JIDDAHTUL KHAIR 34

dafawa” Umma tace “Tare da Aliyu ku ke?” Hajja tace “Ehh wllh, sai da ma ya xageni a hanya muna tahowa daga nace masa ba jirgi fa yake figa haka ba, ni dai bakina alaikum naki biye masa ya kunyata ni a kasar mutane” Umma tace “Amma yace wani abu, shine baxai shigo ya gaisheni ba??” Hajja tace “Ahaf ai wannan mutumi dai daga d’an iska sai shi, baya ganin kowa da gashi” Umma ta kira Huraira a daki tace “Tafi kice ma Abuturrab ina kiransa a waje” Tace “Toh” sannan ta fita, Hajja ta koma ta xauna tace “Gwara dai kiyi masa soso da sabulu sannan ki hadani da d’an arxiki ya maidani gida kar kasheni a hanya” Umma dai bata ce komai ba, Maimoon ta fito tare da Safiyya suka gaidata, Hajja tace “Allah maku albarka, ya baku ilimi me amfani” Jiddah dai tuni ta koma ta ci gaba da karatunta a dining, Ba a dau lkci ba Abuturrab ya shigo parlon kansa a kasa, Ya
karaso ciki ya gaida Umma da ladabi tace “Saboda ka isa yasa ka xo gidan nan ka xauna mota baka shigo gaisheni ba?” Ya ki kallonta a ido, yana kame kame yace “Aa waya nake yi a motar dama xan shigo Umma” Hajja tace “Karya yake algungumi har cewa yayi minti biyar ya bani wllh, ni dai ki hadani da me hankali ya maidani gidan d’a na don Aliyu abun tsoro ne, babu uwar da na hada dashi balle ya cuceni, gashi uwar tayi ta xuba masa ido kamar tana tsoronsa bata fada masa gaskiya, ita kuma yar Benuen can tayi kane kane a kan lamarinsa, ai ni ina ganin iftila’i tunda ja sauka gidan Usman, abubuwa suke babu tsari kamar dai gantalallu” Abuturrab dai sai kallonta yake ta gefen ido, Umma tace “Toh ka kyauta, from henceforth i don’t want to see ur legs in my house again, get out” Bai ce mata komai ba ya juya ya nufi kofa ya fita, Jiddah ta bi sa da kallo, Hajja ta ajiye jakanta ta cire mayafinta ta linke ta ajiye, ta gyara xama tace “Dama
idan babu me mayar dani gida sai dai in kwana a nan kawai, baxan bi mutumin can ba abu ya lalace min” Maimoon ta fashe da dariya Hajja ta marairaice tace “Allah kuwa ke baki ga yanda ya wani fita kamar Zaki ba daga fadan gaskiya” Umma tace “Kiyi xamanki kawai a nan Hajja” Hajja tace “Toh a kai min kayana daki” Karfe tara da rabi Umma na dakinta tare da Jiddah dake gyara mata press din kayanta, Umma tayi dialing number yayarta, nan kuma ta sanar mata duk abinda Aliyu yayi mata daxu, Ummi
tace “Kiyi hakuri Ramlah, Ni yayi ma ba ke ba, kinsan wannan xancen auren da ya kirkiro ma kansa da Hafsah kawai suke sabgarsu, ban san komai a kai ba, uban ne ma yace min gobe xa su kai kudi, wllh bai ce min komai ba shi har yanxu” Umma tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Yaya ina ta ce maki a tashi tsaye kince Aa ba komai, wllh wannan abu ba lafiya a ciki, ga dai abu kiri kiri fa” Ummi tace “Aa ki kyalesu kawai, shi ba yaro bane
kuma sarai da hankalinsa, abinda kike tunani ba shi bane, shi dai ne ya xabar ma kansa haka, ai ba shi daya na haifa ba dai? Dama shi da namiji ai wasu kake haifa ma” Umma tace “Ki kyaleni da shi xan saita masa xama wllh” Sun jima sosai suna waya, Jiddah dai duk sai bata ji dadi a ranta ba, taji kuma a xuciyarta tana son yi ma Abuturrab magana, to amma a ina xata gansa??