JIDDAHTUL KHAIR 38

“Ta tafi da su?? Amma baka yi making ko wani effort na hana tafiya da su ba Aliyu??” Yyi kasa da murya yace “Abba Ummi ta dau lamarin da girma ne, tayi fushi sosai, and….” Abba ya katsesa yace “And what nonsense? Ita kuma Hafsah fa? Ni nasan yawancin abubuwan dake faruwa gidan nan duk Ramlah ke xuwa ta hada, a kan me su basu hada lefe ba kuma su 6ata ma warce ta hada rai kana kallo Aliyu??” Shi dai Abuturrab yyi shiru, Abba ya katse wayarsa, kallon wayar Abuturrab ya dinga yi sae kawai yaji bai ji dadin abinda Abba ya fada ba har ransa, can ya mike ya koma parlon Ummi….. Hauka ne kawai Aunty bata yi ba bayan Aisha ta kai mata rahotun ai har an fitar da akwatuna xuwa gidan Umma, ta fito parlor tana kai koma
inda take shiga ba nan take fita ba, xage xage ta dinga yi kamar yar maguzawa, su Maimoon da Jiddah dai na xaune parlorn, Umma da Ummi duk na jin ta, Abuturrab dake parlon Umminsa yace “Umma muje in ajiye ku gida yanxu tunda driver din bai dawo ba” Umma ta ki tashi, Sanin at anytime Umma na iya tanka Aunty yasa Ummi tace “Ramlah dare nayi ku tafi a ajiye ku a gida” Umma ta mike ta dau wayarta tace “Sai mun yi waya yaya” daga haka ta fita Abuturrab na biye da ita bayan ya ciro makullin motarsa a aljihu, Umma bata ko kalli Aunty ba tana kai xuciyarta nesa tace ma su Jiddah su taso su tafi, daga haka ta fita parlon, Mikewa Jiddah tayi ta xaga xata wuce ta bayan Aunty dake tsaye tsakar parlon dab da ita tana
kumfar baki, Aunty na ganin haka ta fixgota a fusace ta sauke mata lafiyayyen mari tace “Don uwarki ta bayana xaki bi ki wuce duk ga hanya a gidan sbda ni sa’ar uwarki ce fitsararriya?? An aiko ki wajena ne xaki bi ta bayana, to koma wa ya aikoki ki koma kice masa na fi karfin sa, baki gan ni ba, kaji min dai yarinya xaki xaga ta bayana duk ga hanya a parlo??” Bude baki Abuturrab yyi ya tsaya yana kallon Aunty, Jiddah ta kasa motsawa tana dafe da kuncinta ta rufe ido, hakan ya kara tunxura Aunty ta fincikota tana jan kunnenta tace “Ooo rashin kunya xaki min?” Karasowa Abuturrab yyi parlon cikin annoyance yace “This is mean of u
Aunty, me ta maki xaki mareta haka? Who does that? Akan me xaki mareta a fuska, what offense did she commit?” Sake baki Aunty tayi tana kallonsa, can tace “Ni kake tambaya me yasa na mareta Aliyu?” Ko kallonta bai yi ba ya kalli Jiddah dake shessheka yace “Fita….” Taki motsawa hawaye na xuba idonta ya Fixgo hannunta ya nufi kofa, Aunty ta bi sa da kallo baki bude, sae bayan da suka fito balcony ya sake hannunta ta nufi gate tana goge idonta, Umma na tsaye jikin motar Abuturrab dake waje tana jiransa,
har suka isa gidan Umma babu wanda yace komai a motar, Abuturrab yyi parking kofar gida Umma ta bude motar ta sauka, ta nufi gate Abuturrab ya bi ta da kallo, Safiyya dake gaban motar ta sauka, Maimoon ce karshen sauka a motar, yana kallon Jiddah kafin ta wuce yace “Dawo ki rufe min
