JIDDAHTUL KHAIR 36
Jiddah ta juya tana Kallonsa, ya shigo ya kulle kofar, tana ajiye plates din a plate Rack tace “Ina yini?” A takaice yace “Ki daina gaisheni idan kin gan ni, bana so” tace “Toh” Ta dau plate daya ta bude warmer ta debi abinci still bata kallesa ba tace “Ya jikin” Yace “Ke yanxu a xatonki da tunaninki ‘yancin kanki kika samu ko?” Sai a sannan ta juya ta kallesa suka hada ido, ya hade rai yace “Don kinga Maimoon na daukan mayafi karami ta saka ta fita titi kema sai kika fara saka mayafi karami, kin ma mance ke wacece koh” Shiru tayi bata ce komai ba ta kai hannu ta dau cokali, ya wani daure fuska yace “Kin saba saka mayafi daga can hayin rigasa ne, balle kuma gidana da kika xauna?? Kina tunanin ke da Maimoon daya ne?” Tace “To amma ai Umma ta gani bata ce komai, kaga da tace min in cire ai baxan sa ba” Yace “Toh daga yau ko nan da gate kada ki sake sa mayafi ki fita…” Da mamaki take kallonsa, can dai tace “Ko saboda me?” Yace “Saboda haka na fada” Bata kuma ce masa komai ba, yace “And yanxu
kina ganin kin fi kowa freedom shi yasa kike shiga motar maxa har da xama gaban mota ko, uban wa ya ce ki bi ta ku hau motar wani kato har kika shiga gaba, a can hayin rigasar ku haka kike yi” Tace “Kamawa tayi in hau shi yasa na hau ba wani abu ba, kuma ai an san sa a gida” Bude baki yayi yana kallonta, yace “Kin san mene?” Ita dai ta xuba masa ido, yace “Akwai wani wanda yayi dalilin dawowarki cikin gari a duk wa enda kike xaune da su yanxu cikin garin kaduna??” Kallonsa kawai ita dai take, yace “Toh dama ai nine na fito da ke cikin gari, don haka yanxu sai in mayar da ke in da na dauko ki, duk me son sake fitowa dake cikin gari sai ya koma hayin rigasa ya dauko ki na musamman… Kin fahimce ni??” Murmushi kawai tayi tace “Toh” yace “Ehh, ni na raboki da baabarku kuma ni xan maida ki” Tace “Yaushe xan shirya kenan?” yace “Sai kin shirya ashe, dama kin xo da wani abun ne ban sani ba?” Tace “To shikenan” Ya jefa mata wani irin kallo ya fice daga kitchen din ta bi sa da ido, hawaye taji ya kawo
idonta, ta rufe abincin ta fita ta koma daki ta kulle kofa ta kwanta saman gado tana iya kokarin ganin bata fashe da kukan dake cin ta ba… Har karfe uku Jiddah na kwance daki, Huraira ta xo ta kwankwasa kofar jin an sa makulli tana kiran sunanta, Jiddah ta mike da kyar ta isa gun kofar ta bude Huraira tace “Jiddah malamarki ta xo fa tun daxu…” Shiru tayi tana kallon idonta tace “Me ya faru Jiddah?” Ta girgixa mata kai tace “Kaina ke ciwo” Huraira tace “Subhanallah, to ki fito Umma na kiranki” Komawa tayi ta dau hularta ta sa sannan ta fito dakin, a hankali ta nufi parlor ganin Umma da Hajja a xaune, ta sunkuyar da kanta ta xauna a kasa tace “Umma gani” Umma tace “Amma dai nace ki daina barin malamanki na jiranki ke ya kamata ki dinga jiransu ko Jiddah, dole sai kinyi wani
bacci idan malamar safe ta tafi bayan kin san cewar dayar na kan hanya ita ma” Jiddah ta kasa dago kanta cikin sanyin murya tace “Kuyi hakuri Umma, ciwon kai nake” Sai a sannan Umma ta kalleta da kyau tace “Ciwon kai tun yaushe, shine kike kuka?” Ta girgixa ma Umma kai kawai, Umma tace “Toh kin ci abinci” Ta gyada mata kai kawai, Umma tace “Toh Allah ya sauke kije dakina akwai paracetamol kan bedside drawer ki dauka, amma xaki iya karatun kuwa yau?” Cikin sanyin murya tace “Xan iya Umma” Umma tace “Toh je ki dauka ki sha ki dau qur’anin ki ki fita, Allah ya sauwake” Mikewa Jiddah tayi ta wuce dakin Umma, Hajja tace “Mu dai ba gamu mun taho jinyan wancan mutumi da har yanxu tun wayewar gari ban daura ido a kansa ba” Umma tace “Na duba na gansa yana bacci daxu” Hajja tace “Ni wllh dama ki sa duk ya tattaro kayansa ya dawo gidan nan a rabosa da yar Benuen can, ko ya kika ga” Umma tayi wani murmushi tace “Ai baxai dawo ba, wnn ma nayi mamakin da ya yarda ya biyo mu, ina ga tunda yake bai ta6a kwana gidan nan ba ko da xai kai karfe sha biyun dare”
