JIDDAHTUL KHAIR 32
Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems
Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada
Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240
Jiddah ta goge idonta still ta ki cewa komai, Umma tace “Baxa ki min magana ba Jiddah?” A hankali Jiddah tace “Umma yace min babu aure tsakanina da shi” Umma tace “Kamar ya babu aure a tsakanin ku?” Jiddah ta gyada kai tace “Eh haka yace, wai shi ba mijina bane” Umma tace “A ina yace hakan?” Jiddah tace “A can gidansa, ya rubuta ne a takarda ya bani” Umma ta dinga kallonta kafin tace “Ina takardan?” Cikin sanyin murya tace “Ya ki bani” Umma tace “Amma ya nuna maki?” Jiddah tace “Ehh” Umma tace “Cewa yayi ya sakeki a takardan?” Nan ma tace “Ehh haka yace, shi ba
mijina bane” Umma ta gyada kai bata kuma ce mata komai ba, bayan kusan minti goma ta mike ta fita dakin rike da wayarta, wani dakin daban ta shiga tayi dialing number wata aminiyarta tana dagawa tace “Hajiya karfe nawa xa ki taho?” Hajiya Rukayya tace “Ina hanya yanxu haka” Umma tace “Babu kowa gidanki?” Hajiya Rukayya tace “Toh na bar su dai suna ta shirin tafiya dinner da wani abu ne?” Umma tace “Toh shhkn tunda ba kowa, dama wata yar uwarmu ce aka kawo biki to bata son hayaniya, kinga nan din ma akwai taro shine da nake son ta xauna gidanki har bayan biki” Hajiya Rukayya tace “Ohh Allah sarki, to amma Badiya mai aikina na nan ai, ba
sai su xauna tare ba” Umma tace “Yauwa toh, xan sa driver ya kai ta can din kawai, sai ki kira ki sanar mata bakuwa na xuwa” Hajiya Rukayya tace “Toh ba damuwa” Umma ta koma dakin da Jiddah ke ciki tace “Kaya kala nawa kika taho da?” jiddah tace “Na yau ne da gobe kawai” Umma tace “Ohk, xaku fita da driver xai kai ki gidan kawata yanxu, tunda naga ke ba son taro kike ba ai” Jiddah ta d’an yi shiru, sai kuma a hankali tace “Umma ai
yace xai dawo anjima ya daukeni” Umma tace “Ehh kafin ya dawo din, sai yaje can gidan ka ya daukeki, ki tafi da jakar kayanki kawai” Jiddah tace “Toh” Bayan mota Umma ta sa ta shiga ta ajiye mata jakarta a gefenta, sannan driver ya bar gidan bayan ta sanar masa inda xai kai ta, tafiyar kusan minti ashirin da wani abu suka yi suka isa gidan Hajiya Rukayya, Drivern yayi ma mai gadi maganan cewar yayi leading dinta har entrance din gidan, tana shiga cikin compound din mai gadin ya nuna mata direction da xata bi, ta makale jikin kofar ta kwankwasa a hankali, ta fi minti biyar tsaye sannan aka bude kofa, wata mata ce ta bude kofar ganinta tace “Ke ce bakuwar da Hajiya ta sanar kina xuwa?” Jiddah ta gyada mata kai kawai, Badiya ta amshi jakar hannunta tace “Toh sannu da xuwa, Bismillah” Bin bayanta Jiddah tayi, ta xauna parlor, Badiya ta shiga dakin yan matan Hajiya Rukayya ta ajiye mata jakarta. Karfe biyar saura Abuturrab ya isa gidan Umma, ya fi minti biyar cikin mota sanin da mutane gidan shi kuma ba iya shiga xai yi ba, daga karshe kawai Maman Abdallah da ya gani a compound ya aika ta kira masa Jiddah, ba a dau lkci ba sai ga ta, tace “Wllh yallabai Umma tace suna can gidansu amarya” Da mamaki ya dinga
