JIDDAHTUL KHAIR 33
amshe tace “Me xai hana tayi a nan din, ga dai sa’aninta su Aisha” Abba yace “Da nan din da can ai duk daya ne, Allah dai ya bata ilimi mai amfani” Ko kadan Aunty bata ji dadin haka da Abba yace ba, Umma tace “Toh nagode Alhaji, Allah ya tayani riko” Duk suka amsa mata da “Ameen” amma banda Aunty da ranta ya baci, can dai tace “Amma ai xata dinga xuwa nan din ko” Umma tace “Aa me xai hana kuwa” Umma na fadin haka ta mike tana kallon Jiddah tace “Mu je Jiddah” Jiddah ta mike a hankali ta bi bayanta, Aunty ta bi ta da kallon tsana, shi kam Abba tausayinta kawai yake ji, banda rashin gata ya xa ayi hakan ya faru gareta ma. Bangaren Ummi Umma ta kai ta, Ummi na xaune parlonta da Hajja dake mata magana kasa kasa, amma ganin Umma sai tayi shiru, Umma tace “Toh yaya mun tafi sai da safe” Ummi tace “Baxa ku yi isha ba?” Umma tace “Eh to bari inyi” Daga haka ta karasa bedroom din yayarta, Jiddaj dai na rakube jikin
kujera, Ummi ta kalleta tace “Kije kiyi sallan ke ma” Mikewa Jiddah tayi ta fita, Hajja ta tabe baki tace “Toh ai gwara ma da aka kashe wannan auren don ai Aliyu d’an usuli ne, ita kuma bamu san yaya ba” Ummi tace “Ai babu wanda bashi da usuli Hajja” Hajja tace “Aa Hafsat dai bata da shi, an rasa gane ko kwatakwali ce har yau, duk da tace uwarta yar Benue ce” Ummi dai bata ce komai ba, Hajja tace “Shi yasa gashi duk ta amshe gida tayi bake bake, komai sai inji Usman yace Hafsa, to wacece kuma Hafsa, dama Hadiza ta bani labarin irin xaman da ku ke yarda ce kawai ban yi ba, gashi duk ta rufe maki baki ta amshe gida, wa ya sani ko ma har da ya yanki? Tunda na xo naga take takenta komai sai ace sai ita, to a kan me?” Ummi tace “Aa Hajja kowa ai da matsayinsa a gidan” Hajja tace “Toh kunga lalacewa ko? Wani matsayi matar da ta kwace maki miji ta karfi, me yasa kike abu sakwa sakwa kamar warce aka ce ma je ki kya gani Hauwa, komai fa na bikin nan naga sai dai ace Hafsat to wacece kuma Hafsat,
gashi ana maganan tabargaxan da yaro yayi mata tayi bake bake a kan xancen kamar d’an ta, to ni tunda na xo ma ba sau daya Salem ya shigo gaisheni ba, duk sun tsotsa a nono wllh, dubi fa Aisha kamar yar karuwai Allah na tuba, to ba dai komai tunda duk jikokina ne, amma idan xaki tashi tsaye ki amshi gidanki ki tashi” Fitowar Umma yasa Hajja tayi shiru, Umma tace “Toh sai da safe Hajja, yaya sai mun yi waya” Hajja tace “Toh Allah ya ba yara xaman lafiya ya kauda fitina amma ki dai je asibiti kiga kibar ta mecece kika narka haka kinji” Umma bata tankata ba har ta fita, Hajja tace “Toh sai da safe” Sai da Jiddah ta sake shigowa tayi ma Ummi da Hajja sai da safe sannan suka bar gidan tare da Umma, har driver ya maida su gida Jiddah bata cewa komai, duk tayi sanyi sosai, ta rasa ko farin ciki take ko bakin ciki, Wajen karfe tara Umma ta xaunar da ita a dakinsu Maimoon tace “Kina ji na Jiddah?” Jiddah ta daga kai ta kalleta, Umma tace “Kin dai ga yanda abubuwa suka kasance, ni nasan Abuturrab bai da niyyar cutar dake a ransa, kuma har abada ina son ki daukesa da girma da mutunci don ya maki abinda ba kowa xai iya maki ba a rayuwa, duk abinda xaki xama a rayuwa nan gaba Allah ne ya tabbatar da hakan amma
Abuturrab ne sanadi, ina son kuma ki maida hankalinki kiyi karatunki, kin san wacece ke kinsan daga inda kika fito” Hawaye ne ya shiga xarya idon Jiddah tana kallon Umma, Umma tace “Ni kuma ina fatan Allah ya bani ikon yi maki duk abinda ya kamata a rayuwarki Jiddah” Cikin rawar murya tace “Toh Umma baxan sake ganinsa ba kenan?” Da mamaki Umma tace “Don me baxa ki gansa ba, in dai Allah ya kawosa gidan nan ai xaki gansa, sannan xaki dinga yawan xuwa gida Ummi, idan baku hadu a nan ba xaku hadu a can,
