JIDDAHTUL KHAIR 36

ka duba Jiddah don Allah” Yace “Alright” Abuturrab ya bi sa da kallo har ya wuce, sai da ya fara knocking Jiddah ta taso ta bude kofar ganinsa ta koma gefe kanta a kasa tace “Ina yini” ya dinga kallonta yace “Wai ciwon kan kike ma kuka Jiddah?” Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, yace “Kin ci abinci” Tace “Na ci” yace “Jikin ki da xafi?” a hankali tace “Nima ban sani ba” Toh bari in siyo maki magani yanxu in dawo” Yana fadin haka ya juya ya koma parlor, yana kallon Umma yace “Umma let me get her drugs, har yanxu bata jin dadi” Umma ta mike ta tafi daki wajen Jiddah, Ahmad ya karasa gun Abuturrab yace “Kayi bacci sosai ai ko?” Yace “Yau nake son xan koma gida” Ahmad yace “Ohk toh, bari in dawo xan siyo ma
Jiddah magani she isn’t feeling fine” Daga haka ya dau makullin motarsa ya fita. Bayan magrib Jiddah na xaune parlor bayan ta sha drugs din da Ahmad ya siyo mata, tana cin shinkafa da miya da Maimoon ta kawo mata, a hankali take cin abincin don baya ranta, gaba daya ji tayi xuciyarta babu dadi, Safiyya da Maimoon na haddansu a daki, Hajja da Umma kuma na daki, ita kadai ce xaune parlon sai Huraira dake wanke wanke a kitchen, tun da ya shigo parlon ta kallesa sau daya bata sake kallonsa ba, ya karaso
tsakar parlon, ita dai taki yarda ta kallesa, looking at her directly yace “Don nace xan mayar da ke in da na dauko ki shine kika fara rashin lafiya, sabida baki da intention din sake komawa gidanku, ni ban ta6a ganin wanda ke gudun gidansu ba sai a kanki, ai xamanki a can xai fiye maki xama gidan mutane….” Ta daga kai ta kallesa tace “Toh sai ka mayar dani ai yanxu, ni bana tsoron komawa gida… Saboda nasan Allah na tare da ni, ko kaji nace maka baxan koma ba?” Yace “Toh sai ki tashi ki dauko hijab din naki yanxu” Mikewa tayi ta wuce daki, shi ma ya tafi dakin Ahmad ya dau makullin motarsa, Ahmad na kallonsa da mamaki yace “Ba Umma tace ka bari gobe ba” Ba tare da ya kallesa ba yace “Ehh ba nisa xanyi
ba, i want to get something” Bai jira cewar Ahmad ba ya nufi kofa ya fita, Jiddah na daukan Hijab dinta dake linke Maimoon ta kai karshen ayan da take karantawa, tana kallonta tace “Ina xaki?” Jiddah taki kallonta balle taga hawayen dake makale idonta tace “Xan amso abu wajen Maman Abdallah ne” Daga haka ta fita dakin, yana tsaye bakin kofar parlor alamar ita yake jira, ta nufi kofar, muryar Hajja suka ji tana cewa “Ke ina kuma xaki da daddaren nan bayan nace ki min linke uwar rikon ki ta daure maki kugu wai baki da lafiya?” Jiddah ta kasa juyowa, Abuturrab na ganin Hajja ya fita parlon ya tsaya balcony, Ahmad ne ya shigo parlon shi ma yana kallon Jiddah yace “Where are you going to Jiddah?” Still bata juyo ba hawaye na sauka idonta tana gogewa da hannunta, ya karasa ya
tsaya gabanta yana kallonta, buda ido yyi sosai ganin kuka take, yace “Me ya faru Jiddah” Hajja ma ta karaso tana kallonta tace “To ko dai tana da mutanen boye ne Ahmad?” Ahmad dai bai ce komai ba sai kallon Jiddah yake, Hajja tace “Aa ba ruwana bari in kira Ramlah kar abu ya lalace mana” Tana fadin haka ta tafi da sauri, Ahmad yayi kasa da murya yace “Gaya min me ya faru Jiddah, kuma ina xa ki?” Ta kasa cewa komai sai hawaye, Hajja ta dawo tare da Umma, Umma tace “Jiddah” Juyowa Jiddah tayi da jajayen idonta tana kallonta, Umma ta karasa kusa da ita tace “Me ya faru?? Kukan me kike, an maki wani abu ne” Shigowa parlon Abuturrab yyi xai wuce daki, Jiddah na kallonsa tana share idonta a hankali tace “Ce min yayi xai maidani inda ya dauko ni tunda shi ne ya kawoni dama ba wani ba” Gaba
