JIDDAHTUL KHAIR 34
Bayan sati biyu Jiddah na xaune dinning area ita kadai bayan magrib, Hijab ne har kasa jikinta, Huraira kuma na kitchen tana wanke wanke, gaba daya hankalinta na kan takardan gabanta taji an danna bell, mikewa tayi ta nufi kofar ta bude, ta koma baya tana kallonsa tace “Ina yini” Da murmushi yace “Lafiya lau Jiddah” ta juya ta koma parlon ya karaso ya xauna, tace “Ya Aunty Ramlah?” Yace “Tana gaisheku, Umma na daki ne?” Tace “Ehh” yace “Tou xauna mana” d’an murmushi tayi ta xauna edge din kujera yace “Kin fara karatu koh?” Tace “Eh” yace “Amma ki fada min
gaskiya, kina ganewa?” Ta gyada masa kai, yace “Aa bude baki ki min magana” Sunkuyar da kai tayi har sannan tana murmushi tace “Ina ganewa” Yace “Toh wani rana da wani rana ku ke karatun?” Tace “Ranan litinin xuwa juma’ah” Yace “Asabar da lahadi fa?” Tace “Islamiyya muke xuwa tare da su Maimuna” Yace “Toh me da me ake koya maki litinin xuwa Juma’ahn?” Tace “Karfe tara na safiya take xuwa mu yi boko xuwa karfe biyu, sai kuma Islamiyya karfe uku xuwa shidda” Yace “Duk ita ke maki bokon da
Islamiyya?” Ta girgixa kai tace “Aa wata ce daban take xuwa karfe uku” Yace “Maa sha Allah, kawo takardun naki in ga” Mikewa tayi ta nufi dining ya bi ta da kallo ta dauko jakar da duk litattafanta ke ciki ta dau har da na kan dining table sannan ta kai masa, ya amsa yana dubu abubuwan da suka yi na sati biyu, ita dai tana xaune tana wasa da fingers dinta, ya daga kai ya kalleta yace “Anya ke da kanki kike aikin nan da malama ke baki?” Tayi murmushi tace “Ni ce nake yi ka tambayi Maimuna” Yace “Maa sha Allah, ki dinga maida hankali haka kinji?” Tace “Toh” Ya dau wayarsa dake ring, ta jira har ya gama wayar ya ajiye sannan tace “Aliyu fa?”
Daga kai yayi ya kalleta, ta sauke idonta yace “Waye Aliyu?” Jin bata ce komai ba yace “Ohh captain wai?” Still bata ce komai ba, yace “Yana kano, mun yi sati biyu bamu hadu ba, kuma bana jin ya xo weekend” Tace “Toh” Umma ce ta shigo parlon ganin Ahmad tace “Yaushe ka shigo?” Yace “Not too long” Ta karaso ta xauna yace “Ina yini Umma” Tace “Lafiya lau, yau ma baka xo da Ramlan ba?” Yace “Ehh na barta da su Aisha ne sun je can gidan” Umma tace “Ohk” kallon Jiddah tayi tace “Har kin gama karatun?” Tace “Aa ina kan yi” Tana fadin haka ta mike ta isa gun Ahmad ta kwashi duk takardunta ta wuce daki, Ahmad yace “Cewa nayi ta kawo in ga
performance dinta and naga she is really trying” Umma tace “Gaskiya kam, she isn’t dull kawai dai karatun ne bata samu ba, amma in sha Allah nan da few months a yanda naga take da hazaka she might catch up with her mate, tana da kwakwalwa kam maa sha Allah” Ahmad yace “Toh Allah ya sa hakan, sai ayi enrolling dinta jss3 ko?” Umma tace “Ehh” Ya shafa kansa yace “Umma daxu Yousuf ya kirani…” Umma tace “Ya aka yi?” Ahmad ya d’an yi shiru, sai kuma yace “Wai a kan Jiddah…” Murmushi Umma tayi tace “Ni dai nasan ba haka nan yake xuwa gidan nan frequently ba da dalili, toh
maa sha Allah…” Ahmad yace “But Umma ai bata bukatar wannan yanxu, she need to concentrate fully on her studies” Umma tace “Toh ai sai ka jira in gama magana ko… ni baxan hanasa alaka da ita ba, sai dai shigo da batun soyayya gareta yanxu isn’t necessary, he should wait a little….” Ahmad dai bai ce komai ba. Aunty ce xaune gefen gadonta waya kare kunnenta tayi shiru fuskar nan nata a daure, can ta mike tace “Haka yace
