JIDDAHTUL KHAIR 33
Abba ya ajiye masa takarda da biro din hannunsa ya koma ya xauna yace “Tunda kana kokwanton auren da ake ce maka babu tsakaninku upon sanarwa da ka dinga yi ka saketa, to ni yanxu na umarce ka da ka kara wanda baxa kayi kokwanto ba a ranka” Kallonsa kawai Abuturrab ke yi kamar bai gane me yake nufi ba, Abba ya daka masa tsawa yace “C’mon my frnd ina sauraronka” Ya sauke idonsa a hankali yace “Toh ai Abba ni bance baxan xauna da ita ba, ban ta6a maku musun xama da ita ba, tuni na riga da na hakura….” Da karfi Aunty tace “Wllh karya kake munafuki… har ce min kayi kawai sbda Abbanka kake xaune da ita bayan ka saketa don kar ya samu labari yayi fushi da kai, kuma mu baxa mu xuba maka ido kuna xaman haram da yarinya ba, banda ma dai ni da na damu da lamarinka, ina ce ranan da na gano irin xaman da ku ke na xo na sanar gwaleni Abbanka yayi, to Alhmdlh ai yanxu tunda Hajiya Ramlah ce ta xo da batun da kanta” a kufule Hajja tace “Waye wannan dallah… Ya xa ki cika ma mutane kunne haka, ita uwar yaro ma ta ja bakinta tayi gumm kamar sabuwar kurma sae ke xaki
dinga daga jijiyoyin wuya kina hak’i uwa dai kin hada wani abu da Aliyun, iyakarki fa matar ubansa, waye bai san auren cin amana ku ka yi da Usman din ba, daga dai ke da uwarki kuna fama da bakar talauci kuna tuyan masa da miyar taushe a daya daga gidajen hayana dake Tudun wada, shi kuma Usman na aikesa yaje ya fatattaki wani kato da yaki biyana haya kusan sati uku da karewar kudinsa, shkkn fa mata kika makale ma d’a na har da kullo masa yar wainar shinkafa a leda, to mu muka san abinda aka barbada a kai sai ga Usman ya birkice shi xai kara aure bayan ko shekara biyu da auren wannan Bafillatanar Hauwan bai yi ba, a takaice dai wllh tsallak
e maganata yayi ya aureki don na hanasa yaki ji ya bada toka a ido xai xageni, to ba dole in yafe masa ba tunda kowa dai yasan ku ‘yan Benue ne, Mu dai babu abinda muka sani da ya wuce wannan, to yaushe ma xa a ga haka a Masar? Aa wllh basa haka….” Alhaji Umar yayi kasa da murya yace “Hajja ai ina ga ba wannan xancen muke yi a nan ba, duk ba shine ya kawo mu nan ba” a fusace Hajja tace “Toh don ba xancen ake ba sae in yarda ta gigita min jik’a, ni dai har gobe ina danasanin basu gidan hayata, daki daya ma fa suka kama suke rayuwa a ciki, kafin ma in basu dakin cewa suka yi gidan da suka baro watsi aka yi da kayansu bakin titi a unguwar
mu’axu, gashi suka dinga ban wahala da kyar suke biyan kudin hayan a lkcn ma wllh.. to ni duk na wannan ba don Allah ma bai ce ayi tone tone ba, wanda kuma ya rufa ma d’an uwansa asiri Allah ma xai rufa masa asiri, amma ai an cuci Usman, to kuma ni ance min Aliyu ya auri yar hayi lkcn ina Masar, tsoro ya kamani na fita hayyacina na gigice da naji wannan xance sbda ni nasan ina ne hayi, kuma ni nasan mutanen cikinta, to sae gashi kabiru yace min ae suna xaune lafiya lau da matarsa, hakan yasa na saki raina duk da ban samu xuwa bikin ba, toh ynxu abinda ban gane ba wannan yar farar dake xaune ce yar hayin koko?” Umma tace “Ita ce” Hajja tace “Ikon Allah… toh kai Usman ya kake son kashe masu aure kamar kai ka halicci auren?” Alhaji Umar yace “Hajja babu wannan auren fa yanxu
musulinci, don ya riga da ya saketa da bakinsa, sannan kuma ya saketa a rubuce, ni ba mijinki bane ae dai dai yake da na sake ki….” Hajja ta rike ha6a tace “Naga jaraba, a gabanka aka yi sakin kake wnn ciccijewan ko kawai karere, Sannan kana min gatsal gatsal idan shafa’atu ce xaka mata haka yau?” Abba yace “Don Allah Hajjaju kiyi shiru muyi abinda ya kawo mu nan, baki san komai a kan maganar nan da ake a nan ba, yaushe