Hajja tace “To mu dai gamu ga Allah, amma Hauwa tayi sake ai, idan ta bar ta ta kwace miji sai ta yarda har d’anta ta kwace, nima fa don ban xauna a Masar bane a banxa shi yasa har yau bata rabani da Usman ba, kullum cikin tsayuwar dare nake, kyaga a rana sai ya kirani sau uku, to amma dai ba komai tunda Allah yayi min dawowa ba dai nace maki xan nuna nata nima yar banxa bace, Allah ya ba Aliyu lafiya mu koma gidan, na ma fasa komawa gidan Kabiru” Umma tace “Allah dai ya kyauta amma abun kam sai addu’a” Ahmad ne ya shigo parlon ya gaishesu, Umma tace “Ya jikin Ramlan” yace “Da sauki Alhmdlh” Hajja tace “Yaushe xaka sallami wancan mutumin mu koma gida in san ta ina zan fara da Hafsah?” Yace “Ai yace baya son drip din kuma, magunguna kawai yake sha” Tace “Atoh ya tarkata magungunan mu wuce gida kawai sai yayi ta sha a can” Duk suka kalli kofar Jiddah ta shigo parlon da sallama, Umma ta kalli agogo tace “Ciwon kan bai yi sauki ba
kenan” Gyada mata kai tayi, Hajja tace “To Malamar fa?” A hankali tace “Tace inje in kwanta, ta wuce” Ahmad dake kallonta yace “Tun yaushe kan ke maki ciwo?” jiddah tace “Daxu” Yace “Toh je ki kwanta, Allah ya sauwake” Tace “Ameen” Sannan ta wuce daki ta kwanta. Har kusan karfe shidda Jiddah na daki tana jin kanta na mata wani ciwo ba kadan ba, Umma ce xaune parlor tare da Abuturrab da fitowarsa parlon kenan, Umma tace “Ka bari gobe ka tafi” Ya kalleta amma bai ce komai ba, tace “Kuma ka bude kunnenka sosai ka saurareni” Still shi dai bai ce komai ba yana
kallonta, tace “Hafsah kanwar uwarka ce ko ta Ubanka?” Sunkuyar da kansa yayi, tace “Toh bari kaji Aliyu, wllh idan kana son ka dinga ganin dai dai a al’amuranka ka fita harkar matsiyaciyar nan ka kama uwarka…” Da mamaki yace “Me tayi kuma Umma?” Umma tace “Ni kake tambaya me tayi?” Yayi kasa da kai yace “Toh Umma naga dai lafiya suke xaune, kuma ita Aunty…” Umma tace “Tashi ka bani waje mara hankali kawai” Ya kalleta yace “Aa kiyi hakuri Umma” Cikin daga murya tace “Ka fini sanin lafiya suke xaune ko ba lafiya suke xaune bane?? tunda nake ban ta6a ganin d’an da ya hofintar da uwarsa ya dauketa ba komai ba yake bama Kishiyarta muhimmanci fiye da tunanin mutum kamar kai ba, anya kana son gamawa da duniya lafiya Aliyu?? Anya kana son ganin dai dai a rayuwar ka?? Uwa
fa??” Kasa ce mata komai yayi yana ta kallonta da mamaki, to me Ummi tace ya mata?? tace “Toh wllh rayuwarka na cikin tashin hankali da garari don ma kaji in gaya maka yanxu” A sanyaye yace “Umma da akwai wani abun da nake yi ne ni ban sani ba? Ko da akwai wani abun da tace na mata ne” Tace “Kaje ka xauna kayi karatun ta nutsu bani xaka yi ma nonsense question din nan ba” Bai kuma cewa komai ba maganganunta na yi masa yawo a kai, shi a iya saninsa babu abinda yake ma Ummi yana mata biyayya yanda d’a ke ma uwa, to what is Umma talking about” Sake daga kai yayi yana kallonta yaga irin kallon da take masa tana girgixa kafa, ya shafa kansa a hankali bai ce komai ba, can kuma dai yace “Toh Shikenan xan je in bata hakuri, duk da ni dai ban san me nayi ba” Bai jira me Umma xata ce ba ya mike ya wuce dinning don tun daxu abincinsa ke can, Umma ta bi sa da kallo tana furta Innalillahi wa inna ilaihi raji’un a ranta, lamarin Abuturrab anya lafiya kuwa?? Ahmad ne ya shigo parlon, Umma tace “Da wannan safa da marwan da kake a kan titi meyasa baxa ka dawo da Ramlah gidan nan ba Ahmad” Ya shafa kansa yace “Toh Umma” Umma tace “Kayi knocking ka