maki?” Daga daya bangaren Aneesah tace “Wlh Aunty” Aunty tace “Toh kyaleni da d’an iskan, nasan maganinsa….” Aneesah tace “Ni fa wllh Aunty yau kusan wata daya kenan na ma kasa gane kan relationship din nan namu” Aunty tace “Daina kiranki yayi?” Tace “Toh ai dama tun farko ba kira yake ba sai in ni na kira ya bi miss call, yanxu kuma ko na kira din ma sai sanda ya ga dama yake kira, sai yace aiki yayi yawa…” Aunty tayi shiru tana sauraronta, sai kuma ta sauke wani ajiyar xuciya tace “Amma kuna dai maganan still koh?” Tace “Aa muna magana, kawai sabon miskilanci da jiji da kai ya karo… Sai yayi ta cewa shi baya son damuwa, shi baya jin dadi, shi he want to sort somethings bothering him, shi yana son
break, shi he wants to be alone for sometimes, haka dai wllh… Kamar baya son magana da ni” Aunty dake ta jin ta, tace “Amma ya siya maki abinda nace kice ya siya maki ko bai siya ba?” Tace “Aa ya tura min kudin har da kari ma” Aunty tace “Toh shkkn, xan kiraki xuwa anjima, ki kwantar da hankalinki” Tana kai wa nan ta katse wayar tayi dialing number Abuturrab, sai da ya kusa yankewa ya daga, yace “Ina kwana Aunty?” Tace “Wani laifin muka maka Aliyu yau kusan sati uku babu kai babu labarin ka?” Yace “Aa aiki ne yayi yawa yanxu…” tace “An sake employing dinka a wani airline din ne bayan wanda kake aiki?” D’an murmushi kawai yyi bai
bata amsa ba, tace “Atoh gwara ai in ji, kuma ai kana shigowa kadunan, xuwa gida ne kawai baka yi” yace “Aa bana shigowa, amma xan shigo friday din nan in sha Allah” Tace “Toh ina saurarenka” Daga haka ta katse wayar. Hijab Jiddah ta dauka xata saka bayan ta gama shiryawa Maimoon ta hade rai tace “Meye hka kuma, ba ga mayafi na ajiye maki ba” Jiddah ta xaro ido tace “To ae an hanani” Maimoon tace “Wa ya hanaki?” Ta sake xaro ido sae kuma tace “Tou bari in sa” daukan mayafin tayi ta yafa, Maimoon ta washe baki tace “Waoww kinga yanda kika yi kyau kuwa” Murmushi kawai
Jiddah tayi, suka fita xuwa dakin Umma, Umma tace “Kuna kai sakon ku dawo, ba sai na gaya maku kuna da Islamiyya karfe biyu ba” Maimoon ta marairaice tace “Yau dai kawai Umma, Sis Ramlah fa na can gidan” Umma tace “Toh ku bani xan ba Driver ya kai idan ya dawo” Maimoon ta xaro ido tace “Aa wllh ynxu xa mu dawo Umma” Kudin mota ta basu suka fita gidan, Jiddah na rike da ledan sakon da Umma ta bada su kai ma Hajja, karfe sha daya da rabi suka isa gidan, Maimoon tayi sallama bakin kofa tayi
knocking sannan ta tura, Jiddah ta bi bayanta, babu kowa a parlon suka nufi part din Ummi, Ummi ta fito daga bedroom dinta jin sallama, ganinsu tace “Aa sannunku da xuwa” duk suka xauna suka gaisheta ta amsa da fara’a tace “Ku kadai?” Maimoon tace “Eh Umma ce ta aiko mu gun Hajja” Ummi tace “Ohk, ya karatu Jiddah” Jiddah ta kalleta ta d’an yi murmushi tace “Alhamdulillah” Ummi tace “Toh maa sha Allah, Allah ya taimaka” Maimoon tace “Ramlah ta koma ne Ummi?” Ummi tace “Aa tana ciki tana bacci”
Maimoon tace “Toh bari mu kai ma Hajja mu dawo” Ummi tace “Ohk” mikewa tayi jiddah ma ta tashi suka fita daga parlon, dakin da Hajja ke sauka idan tana garin Maimoon ta nufa Jiddah na biye da ita, Maimoon tayi sallama bakin kofar sannan ta bude, Hajja ta daga kai tana amsa sallaman, karasawa ciki Maimoon tayi ta duka tace “Ina kwana Hajja” bata jira ta amsa ba ta kalli Abuturrab dake xaune dakin yana kallonsu daga sama har kasa ta cikin glass din idonsa, ta sunkuyar da kanta tace “Ina kwana
yaya?” Yace “Me yasa baki ajiye mayafin a gida kin fito haka ba?” Maimoon ta hau gyara mayafin jikinta tana murmushi, Jiddah dai kanta na kasa ta durkusa ita ma ta gaida Hajja, sannan ta d’an kallesa taga wayarsa yake dannawa tace “Ina kwana” Ya kara wayar a kunne ya mike ya nufi kofa, Hajja ta saki baki tana kallonsa har ya fita, can ta kalli Jiddah tace “Ji ruba66e, toh ke idan ba dai neman wajen xama kike ba meye na gaishesa bayan iyayensa sun sa ya sakeki babu ko dar ya cike takarda ya mika maki, ai babu abinda kika hada da shi kuma yanxu, toh ga dai shi ya gwaleki, tun jiya fa na samu labarin dawowar almurin amma kun ga sai yanxu ya