JIDDAHTUL KHAIR 32

sauran yan matan ma sai kallon Jiddah suke, Wani ne ya shigo parlon daga waje waya kare kunnensa, ganin mahaifiyarsa a parlon ya katse wayar ya zauna yace “Ina kwana” Tace “Lafiya lau… Jiya kuma sai kayi wucewarka ka bar mu a event center” Yace “Mama ciwon kai wajen ke sa min, it’s been long da na tsaya waje that’s so noisy haka” Hajiya Rukayya tace “Toh Allah ya kyauta” Tun da ya shigo Jiddah ke kallonsa kamar taga wani mugun abu, Ganin xai kalli direction din da take ta dauke kanta da sauri gabanta na faduwa, Yace “Mama bakuwa ku ka yi?” Hajiya Rukayya tace “Ehh, ga breakfast dinka can a dining” Yace “Ohk” sannan ya mike ya tafi dining din, Mikewa Amina tayi ta tafi dauko ma ita da Jiddah breakfast don taga alamar yayyinta duk sun yi, kuma da ba don Jiddar ba tare xata je ta xauna su yi breakfast din da yayanta, gaba daya Jiddah ta kasa sakin jiki a parlon, lkci lkci take satan kallon hanyar dinning din, daga karshe dai ta mike xata wuce daki, Hajiya Rukayya tace “A daki xaki yi kumallon?” Ta d’an yi murmushi ta gyada kai ta wuce daki da sauri, dole dakin Amina ta kai masu Breakfast din. A ranan bayan an sauko juma’ah aka daura auren Ramlah da Ahmad… Abuturrab na tsaye daga bakin kofa a bedroom din Umma bayan sun gaisa yace “Tana gidan nan ne Umma?” Umma ta kallesa tace “Wa?” Jin bai ce komai ba tace “Wai Jiddah?” Yace “Eh” Tace “Ba a jima ba suka tafi can gidanku da Maman Abdallah” Bai kuma cewa komai ba, tace “Hajja
kuka tace tun da ta xo baka je ka gaisheta ba” Yace “Ai ban je can gidan ba Umma, anjima da daddare xan shiga in gaisheta” Tace “Yauwa gwara kaje din da daddare dama ya fi, an kai maku abincin kuwa?” Yace “Ehh an kai” daga haka ya juya ya fita. Da yamma su Amina duk suka tafi gidan yinin Biki, Hajiya Rukayya kuma tun karfe goma dama ta bar gidan, gidan ya rage daga Jiddah sai Badiya, tana kitchen tare da Badiya tana tayata girkin dinner, wayar Badiya dake parlor ya fara ring, Badiya tace “Dauko min
wayar Jiddah…” juyawa tayi ta fita xuwa parlor, dai dai nan kuma aka bude kofar parlon suka hada ido, sanye yake da farar shadda idonsa sanye da glasses, sosai gabanta ya fadi, ta sunkuyar da kanta tana kalle kallen inda xata ga wayar Badiya, kasa karasowa cikin parlon yyi, sbda rudewa ta ma rasa inda wayar yake ta juya xata koma kitchen din taji yace “Jiddah” juyowa tayi suka sake hada ido, tayi murmushin karfin hali tace “Ina
yini?” Ya karaso cikin parlon yana ci gaba da kallonta da mamaki, bata jira me xai ce ba ta juya da sauri ta koma kitchen din. Har Hajiya Rukayya ta dawo wajajen magrib Jiddah bata sake yarda sun hadu da Yousuf ba, can daki ta shige taki fitowa through out, Hajiya Rukayya na shigowa gidan ta kira Yousuf a waya don baya nan, yana shigowa tace “Don Allah bakuwar nan xaka ajiye min gidansu Ahmad yanxu, Hajiya Ramlah tace ka kaita” Yousuf yace “Ohkk” Har mota su Amina suka raka Jiddah, shi da Yousuf na xaune cikin motar tasa, Jikin Jiddah yyi sanyi ganin shi xai maidata, hannu kawai ta daga ma kanninsa har suka fita compound, sai da suka d’an yi nisa taji yace “Dama ke yar uwar Ahmad ce?” Kai ta gyada masa kawai, ya d’an kalleta yyi murmushi yace “Har yanxu sai kice min baki da waya ko?” Ta gyada masa kai, yace “What if na baki tawa wayar?”
