JIDDAHTUL KHAIR 35

Ranan asabar kamar yanda Ummi ta sanar ma Umma aka kai kudin auren Aneesah, on that same day kuma aka saka ranan bikin wata biyu, Umma na xaune parlor da yamma Hajja ta shigo parlon ta rike ha6a tace “Ramlah kinji wai an sa bikin Aliyu nan da wata biyu, yanxu Usman ya kirani yake sanar min, sun kai komai saura sadaki” Umma tace “Toh Allah ya sanya alkhairi” Hajja tace “Atoh dai, mu iyakar abinda xa mu ce kenan, yaron da baya mutunta iyayensa….” Daga haka ta juya ta koma ciki, ita dai Umma bata ce komai ba. Abuturrab na xaune shi kadai a parlorn gidansa dake Abuja idonsa na kan screen din wayarsa da yake dannawa…. knocking din kofar parlon aka yi ya kalli hanyar kofar, amma bai yi wani yunkurin
tashi ya bude ba, aka sake knocking duk a tunaninsa Aneesah ce, wayar hannunsa ya fara vibrate ya ga Ahmad, yyi ta kallon wayar kafin ya daga ya kai kunne, Ahmad yace “Are visitors not welcome any longer?” Abuturrab yace “Nace maka ina nan ne?” Ahmad yace “Su kuma takalman da ka bari
bakin kofa fa?” Abuturrab bai ce komai ba ya katse wayar, bayan few seconds ya mike ya nufi kofar ya bude ya dawo cikin parlon, kallonsa kawai Ahmad yake don rabon da ya gansa an yi sati uku yanxu, ya kirasa severally baya responding, har ma ya daina kiransa, Ahmad ya karasa ya dau drugs da ya gani kan center table yana jujjuya su, lkci daya ya ajiyesu yace “Bai kamata ka dinga shan irin wa ennan magungunan saboda yanayin aikin ka, and why are u having sleepless night?” Abuturrab ya kallesa yace “Haka nace maka?” Ahmad yace “Aa haka dai drugs din yace min…” Abuturrab yace “Then you are mistaken, ka kara gaba can da karyar likitancin ka…” Murmushi Ahmad yyi yace “Toh Shikenan, amma da an canxa maka prescription din drugs din” Abuturrab yace “Wannan kuma likitan da ya fi ka yayi prescription din” Ahmad yace “Ohk then, kwana da yawa, i called severally baka responding ko nayi wani laifi ne” Abuturrab ya ki kallonsa, Ahmad yace “Shine dai yau sanin schedules dinka nace bari in karaso gidanka na nan inji laifin da nayi” Abuturrab yace “I just decided to live my life without hypocrite” Ahmad ya buda ido sosai yace “Hypocrite? Su waye hypocrite din?” Abuturrab yace “Decision dina kenan”
Ahmad yace “Kai ne babban hypocrite ai tunda har kana tunanin anyi wronging dinka amma ka kasa bude baki kayi magana ka dau gaba da mutane, balle ni dai nasan i did nothing to you” Abuturrab ya jefa masa wani kallo yace “You did nothing to me?” Ahmad yace “Of course, ba abinda na maka” Abuturrab yace “That’s ur cup of tea… To yanxu bayan munafurcin da ku ka je ku ka hada har aka sa na saki wancan yarinyar ko da akwai wani abu da ya ragu a rayuwata tun bayan wannan lkcn, akwai wani abu da nayi loosing?” Ahmad yace “Eh mana gashi har bacci kayi loosing, sbda duk wanda ke isasshen bacci babu abinda xai hadasa da wa en nan kwayoyin dake gabanka….” Kallonsa kawai Abuturrab ke yi babu ko kiftawa, Ahmad ya daga shoulder yace “And da bai dameka ba ko baka yi loosing komai ba babu abinda xai sa ka dinga isolating kanka daga cikin al’umma, but that’s not my problem now, my major problem is that daga yanda na ganka nasan you are down for now may be they took u unexpected, don haka take a break
from work, kada wataran muje mu ji labarin da ba shi kenan ba, shi Pilot banda nutsuwa da kwanciyar hankali ba a bukatar komai daga garesa, amma yanxu yanda kake a birkicen nan bai kamata ka dinga daga al’umma xuwa sararin samaniya ba, toh bayan wannan kuma ina son ka cire duk xargi a ranka, ka bar ganin ko da hadin bakina aka saka ka saki Jiddah, i know nothing about it… Kawai dai coincidentally nayi maka magana da kwana biyu sae kuma abinda ya faru ya faru, da ina da niyyar sanar ma kowa tun farkon auren xan sanar ae ba sai da aka dau lkci ba” Abuturrab yace “To ko kai ka fada ko ba kai ka fada ba ance maka abun damuna yyi ne? Banda ma wani burden da aka sauke min meye nayi loosing a lamarin nan, sae ma
