JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDAHTUL KHAIR 38

Waya Abuturrab ya tadda Aunty na yi a parlonta rai bace, ko ba a fada ba yasan da wanda take wayar, yana dai tsaye har ta gama ta jefar da wayar kan kujera tana huci, ya kwantar da murya yace “Aunty duk bai kai wannan extent din ba, pls i want u to calm down….” A fusace tace “Ya kai har ya wuce extent din da kake fada, kuma wllh xan ga uban da xai fitar da kayan nan a gidan ga yau, sun san da nuna ikon me ya hanasu wahalan hada lefen? Tun da na fara hada kayan nan kullum sai na fita kamar yar iska, kuma bani xan shigo gidan nan ba sai karfe takwas din dare, to a kan me

ba a ce min Allah ya shi min albarka ba xa a dinga bata min rai ana sa ni a bakin duniya?? To wllh wllh Ramlatu ta fita harkata, ta fita idona in rufe idan kuwa ba haka ba xan kai kararta ba wani shege, ko kuma in kai ta gani ga ka ayi min iyaka da ita” Abuturrab dai kallonta kawai yake, wayarta ne ya fara ring ta dauka ta shige daki a fusace ta kulle kofar, Abuturrab ya shafa kansa sannan ya juya ya fita daga dakin, bangaren Umminsa ya shiga, ya kasa kallonta ya xauna saman kujera cikin sanyin murya yace “Ummi don Allah kiyi hakuri, duk bai kai haka ba” Ummi tace “Inyi hakuri da me??” Kasa cewa komai yayi, Ummi tace “Wllh in har

akwatunan nan suka kwana gidan nan sai dai ka nemi wata yarinyar da xaka aura ba wannan ba Aliyu” Umma dai na xaune tana danna wayarta tana girgixa kafa, Abuturrab bai kuma cewa komai ba ya mike ya fita parlon, a main parlor ya tadda Hajja tsaye bakin kofar parlon da su Maimoon, sai ga mai gadi ya fito daga dakinta rike da akwatuna biyu a hannunsa, Hajja ta basa hanya tace “Yanxu saura nawa?” Mai gadin yace “Saura hudu” Hajja tace “To yi maxa…” Mai gadin yayi kofar gida da akwatunan ya saka au booth din mota da driver din Umma ya bude sannan ya koma ciki da sauri, Hajja ta kalli Jiddah dake tsaye wajen balcony din tace “Toh ke wa kike da suna, ki kwashi kananun da ya ajiye a nan ki kai mota da tsayuwar nan, ki daina lagwai lagwai kamar ba mace ba kinji??” Jiddah bata ce komai ba sbda bata son mata musu ta dau kit din biyu ta nufi gate, Banda hararan Hajja babu abinda Abuturrab yake daga inda yake tsaye, can ya nufi kofar

kamar xai tashi sama, Hajja na ganin haka ta basa hanya da sauri, bayan ya fita ta kalli su Maimoon tace “Kun ga d’an banxan ko? Kunga irin dabancin nasa ko?? Da ban kauce ba bangajeni yayi niyyar yi fa, anya wannan Aliyun da na tafi Masar na bari kenan shekaru uku da suka wuce? o,o to baxan biyesa ba, ba ruwana ni ba yarinya bace, kuma sai dai ya bangaje Hauwa ko Usman, ko kuma yar Benuen can, amma ba ni ba tunda ban hada komai da shi ba ai” Jiddah na ajiye kits din bayan booth taki komawa cikin gidan tana tsaye jikin gate har ranta bata jin dadin abinda ke faruwa, Abuturrab ya fito compound din, kallon driver din Umma yayi yace

“Wa yace ka saka akwatunan a bayan mota?” Drivern ya xagayo da sauri yace “Aa kawai ni bude booth nayi ake xubasu a ciki” Calmly Abuturrab yace “Toh sauko da su” Kallonsa Jiddah ta dinga yi da mamaki, Driver ya koma gun booth da sauri xai sauke kayan, kafin driver ya fara sauke kayan ta daure tana kallon Abuturrab tace “Ina son in maka wata tambaya don Allah…” Sai a sannan ya kalleta, tace “To ka d’an ce masa ya jira kafin ya sauke kayan, kaji?” Driver ya kalli Abuturrab din dake ta kallon

