JIDDAHTUL KHAIR 36

daki” Jiddah ta karasa a hankali ta dau abincin ta wuce daki, Hajja tace “Ni wllh don baxa ku yarda bane amma da kun bani yarinyar nan kawai in tafi da ita” Umma tace “Sai dai taje maki hutu” daga haka ta bar parlon. Jiddah ta maida hankali sosai a karatunta babu wasa, wanda hakan yasa Umma ke kara jin sonta a rai domin kwazonta ya wuce misali, both Islamic da western din duk she’s flowing well, kusan duk bayan kwana biyu Yousuf ke xuwa gidan da daddare, kuma duk idan ya xo ba wai wani hira suke da Jiddah ba iyaka ya sake guiding dinta a karatun nata shi ma, yawanci kuma turanci yake nace mata ta koya, kuma babu laifi she is really catching up, duk weekend Ahmad ke shigowa kaduna sbda duba Ramlah dake laulayi,
shi ma kuma yana assisting din Jiddah a bangarori da dama na karatunta. Umma na parlor ranan wata asabar Jiddah ta fito rike da wayarta dake ring ta karaso ta mika mata, Umma ta amsa tana duba me kiran nata, Ganin Ummi ke kira ta daga, bayan sun gaisa Ummi tace “Toh sun gama hada lefensu wai sai ki xo ki gani gobe xa a tafi da shi” Umma tace “Kai ba lallai ba yaya, Allah ya sanya alkhairi kawai” Ummi tace “Aa da dai ki daure ki xo din Ramlah xai fi” Umma ta d’an yi shiru kafin tace “Allah da kawai kin bari su tafi da shi goben Yaya, ai ba sai na gani ba” Ummi tace “Toh ni kuma nace ki xo ki gani” Umma ta d’an yi shiru sai kuma tace “Toh shkkn, bari ruwan ya tsagaita xan sa driver ya kawo ni ko da yamma ne” Ummi tace “Allah ya kai mu” ajiye wayar tayi ta ci gaba da kallon da take a Tv. Da yamma kamar yanda Umma tace ta shirya wajen karfe biyar ta fito parlor
tana kallonsu Maimoon da basu je Islamiyya ba sbda ruwan da aka yi, tace “Xa ku je can gidan ne ganin lefe?” Maimoon ta mike da sauri tace “Eh Umma dama ina tsoron gaya maki ne” Umma tace “Toh sai ku shirya ni ina ruwana kuma da xan hana ku” Maimoon da Safiyya suka mike gaba daya, ganin Jiddah bata motsa ba Umma tace “Ke baxa ki ba Jiddah?” jiddah ta girgixa kai tace “Aa xanyi assignment dina Umma” Umma tace “Ai ba dadewa xa muyi ba, tunda babu kowa gidan kawai ki shirya mu je yanxu xa mu dawo, idan muka tafi ma babu ke Hajja sai ta fassara mu tace ba a haka a Masar” Jiddah bata iya tace ma Umma komai ba, amma ba don ranta ya so ba ta mike ta wuce daki, Hijab ta saka suka fito parlon tare da su Maimoon……