakin kawai bayan ya amsa kiran nata, Jiddah na tsaye bakin window ya nuna mata alamar ta shige bandaki, ai da gudu ta shige ciki ita ma jin muryarta, ta kulle har da sa makulli hakan ya kusa basa dariya, dai dai nan Aunty ta shigo dakin, ya xauna gefen gado yana shafa kansa yace “Ya gajiyan aiki Aunty?” Maimakon ta amsa sai ta sa makulli dakin ta shigo, shi dai kallonta kawai yake, ta kalli ledan abincin tace “Wannan fa?” Yace “Ni na siyo na ci” Kujera ta ja ta xauna tace “Abuturrab!!” Ya daga manyan idanuwansa ya kalleta, sake kiransa tayi murya can kasa yace “Na’am….” Tace “Dama Abuturrab ra’ayinka ne xuwa hayi kayi aure ban sani ba? Dama haka ka mayar dani gantalalliya ban sani ba” Ya girgixa kai yace “Wllh ba ra’ayina bane Aunty” tace “To son yarinyar ka fara all of a sudden? Da ka toxarta ni gaban ubanka?” Ya girgixa kai yace “Ko daya wllh Aunty” tace “Toh kawai xubar min da mutunci da walakanta ni gaban iyayenka ka so yi??” ya sauke wani ajiyar xuciya yace “Ba haka bane Aunty, kiyi hakuri” tace “Inyi hakuri?? Dama shirga ni kayi baka saketa ba Aliyu??” Da kyar yace “I’m finding it hard to confide in u anymore aunty…” Tace “Why??” Yace “U did what i never expected, kema kin san na kowa me sauki ne kan na Abba, how will u expect him to take it cewar na saketa da gaske? Wllh he can even disown me, kin fa san waye Abba, kin fi kowa saninsa, amma kika yi exposing dina wajensa” Da karfi tace “Karya kake, wllh baka saketa ba ni xaka mayarda sha sha sha yanxu? Are u stupid?” Yayi kasa da murya yace “Xa kiyi kaffara Aunty, nace maki ba aure tsakaninmu da yarinyar nan amma kuma bai kai har ki je ki gaya ma Abba ba, i trust u shi yasa na sanar maki” Shiru tayi tana kallonsa tana huci tace “Toh dadin xama kake ji da ita ne da kaki rabuwa da ita har yanxu???” Yace “Ko daya, idan na rabu da ita bata da wajen xuwa Aunty, Aunty da xa ki kwantar da hankalinki ki xuba min ido xaki ga me xai faru in sha Allah, i have plans wallahi, ba haka nan kawai na ajiyeta gidana ba, the house isn’t meant for