Jiddah da mamaki, Ta koma gefensa tana kallonsa, kana ganinta kasan she is afraid of talking to him, gathering many courage ta fara magana tana wasa da fingers dinta “Dama ina son in san wacece Baabarka a cikin Aunty da Ummi, ni har yanxu ban sani ba” Daga sama har kasa ya kalleta, ta ci gaba da magana ba tare da ta yarda sun hada ido da shi ba tace “In dai Aunty ce Baabarka to kayi dai dai idan kace a sauke akwatunan nan, tunda ai ba a wasa da maganan uwa, idan kuma Ummi ce Baabarka….” Sai kuma tayi shiru, yana kallonta da kyau yace “Ina jin ki” Cikin sanyin murya

tace “Kaga ni ban samu gatan sanin mahaifiyata ba, na taso cikin maraicinta, saboda maraici da rashinta yasa na taso cikin rashin gata da kula…” Hawaye ya kawo idonta tana gogewa tace “Da mahaifiyata na nan duk abubuwan da suka faru dani da nasan baxa su faru ba, ko yan uwanta ni ban samu daman sani ba, bansan ko tana da yayyi ko kanni ba, ban ma ta6a ganinta ba” Ta kasa ci gaba tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, shi dai kallonta kawai yake, cikin sanyin murya tace “Toh kaga duk wanda baya ba Baabarsa muhimmanci baxai ji dadin rayuwarsa ba, kuma xai hadu da fushin Allah” Sai kuma ta daga kai ta kallesa tace “Albarkacin haifanka da Ummi tayi kaji maganarta na yau kawai mana, tunda tace bata son a bar kaya a nan ka bari a tafi da su xai fi, ko kai baka son ka xauna lafiya da matar da xaka aura?” Hajja ce ta fito gate din gidan tana yafa

gyalenta da yar jakarta a hannu tace “Ina matukin motar yake mu tafi” Drivern Umma ya xagayo da sauri yace “Gani Hajiya” Tace “A ina xan xauna a motar?” Bayan motar ya bude mata ta shige ba tare da ta kalli su Abuturrab ba tana cewa “Bari in fara yin gaba da kayan” tana shiga ta kulle motar, Drivern dake ta kallon Abuturrab yana jiran wani instruction din jin bai ce komai ba ya xaga ya shiga motar ya tada suka bar layin… Jiddah ta daga kai ta kallesa ganin kallonta yake ta sunkuyar da kanta gabanta na faduwa, ya gyara tsayuwarsa yace “Ohk, shikenan kin gama?” Shiru tayi da farko, sai kuma ta girgixa masa kai a hankali tace “Aa, yanxu don Allah kaje ka ce Ummi tayi hakuri ta yafe maka, sai kace mata Hajja kuma ta riga ta tafi da kaya” Yace “Koh?” Ta d’an kallesa, sai kuma ta sauke kanta ta gyada masa kai, yace “Ohk, kalleni” Kin yarda ta kallesa tayi, yace “Kalleni nace” Ta dake ta dago kai ta kallesa yace

“Toh daga yau… Kika sake sako min baki a abinda ya shafi rayuwata sai na mareki, ke har xaki gaya min abinda xanyi da wanda baxan yi ba? ” Jiddah dai bata ce komai ba, kawai ta juya ta nufi gate ya bi ta da kallon mamaki yace “Kee” ko waigowa bata yi ba, yace “Ba magana nake maki ba” Tayi shigewarta gate, shafa kansa yayi sai kuma ya bi bayanta. Parlor ya tadda ta xaune tare da su Maimoon, bai kalleta ba ya wuce bangaren Ummi, har sannan Ummi na xaune da Umma dake ta bata hakuri, kansa a kasa ya xauna kan rug din parlon, da kyar yace “Ummi don Allah kiyi hakuri ki yafe min, in sha Allah duk yanda kika ce xa ayi hakan xa ayi, kaya kuma

na sa Hajja ta tafi da su can gidan Umma” Dama bai sa ran Ummi xata basa amsa ba, hakan yasa ya kalli Umma ita ma yace “Ku yi hakuri Umma, in sha Allah hakan baxai sake faruwa ba, duk yanda ku ka ce haka xa ayi, kaya kuma duk ranan da ku kace a kai sai a kai, kuyi hakuri don Allah” Yana kai wa nan ya mike ya nufi kofa duk suka bi sa da kallo, ba Ummi ba har Umma tayi mamaki sosai ba kadan ba, abinda bai ta6a yi ba kenan duk rayuwarsa karkari ya je ya ba stepmom din tasa hakuri ya bar gidan sai kuma randa aka gansa, Ummi tace “Wannan ba xuwan kansa bane…” Umma tace “Aa nima nayi mamaki, ko Hajja ce dai…” Ummi ta kalleta da sauri tace “Wacce Hajjar? Shi dai ya san what he is up to shiyasa ya shigo bada

hakuri, amma this is so unusual of him, ni bai ma ta6a bani hakuri ba” Umma ta sauke ajiyar xuciya tace “Toh koma dai menene tunda ya shigo kuma yace ayi hakuri, sannan yace Hajja ta tafi da kaya kawai kiyi hakuri yaya” Ummi dai bata ce komai ba. Abuturrab na fita Bedroom dinsa ya shiga ya sa makulli, wayarsa dake hannunsa ya fara ring ganin Abba ke kiransa ya daga, Abba yace “Kana ji na Aliyu?” Abuturrab ya xauna gefen gado yace “Ina ji Abba” Abba yace “Plss ka lallaba iyayenka duk yanda xa ayi kar a fitar da kayan nan daga gidan nan… It should remain their gobe a kai su” Abuturrab ya shafa kansa yace “Abba Hajja ae ta tafi da su” Abba yace

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button