kallonta, can yace “Toh nagode” Tada motar yayi ya bar layin ya dau hanyar gidansu, bayan yayi parking a waje ya dau waya ya kira Siyama tana dagawa yace “Ki ce Jiddah ta fito” Tace “Yaya mu muna wajen make up fa, kuma har muka bar gidan bamu ga ta xo ba” ya d’an yi shiru, kafin ya katse wayar. Tunanin wanda xai kira ya dinga yi a ciki amma ya ga ba kowa kuma don ko hauka yake ya san baxai kira Ummi ba, d’an tsaki yyi ya tada motarsa ya bar wajen. Tun da Abuturrab suka isa wajen da ake dinner tare da Ahmad da sauran abokansu yake xuba ido yaga inda xai hango Jiddah a wajen amma bai ga alama ba, hakan bai wani damesa ba don dama xuwa dinner din ne baya son ta xo ya kaita can gidan Umma, tun sanda Aneesah ta kyallara ido ta gansa take masa zarya a wajen, barin yanda taga yayi wani kyau cikin fararen shaddan da duk abokan Ahmad suka saka, ita a dole sai ta ankarar da jama’a cewar saurayinta ne, Ko mayafi bata daura kan damammen doguwar rigar jikinta ba shi dai sai bin ta yake da kallo, wani abokin Ahmad dake side din Ahmad din Abuturrab ke ta kallo yana son tuna inda ya ta6a ganinsa, he looks familiar amma dai bai ce masa komai ba, karfe goma saura Aneesah ta xo ta samesa tana yauki tace “My captain wai xaka xo ka maida su Mummy gida yanxu” Ya d’an kalleta yace “Toh ai bani na taho da motata ba, ban ma san inda yake yanxu ba, nima abun hawa na samu ya kawo ni nan” Tace “Haba Captain, ko wajen daya daga abokanku baxa ka amshi mota ka maida su gida ba….” Ko rufe baki bata yi ba sai ga aunty ita ma ta sha wani ubansun lace tana goge xufan goshinta da handkicin hannunta tace “Aliyu ka tashi ka maida su Hajiya Safiyya gida” Bai ce mata komai ba, tace “Ko baka ji na ne?” Yace “Toh bari in nemi wanda makullin motata ke wajensa” Juyawa tayi ta bar wajen, ya kalli
Aneesah da ta hade rai tana kallonsa, d’an murmushi yyi yace “Kema dai kinsan wasa nake, dole in nemo mota ko na waye in maida su” Yana fadin haka yayi patting shoulder din Umar dake side dinsa yace “Bani makulli
n motarka pls” Umar ya mika masa sannan ya mike yace “Kice su fito” Daga haka ya nufi hanyar fita daga hall din…. Karfe daya Abuturrab ya koma gidansa bayan sun maida duk bak’in da suka je dinner masaukinsu, ya fi minti goma xaune a parlornsa thinking of where Jiddah might be, daxu da ya maida Mum din Aneesah har gida ya shiga bai ga alamar tana nan ba, shi kuma ya kasa tambayar Ummi, akwai wasu bakin da still ya mayar can gidan Umma, can ma ya shiga bai ganta ba, bayan kuma ya tambayi Maimoon tace ai tana gidan Umma, mikewa yayi daga karshe ya wuce sama xuwa dakinsa don ya gaji sosai. Da asuba kiran sallah ya farkar da jiddah, ta mike xaune daga kan gadon da take tana kallon yarinyar dake kwance saman gado gefenta, tun xuwanta gidan jiya banda ita da Badiya bbu kowa a gidan har tayi
bacci wajajen karfe goma saura, bandaki ta tafi ta dauro alwala ta fito sannan ta tada yarinyar da baxata wuceta ba, yarinyar ta mike xaune, ita kuma ta shimfida darduma ta fara sllh…. Karfe tara saura yarinyar da tayi wanka ta shirya cikin atamfa ta kalli Jiddah tana murmushi tace “Ya sunanki?” Jiddah tace “Jiddah” Yarinyar tace “Ni sunana Amina, mu je parlor mu gaida su Mama sun fito” Jiddah ta saka Hijab dinta ta bi bayan yarinyar suka fita parlor, yan mata biyu ne xaune parlon sai Hajiya Rukayya, wanda Jiddah na ganinta ta gane mahaifiyarsu ce don sun yi kama, Jiddah bata yarda ta xauna kan kujera ba ta gaida matar, ta amsa da fara’a tana tambayarta ta tashi lafiya, Jiddah ta sunkuyar da kanta,