rabonki da kasar??” Hajja ta rungume hannu hade da ta6e baki tace “Nayi shiru, amma mu a masar wa xai yi haka? Wllh ba a haka, ayi aure kuma a dawo ana cewa ya mutu bai mutu ba” Ta gefen ido Abuturrab ya kalli Jiddah da ta kasa dago kanta, Aunty dai ta wani sha kunu a parlon tun bayan xancen Hajja a kanta, ita dai Ummi kallonsu kawai take ba um ba um um, a fusace Abba yace “U are wasting our time Aliyu, saki me hujja nake so kayi ynxu tunda duk wanda kayi a baya baka aminta da su ba…” Ya dago kansa yana kallon Abbansa yace “Abba ni nasan na aureta sannan ina xaune tare da ita saboda inyi biyayya gareka, bayan hakan babu wani abu
kuma….” Abba ya katse sa yace “Toh an dauke maka wannan biyayyan, write d divorce now, sai ka tashi ka tafi Allah ya baka ladan taimako, ae kayi me wuyan tunda ka rabota da tsananin da take ciki” Abuturrab bai kuma cewa komai ba, bayan few seconds yace “Yanxu sakin xan rubuta mata?” Abba yace “Ehh, baxa ka mayar da mu kananun yara ba mu xuba maka ido, har yau mun rasa gane xaman me ku ke da yarinya” Abuturrab ya sunkuyar da kansa ya fara rubutu a takardan, d’aga kai Jiddah tayi tana kallonsa, ya gama rubutun ya mike da ladabi ya mika ma Abba, Abba ya amsa yana duba content din takardan, Abba yace “Good, Allah ya maka albarka, ya baka ladan taimako, daga yanxu kuma babu ruwanka da duk wani harka da ya shafeta, xa mu yi mata komai in sha Allah, kai ma kuma kayi iya naka kokarin don ta dalilinka duk muka santa, Allah ya maka albarka….” Abuturrab ya amsa da “Ameen” Sannan ya juya ya fita daga parlon jiddah ta bi sa da kallo, Abba ya nuna ma brothers dinsa biyu takardan, Alhaji Umar yace “To maa sha Allah, kaga yanxu babu wanda xai ci gaba da kokwanton xaman da suke,
Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi, shi kuma Allah ya saka masa ya basa ladan taimakonsa, ku kuma Allah ya baku ikon riketa da gaskiya” Aunty da taji jikinta na wani tsumma don farin ciki gaba daya ta mance abinda Hajja tayi mata sae jiran takardan take ya xo garesu, ai ko ana miko mata bayan ta karanta tayi wani murmushi ta mika ma Umma, Umma ma ta mika ma Ummi bayan ta karanta, Hajja tace “Amma na tsorata da lamarin Aliyu, Kunga da yana sonta da gaske ai kuka xai sakar mana a nan yace shi baxai saketa ba, amma almurin kamar jira yake gashi ya cike takarda da rubutu, aa gaskiya ba sonta yake ba, ku duba fa babu wani gardaman a xo a gani ya rubuta takardan, Lahh wanne mutum a masar, to amma ai shkkn sae a bani ita mu tafi Bauchi don kwana biyar xanyi a can kafin in koma Masar, idan ma kunga xaku iya biya mata jirgi kawai sai mu tafi tare, ai d’a na kowa ne bawa sai mai shi…” Umma ta kalleta da sauri tace “Hajja karatu xa a sata ai” Wani kallo Hajja ta watsa mata tace “Shi kuma masar din duk jahilae ne ba a karatu…. Banda neman magana ina ruwanki Ramlah, ni fa da d’a na nake kika tsomo baki, ko Ahmad ne ya tsintota a hayi?” Ta gefen ido Ummi ke kallon Hajja, Abba yace “Dama haka ake tafiya Masar din
Hajja, ina laifin ma kice idan kin tafi a turo ta?” Hajja tace “Kai ba ruwana ni ku rabu dani, xa a Wani min caaa, dangin uwa ko na uba, meye hadina da ita banda Aliyu da ya aurota a gantale ya saketa kuma a gantale, kuma ma wasa nake, haka kawai inje in daura masu nauyi nima da ya ake bani yar gurasar da ake ban balle na tafi da wata?” Mikewa tayi tace “Banda Najeriya ina ake aure a gantale ayi saki a gantale, Hauwa taho ki bani sakon da na baki” Tana kai wa nan ta fita, Ummi ta mike ta bi bayanta, Aunty ta bi ta da harara, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace “Alhaji xan tafi da Jiddah ta koma gidana ta fara karatu” Caraf Aunty ta