daya duk suka juya suna kallon Abuturrab da yaki kallonsu kuma yaki tsayawa, cikin tsawa Umma tace “Dakata a nan Aliyu” Ba musu ya tsaya amma bai juyo ba, Hajja ta marairaice tace “Wannan wani irin Bala’i ne Usman ya haifo Ramlah?” Umma ta kalli Jiddah fuska a daure tace “Gaya min abubuwan da ya fada maki” Cikin rawar murya Jiddah tace “Kawai haka nan yace, wai duk me son daukoni sai ya je ya dauko ni idan ya maidani hayi” Umma tace “Yanxu Hijabin da kika sa hayin xai kai ki?” Jiddah ta gyada mata kai, Hajja tace “Amma daga d’an iska sai Aliyun nan wllh, Muna ta tausayinsa ba shi da lafiya ashe dabanci xai xo yayi mana a nan ni Dijeee, anya kana son gamawa da duniya lafiya kuwa d’an nan, ashe haka kake Aliyu” Cikin dakewa Umma tace “Aliyu!!” sai a sannan ya juyo ya kalleta tace “Xan baka takarda kayi list din duk abinda ka kashe ma
Jiddah tun daga lkcn da ka fara saninta har xuwa lkcn da ka rabu da ita, idan ma kudin sun fi karfina xan kai ma Abbanka ya bada su, sannan after that wallahil azeem ka sake kallon inda Jiddah take, i mean ka sake kallan min ita wllh sai ka sha mamakina a duniyar nan, xan maka tijara Aliyu, babu kai babu Jiddaha har abada, idan kuma kai ka cika d’an halaq ka dauketa ka mayar da ita hayin kaga, sannan maxa ka kama hanya ka koma gidanku kada ka sake xuwa min gida, idan kuwa kayi gigin xuwa sai nayi maka walakancin da baka ta6a xato ba” Hajja tayi mitsi mitsi da ido tace “Algungumi kawai, ana ta tausayinsa ba shi da lafiya ashe shi abinda xai kawosa nan gidan daban, to wllh har abada kai da wannan baiwar Allahn don ta ma fiye min kai sau dubu yanxu tunda bata ta6a xagina ba balle
manyanta, kai kuwa idan aka ce xa a kirga adadin xagin da ka min ai sai da a tafi kotu don xuciya xai iya dibana inki yafe maka, to meye kuma xaka sa yar mutane a gaba bayan an raba ku, ko dai har yanxu sonta kake bamu da labari? Banda tsautsayi ma da ya fada mata me xata yi da d’an banxa irin ka?” Umma da taji xuciyarta na tafarfasa tace “Wato shi yasa dama babu musu ka yarda ka biyomu don ka ci mata xarafi da mutunci, to wllh kayi na farko kayi na karshe, Jiddah da kake gani tafi karfin walakancinka yanxu tunda ba kai ke ciyar da ita ba, wanda kayi a baya ma duk nace kayi list a biyaka” Hajja tace “Ko ni sai in dage gidana daya in siyar a biyaka wllh” Sai a snn ya kalli Hajja yace “Saboda nace maki don ke nayi da xaki biyani” Da karfi Hajja tace “Huuuuu ka dai ji kunya duk ka xubda ladanka, gantalalle kawai” Ta gefen ido ya kalli Jiddah dake
share hawayen da yaki tsaya mata, shi dai Ahmad ya ma rasa abun cewa sai kallon Abuturrab yake da mamaki, kofa Abuturrab ya nufa ba tare da ya kallesu ba kamar xai tashi sama, Hajja ta dafe kirji tace “Mu ka xaga ka fita Aliyu?? Mu??” Ko kallonta bai yi ba har ya fice gaba daya, da karfi Hajja tace “Wawa kawai me xuciyar Hafsah, da kyar idan matar nan bata faki idon Hauwa kana jariri ta dura maka nononta ba, don babu halinta da ka xubar al-qur’an” Umma na kallon Jiddah tace “Daga yau ko gidan uban wa kika hadu da shi kika sake kallon inda yake balle ki gaishesa ko wata magana ta hadaki da shi sai na sa6a maki, babu ke babu shi har abada, a
duk inda xa ku hadu kuwa….” Hajja tace “Dama kina ganinsa ki gudu kiyi ta kanki, ko kuma ki fasa ihu kawai idan wani taimakon ne a kai maki da gaggawa, ni ai nafi kowa sanin halinsa tunda a hannuna aka haifesa, sau nawa idan an bata masa rai yake take kaza ya kasheta har lahira a lkcn ma yana d’an mitsitsi…. Yanxu ai sai dai ya take d’an mutum” Jiddah dai kanta na kasa, Hajja tace “Kuma tun ban tafi Masar ba ya xama d’an daba fa, fada ne kawai banyi ba kar uban ya kullaceni nayi tafiyata bakina alekum, wa ya sani irin mugun abun da ake koya masu idan sun daga jirgi sama, shi sa har yau ban yarda na hau jirgin da yake ja ba wllh ko don yanda ya tsaneni ma ba sai ya sake jirgin da gangan duk mu hantsulo kasa ba” tana fadin haka ta nemi waje ta xauna tana fifita saboda xufan da ta hada don bala’i, Umma na kallon Jiddah tace “Dauka abincinki ki wuce