JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDAHTUL KHAIR 34

shigo gaidani yana shan kamshi ya wani sha uban gilashi kamar sabon makaho, Aa bak’in halinsa ya fi karfinsa gaskiya, alhalin sbda shi nake xaune har yau a gidan nan ban koma masar ba, to Hafsah ta ce min sati me xuwa xa a kai kudi gidan yarinyar da yake so da aure amma in ja bakina inyi shiru tunda ba a gaya min ba tukun, shine yasa nake ta xaune nan Allah” Maimoon dai sai murmushi take, Hajja tace “Toh aiko ku Ramlan tayi?” Maimoon ta ajiye mata ledan kusa da ita tace “Ehh tace mu kawo

maki wannan” Hajja ta leka cikin ledan tace “Ahh da kyau, baiwar Allah nace mata gobe xan tafi shine ta bada tsaraba a kawo min, to tafiya ai ta lalace tunda auren Aliyu ya tunkaro, yanxu shigowarsa nake tambayarsa shi ma ya tabbatar min da haka ne” Jiddah dai sai kallon Hajja take, Maimoon tace “Toh Allah ya kai mu lafiya” Hajja tace “Ameen, ita ma Ramlah gata can ta xo tun shekaranjiya, kilan mijin baya nan, amma da kyar idan ba ciki ne da ita ba, kai cikin ne ma wllh, sai wani salalo salalo take” Maimoon ta kalli wayarta dake ring ta mike tace “Xa mu koma Hajja, sbda muna da Islamiyya karfe biyu” Hajja tace “Toh ai shkkn, anjima xan sa

Aliyu ya kawoni in mata godiya idan ya ga dama kenan, kabu kabu fa yake amma jin kansa yake kamar me wani sana’ar arxiki baya ganin kowa da gashi, ga d’an banxan girman kai, ba ga masu kabu kabun ba muna ganinsu a tashar mota, ga yan acaba suma ai duk kabu kabun ce, to kuma waye shi Allah na tuba” Su dai basu ce mata komai ba suka fita dakin, sai a snn Maimoon ta mika ma Jiddah wayar tace “Yousuf” Jiddah ta amsa ta daga sannan ta kai kunne, murya kasa kasa Maimoon tace “Don Allah kice ya

xo ya daukemu basu da nisa sosai daga nan” Tana fadin haka ta wuce bangaren Ummi, Jiddah ta nufi parlor, cikin sanyin muryarta tace “Ina kwana” Yace “Lafiya lau, me Maimoon take rada maki?” Murmushi tayi ta xauna saman kujera tace “Aa babu komai, ya ciwon kan yayi sauki?” Yace “Alhmdlh, ya su Umma?” Tace “Umma tana gida” Yace “Ku kuna ina?” Tace “Umma ta aiko mu gidansu Aunty Ramlah” Yace “Ohk, yaushe xaku koma gida?” Tace “Karfe biyu xa mu tafi Islamiyya” Yace “Baxa ku dade ba kenan?” Tace “Eh” yace “Toh in xo in maidaku gida?” Ta d’an yi shiru, yace “Kin fa ce kin daina taurin kai” D’an murmushin tayi ta kwantar da kanta jikin

kujera dai dai nan suka yi ido hudu da Abuturrab dake xaune dinning area din parlon da laptop gabansa, wani faduwa taji gabanta yayi, Yousuf yace “Kinyi shiru” Ta dago kanta tace “Toh sai ka xo” Yace “Good, in few minutes time xan iso yanxu in sha Allah” Cikin sanyin murya tace “Toh” Katse wayar yayi, ta dinga kallon screen din, can ta saci kallon

Abuturrab taga laptop dinsa yake dannawa, ta mike ta wuce part din Ummi, ya bi ta da ido. Karfe daya saura Yousuf ya iso kofar gidansu Abuturrab, ganin xa a tada sallah ya sauka ya shiga masallacin kofar gidan, bayan an idar ya kira number Maimoon, Maimoon ta mika ma Jiddah, Jiddah na kai wa kunne yace “Ina waje ku fito” Jiddah tace “Toh” Katse wayar yayi, suka yi ma Ummi sallama a bedroom dinta sannan suka fita, gaban Maimoon ya fadi ganin Abuturrab da ya fito daga masallaci, amma taki yarda su hada ido, Jiddah kam bata ma gansa ba ta kalli Maimoon tace “Ke da kike son ya xo ya daukemu ai ke xaki yi jagora” Maimoon tace “Don Allah ke dai mu je” Jiddah ta fara tafiya Maimoon na biye da ita, ta bude front seat ta

shiga, Maimoon ta shiga baya, sai a sannan Jiddah ta ga Abuturrab da ya tsaya yana kallonsu, Yousuf da ya gansa shi ma yace “Ba yayan nan naku bane wancan” Maimoon ta kirki murmushin karfin hali tace “Ehh, kaje gu gaisa ya Yousuf sai kace masa Umma ce tace ka xo ka daukemu” Ta madubi ya kalleta ta kara kirkiran murmushi, Jiddah dai taki yarda ta sake kallon wajen motar, Yousuf ya bude motar ya sauka ya nufi gun Abuturrab da ya kara waya a kunne roaming about the gate, hannu ya mika masa hade da