peace of mind da freedom da na samu, plss close this chapter, ba shi da wani amfani a gareni” Ahmad yace “Ok then, i heard su Abba sun xo gidansu Aneesah yau” Abuturrab yace “You heard right!!” Ahmad yace “Toh Allah ya sanya alkhairi” Abuturrab bai tankasa ba ya mike ya shiga kitchen, Ahmad ya bi sa da kallo yana murmushi, Hmm is Abuturrab really sure he looses nothing living without Jiddah?” Har karfe sha biyu Ahmad na gidan
kasancewar bashi da night duty, ya tashi ya shiga bedroom yyi kwanciyarsa ya bar Abuturrab yana operating laptop. Karfe uku da yan mintuna Ahmad ya fito parlor ganin Abuturrab bai shigo ba, bai gansa a parlon ba har sannan kuma wutan parlon na kunne ga laptop dinsa ka a kunne, kitchen ya karasa nan ma bai gansa ba, ya fito ya duba sauran dakunan duk baya ciki, ganin kofar parlon da ba ayi jamming ba ya karasa ya bude kofar, xaune ya gansa balcony with his phone, da mamaki Ahmad yace “What are you doing here by this time?” Abuturrab yace “Zafi nake ji” Da mamaki Ahmad yace “Xafi kuma ga Ac ga fanka? Are you okay?” Abuturrab yace “To iskan waje nake so ba na Ac ba” Ahmad ya fi minti biyu tsaye yana kallonsa, Abuturrab bai kuma kallon inda yake ba, Ahmad yace “Ka sha drugs din
naka?” Abuturrab yace “Ae ba kai ka min prescribing ba balle ka tambayeni” Ahmad bai kuma ce masa komai ba don sae a sannan ya tuna cewar ya sha wajen karfe sha daya, juyawa yyi ya koma parlon ya xauna yana mamakin is Abuturrab okay?? Har kiran sallan farko Abuturrab na xaune balcony, Ahmad ya gaji da xama ya koma daki ya kwanta. Da asuba Ahmad ya fito da alwala parlon, dai dai sanda Abuturrab ma ya fito daga bathroom din parlon, shi dai Ahmad kallonsa kawai yake har ya fita don bai ga alamar ya kwanta ba, Abuturrab ya bi bayansa xuwa masallaci… Bayan an idar sun fito mosque din Ahmad na kallonsa yace “Karfe nawa xaka yi piloting yau?” Abuturrab yace “Karfe daya…” Ahmad yace “Okay…” Gidan ya shiga ya dau makullin motarsa ya fito ya ga Abuturrab xaune balcony
yace “Xan dawo before 7” Da ido Abuturrab ya bi sa har ya wuce. Kamar yanda ya fada karfe bakwai ya dawo gidan, xaune ya tadda Abuturrab a parlor ya jinginar da kansa jikin kujera, Ahmad ya xauna ya ajiye ledan hannunsa yace “Good morning” Abuturrab yace “Afternoon duty ka koma yanxu” Ahmad na bude ledan da ya ajiye yace “I think u are suffering from lack of sleep” Abuturrab ya dinga kallonsa yace “Wa ye xaka yi ma allura? Ni nace maka bani da lafiya ne??” Ahmad ya kallesa yace “Aa baka ce min ba, but this will help” Abuturrab ya gyara xama yace “You are wasting ur time, gwara ma kar kayi wasting alluranka, idan kuma ka hada sae ka nemi
wanda xaka yi ma” Ahmad bai tanka sa ba ya gama hada ruwan alluran, sannan yace “Kaga kar ka 6ata min lkci ka 6ata ma kanka lokaci Captain, how will a normal human being stay all through the night without sleeping, sannan anjima yaje ya daga jirgi with over 300 passengers or less??” Abuturrab yace “Wai kai nace maka banyi bacci bane, shkkn kuma mutum daga farkon dare har karshe sae yayi ta bacci?” Ahmad yace “Duk kwararren likita ya ganka yasan baka bacci bawan Allah, don haka idan xaka daina gardama ka daina….” Abuturrab yace “Ashe kai kwararren likita ne” Mikewa Ahmad yyi yace “You ur self will feel relieved after the injection….” It took anoda 15mins to convince Abuturrab sannan ya yarda Ahmad yyi masa alluran, in just less than 20mins ya kwanta nan kan doguwar kujera, Ahmad dake watching dinsa yace “Da dai ka tashi ka shiga ciki baccin xae fi maka ma’ana” Tashi Abuturrab yyi ya wuce bedroom