Ta xaro ido tace “Sai in ce wa ya bani?” Yace “Ni” ta girgixa kai tace “Aa bana so” yace “Jiddahh” ta d’an kallesa suka hada ido, yace “Kin san wani abu?” Ta girgixa masa kai, yace “Tun da muka hadu dake a jirgi kullum nake addu’an Allah ya sa in sake arba da ke, sae gashi kin xo har cikin gidanmu, kinsan me yasa hakan ya faru?” Nan ma ta girgixa masa kai, yace “It is because i have good intention toward u…” Jiddah dai tayi shiru kamar ta gane me yace. And the rest of the ride was silent, yayi parking dai dai kofar gidansu Ahmad ya juya yana kallonta, yace “Tunda baxa ki amshi wayata ba, xan kiraki ta wayar Maimoon” Ita dai bata ce komai ba, ta bude motar ta sauka, ta bude baya ta dau jakan kayanta, Yousuf na kallonta yace “Sai na kira” Tace “Toh” sannan ta nufi gate, shi kuma yayi reverse…. Dama Umma Jiddah kawai take jira don har ta saka Hijab dinta tana parlor a xaune, Jiddah na shigowa kuwa ta saka driver ya kai su can gidansu Abuturrab, har sannan da akwai sauran yan biki a gidan duk da tun wajen shidda saura aka kai amarya, direct parlon Abban
Abuturrab Umma ta nufa tare da Jiddah suka shiga da sallama, Abban Abuturrab da brothers dinsa ne a parlon sai Hajja dake xaune kan carpet, bayan ta xauna suka gaggaisa, ta gaida Hajja ma, Hajja tace “Ni dai tun jiya nake ta kallon ki Ramlah, ya aka yi kika amince kika narka uban kiba haka, to ai ba kyau, mu a masar da tuni an kai ki asibiti duk hankali a tashe, mu ba ma haka a can” Umma dai bata ce mata komai ba, Can ta kalli Jiddah da ta sunkuyar da kanta tun bayan gaida su Abba tace “Ita kuma wannan sadaka yallar fa?” Nan ma babu wanda ya ce mata komai, Abba ya dau waya ya kira Ummi ya sanar mata Umma ta iso, su xo tare da Aunty, Hajja tace “Ai masar tayi wallahi, ba ruwanmu da abinda bai shafemu ba, kowa ta kansa yake, shi yasa xuwa jibi nake son idan Allah ya kai mu in koma, nafi wayo a can…” Ummi ce ta shigo parlon tare da Aunty, tunda Jiddah taga Aunty gabanta ke faduwa, Brother din Abba dake gefensa yace “Ka kira Aliyun ne?” Abba yace “Ehh na kirasa” Abba bai rufe baki ba Abuturrab ya shigo parlon da sallama, sosai gabansa ya fadi ganin Jiddah da Umma a parlon, ya dai dake ya xauna, sannan ya gaida kowa na parlon…. Brothers din Abbansa ne kadai suka amsa gaisuwarsa, Abba na kallonsa a takaice yace “Ina takardan da ka rubuta ma yarinyar nan?” Abuturrab ya buda ido sosai ya kalli Jiddah, da farko kasa cewa komai yayi, can kuma yace
“Takarda kuma Abba?” Lkci daya hawaye ya kawo idon Jiddah ta kalli Umma da ta hade rai, Abba yace “Ina tambayarka kana tambayata? Are u stupid?” Yyi kasa da murya kamar wani mara lfya yace “Abba ai ban san wani takarda ba” Umma ta kalli Jiddah tace “Ya rubuta takarda ya baki ko bai rubuta ba?” Hawayen idonta na xuba ta kalli Umma ganin yanda ta daure fuska cikin rawan murya tace “Ya rubuta” Kallonta kawai Abuturrab yake ko kiftawa babu, Umma tace “Yace maki me a jikin takardan?” Da kyar tace “Wai ba aure a tsakanin mu, shi ba mijina bane” Aunty dake ta gyara xama taji kamar ta saki shewa a parlon murmushinta ya kasa boyuwa, on a serious note Abba na kallon Abuturrab yace “Mu ka mayar kananun mutane Aliyu? Ashe baka dau addininka bakin komai ba bamu sani ba, for all this while kana xaune da yarinya babu aure Aliyu??” Da kyar Abuturrab yace “Abba wllh wllh ba saki na rubuta a takardan ba…” Hajja dai ta hangame baki tana bin kowa da kallo a parlon, Caraf Aunty ta amshe tace “Toh ai aikin banxa kenan, tunda duk ka bi ka sanar ka saketa aure kuma ai ya
lalace, ko ka mance addininka ne? Ni kaina kace min ka saketa ya fi sau talatin, ga Aneesah ga Ahmad da abokanka, ka ga kuwa ta saku” Abuturrab ya kalleta xuciyarsa na tafarfasa yace “Toh ai ita bance mata na saketa ba, na dai ce mata ni ba mijinta bane, ban ta6a bude baki nace mata na saketa ba….” Mikewa Abba yayi ya tafi daki sai gashi ya fito…. Abuturrab ya dinga kallonsa xuciyarsa na bugawa.