sallama yana kallonsa, Abuturrab yyi stretching nasa hannun, nan suka gaisa sannan yousuf ya juya ya koma gun motarsa, yana shiga motar Maimoon da duk hankalinta ya tashi tace “Kace masa Umma ce tace ka xo ka daukemu?” Yousuf yace “He don’t have any business with that” Maimoon bata kuma cewa komai ba, ya tada motarsa suka bar anguwar. Hansai ce xaune da aminiyarta Zulai gaban wani katon mutumi da babu riga jikinsa, Hansai duk ta baxa kunnuwa da idanuwa tana jiran jin abinda xai ce bayan ya gama dube dubensa, Mutumin ya kalleta da idanuwansa da aka lafta ma uban

kwalli yana girgixa kai cikin katon muryarsa yace “Babu wani aure a kan yarinya, amma tana can cikin kwanciyar hankali da daula… Bata da wani matsala a rayuwa, ba abinda ta rasa…” Hansai ta sharce wani bakin xufa a goshinta tace “Toh Malam babu abinda xa ayi da xai sa hankalinta ya karkato ta dawo gida, idan ya so sai a maida min Bibalo can, wllh Malam ina fama da bakar talauci yanxu, jarin babu shi babu dalilinsa kamar dai kar ta bar wajen yarinyar, ga basussukan jama’a a kaina suna min tonon asiri har na fara tunanin in siyar da d’an gidan da muke ciki in biya

bashi sai mu kama haya da sauran, in sake jan wani jari, to amma gidan fa duk ya ru6e, wa xai siya da mutunci” Mutumin wanda da alama ya gaji da surutunta yace “Ki fadi abinda kike so ayi a takaice” Hansai ta gyara xama tayi kasa da murya tace “Kaga Malam so nake kayi duk abinda xai dawo min da ita duk inda take, ta dawo wajena ni ban k’i ko karuwanci ma ta xo ta min ba mu samu na rufa ma kai asiri, nasan dai yanxu karya ne ace bata san maxa ba, dama gata da kyau ga farin jini wllh kasuwa xa mu yi sosai” Zulai sai gyada kai take, Mutumin yace “An gama, dubu hamsin kudin aikin

ki” Zulai ta dafe kirji tace “Dubu ashirin fa Malam, ina nagansa? Bani da shi bani da dalilinsa wllh, ko dubi daya na kaina bana magani yanxu” Yace “Toh ku tashi ku tafi duk ranan da ku ka shirya ku dawo” Xata yi magana cikin tsawa yace “Ku fita nace sai kun shirya” Da sauri suka mike suka fita a d’an dakin, Hansai ta fashe da kuka tace “Yanxu ya xanyi Zulai, kema kinsan bani da ko dubu biyu na kaina wllh, duk na siyar da kayan dakina babu komai balle in dauka in siyar” Zulai tace “Daga karshe dai gidan nan kawai xaki siyar in dai bukata xai biya, in har Jiddah ta dawo ai sai kin kera wanda ya fi wannan a cikin gari, dama ba sai an 6ata ake gyarawa ba, kawai mu je a sa gida a kasuwa…” Hansai ta share idonta

tace “Toh shkkn, in sha Allahu baxan ji kunya ba” Daren ranan Jiddah na karatu a dinning kamar yanda ta saba bayan magrib aka bude kofar parlon, Hajja ce ta shigo sakale da jakarta tace “Assalamu alaikum” Jiddah ta amsa sallaman tana mata sannu da xuwa, Hajja tace “Ina Ramlan take?” jiddah ta mike tace “Tana daki bari in mata magana” Hajja tace “Toh yi maxa wancan d’an daban sai ya iya tafiya ya kyaleni, kinsan dama da kyar ya kawoni sai da uban ya sa baki” Jiddah dai bata ce komai ba ta tafi dakin Umma, ba a dau lkci ba Umma ta fito sanye da Hijab da murmushi tace “Sannu da xuwa Hajja” Hajja tace “Yauwa Ramlah daxu naga abun arxiki

shine nace bari dai in taso in xo da kaina inyi godiya, don mu a Masar haka ake, Allah yayi maki albarka ya kara arxiki sai dai tafiyar ma ta lalace don wannan yaro Aliyu gobe xa a kai kudin aurensa kuma ina nan har sai anyi komai idan Allah ya yrda” Umma tace “Allah sarki, ai da kinyi waya na xo kawai Hajja ba sai kin fito da daddaren nan ba” Hajja tace “Aa barni na xo, banda me sonka wa xai tuna da kai har ya baka tsaraba haka…” Tana kai wa nan ta mike tace “Toh ni dai bari in koma ni da wancan d’an kabu kabun ne muka xo kar ya tafi ya barni in rasa tudun

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button