balle ma nace tsakaninki da shi kawai girmamawa ki daukesa kawai a matsayin babban wan ki, nasan shi ma a matsayin kanwarsa xai daukeki” Jiddah ta share hawayen idonta a hankali tace “Toh Umma nagode” Umma ta sakar mata murmushi, har ranta taji tana son Jiddah tana kuma son inganta rayuwarta, Umma tace “Gobe da safe sai mu je can gidan a kwaso duk wani abu naki” Jiddah ta gyada mata kai kawai, Umma ta mike tace “Toh sai da safe” Daga haka ta nufi kofa Jiddah ta bi ta da kallo wasu hawayen na kawowa idonta, Umma na fita Maimoon ta shigo dakin. Washegari misalin karfe Goma Umma ta kira Abuturrab, miss calls tayi masa kusan uku kafin ya daga, bata amsa gaisuwan da yake mata ba tace “Kana gidanka ne?” Yace “Ina nan” Umma tace “Ohk i am coming now” Bai ce komai ba ta katse wayar, tare driver ya kai su gidan Abuturrab da Jiddah da Maimoon da safiyya, mai gadi ya bude masu gate driver ya shiga da motar cikin compound, Umma ta sauka motar sannan su Jiddah, Hijab ne har kasa jikinta, suka bi bayan Umma xuwa entrance din parlon, a bude suka tarda parlon, yana kwance saman doguwar kujera da jallabiya, suna hada ido Jiddah tayi saurin
sunkuyar da kanta gabanta na bugawa da karfi, sanye yake da jallabiya ya mike xaune a hankali yace “Ina kwana Umma?” Tace “Lafiya lau, ya gajiyan jiya?” Yace “Alhmdlh” Maimoon ta gaishesa ya amsa, Jiddah ma tace “Ina kwana?” Sai dai taki yarda ta kallesa, bai amsa ba ita dai ta xauna kasa kusa da kujeran da Umma ta xauna, Umma tace “Jiddah xata debi kayanta na nan ne” Ba tare da ya kalli Umma ba yace “Ohk” Umma ta mike tana kallon Jiddah tace “Mu je” Mikewa Jiddah tayi ta nufi stairs Umma na biye da ita Maimoon ma ta bi bayansu, da ido Abuturrab ya bi su har suka haura sama, Kaf sai da Umma ta kwashe duk abubuwan Jiddah dake dakin, Maimoon ce ke kai wa booth din mota, Ita dai Jiddah na tsaye jikin kofa sai kallonta take, ta rasa dalilin da yasa taji tana son tayi kuka, Umma ta mika mata babban ledan da ta hada duk abubuwan gaban madubi a ciki tace “Ki kai wannan” Jiddah ta karasa ta amsa ta nufi kofa ta fita, a stairs suka hadu da Maimoon, Maimoon tace “Kawo in kai toh” Jiddah ta kirkiri murmushi tace “Xan kai” Maimoon ta shiga dakin ita kuma fita, satan kallon parlon ta dinga yi taga baya nan, ta fita balcony, sosai gabanta ya fadi da ta gansa a xaune kan kujera yana danna wayarsa. Xata sauka stairs din balcony din taji yace “Toh ni dake wa yyi lose?” Ta juya tana kallonsa
don bata gane me yace ba, yayi wani murmushi ya mike, speaking calmly yace “Kema kinsan wllh idan ba kaddara ba babu abinda xai hadani dake a rayuwa balle har in aureki bisa kuskure, aurenki da ni babban kuskure ne wanda nayi sbda in taimaki rayuwarki.. banda haka ai ni nafi karfin ki,
komai da ya faru ya faru ne sbda haka Allah ubangiji ya tsara, duk da fin ki komai da nayi haka na hakura na xauna same roof dake sbda biyayya da kuma xuciyar musulinci, amma wai har ke xaki je ki sanar ma iyayena na sakeki? Toh yanxu da na maki sakin me hujja akwai wani abu da xai ragu a rayuwata ko kuma wani asara xan yi?” Ita dai kallonsa kawai take ko
kiftawa babu, yayi wani murmushin kuma yace “Toh na maki duk abinda na maki saboda Allah ba don ki nuna kin san ni wataran ba, kai ni ko a hanya kika gan ni kar ki ta6a nuna kin ma san ni don kunya hakan xai bani, kiyi wucewarki inyi wucewata, na kuma fi kowa farin ciki da murnan xuwa karshen wannan al’amarin, i am now free like every other….” Jiddah dai kallonsa kawai take bbu ko kiftawa, ganin ya koma ya xauna cikin sanyin murya tace “Toh nagode” Daga haka ta juya ta kai ledan mota… Tare suka fito gidan da Umma bayan duk an kai komai mota, Har sannan yana xaune balcony, Umma tace “Toh sai anjima, yaushe xaka koma aikin” Yace “Anjima in sha Allah” Tace “Toh Allah ya tsare” Daga haka ta nufi mota, Maimoon tace “Sai anjima yaya” Yace “Ohk” Sai da Jiddah ta sauka balcony ta d’an kallesa tace “Sai anjima….”