motata da kyau” Dawowa tayi ta bude motar ta sake rufewa sannan tayi wucewarta ciki. Washegari lahadi da yamma Jiddah na xaune balcony tare da Yousuf hannunta rike da Literature da ya sa ta karanta masa, mota ce ta shigo compound din, tunda ta kalli motar sau daya ta ci gaba da karatun da take Yousuf na kallonta, Ummi ta fara saukowa motar sannan Abuturrab ya sauka, suka nufo entrance din gidan a tare, tun basu kai balcony din ba Abuturrab ke kallonsu, Da ladabi Yousuf ya gaida Ummi ta tsaya Balcony din ta amsa da fara’arta, Abuturrab bai ko kallesa ba ya shige parlon, Jiddah ta gaida Ummi sannan ta mike ta amshi ledan hannunta, Ummi tace
“Ki xauna kiyi karatun ki Jiddah… Don’t worry my dear” Jiddah tace “Bari in kai ciki Ummi” Daga haka ta amshi ledan ta shiga parlon Ummi ta bi bayanta, dakin Umma ta nufa tare da Ummi, bayan ta ajiye ledan ta fito parlor, satan kallon Abuturrab tayi taga idonsa na kan TV, sai ta kasa wucewa bata gaishesa ba, hakan yasa ta d’an tsaya tace “Ina yini” Bai ko kalli direction dinta ba balle ya amsa fuskarsa daure, tayi wucewarta waje, tana dawowa balcony din ta dau literature din da ta ajiye sannan ta xauna Yousuf na kallonta, murmushi tayi tana duba page din da take, sai ga Abuturrab ya fito, ya nufi motarsa ya shiga yayi horn mai gadi na bude masa gate ya fice daga gidan, Yousuf ya kalli Jiddah yace “Is he alright?” D’an murmushi tayi tace “Nima ban dai sani ba” Yousuf yace “Naga baki gaishesa ba” Tace “Aa na gaishesa a parlor” Yousuf yace “Go on
with ur reading” ba musu ta ci gaba da karatun yana kallonta. Aunty ce kwance kan gadon sister dinta godiya, Aunty ta mike xaune tace “Ni fa duk abubuwan da aka yi a gidan nan bai dameni ba don Alhaji ya tsaya min kuma ya dawo yayi ta bani hakuri wllh, ita ma Hauwan taga bacin ransa wllh kuma komai ya xo da sauki tunda uwarsa ba gidan ta kwana ba, abinda ya dameni shine yanda har yanxu Aliyu ya ki ce min komai a kan lamarin, tun da ya shigo sau daya ina waya da Abban nasa a daren har yau da nake maki magana bai sake ce min komai ba, ko a waya kuwa, abinda bai ta6a min ba,
bayan xuwa ya bani hakuri sai ya sake kirana ya ban hakuri sannan ya tura min text kuma to wannan karan wllh duk babu” Godiya tace “Kuma yana gidan?” Aunty tace “Jiya Monday dai ya koma bakin aiki da safe, kuma ko baya gidan ma ai yana kirana a waya, to ni duk ba wannan ba, abinda ya bani shock shine yanda yake querying dina a kan dalilin marin talakan nan da ya je ya kwaso mana a hayi….” Godiya tace “Wai ba kince an gama case dinta ba har ma ya saketa? To me kuma ya hadasa da ita” Aunty tace “Toh ai har yanxu tana gun kanwar uwarsa, ta amsheta wai xata riketa har sun
sa ta a karatu” Godiya tace “Toh sai ya maki magana don kin mareta ko ko?” Aunty tace “Wllh kuwa Kyauta, cikin bacin rai ya gaggaya min magana wai a kan me xan mareta sannan ya kada keyarsa ya fita, ni tsabar shock ma ban samu bakin ce masa komai ba” Godiya tace “Aa to da akwai lauje cikin nadi a wannan batun naki, me yasa xai ji haushi har yyi magana don kin mareta” Aunty dai bata ce komai ba ta ta6e baki abun na sake dawo mata ranta na k’una, Godiya tace “Toh ko dai bai saketa din bane dai Hafsah” Aunty tace “Haba dai ga takarda ubansa ya sa ya rubuta kowa ya
gani, kowa ya shaida babu wani aure tsakaninsu, kawai toxarta ni yake da niyyar yi dama, amma ba komai in dai ni ce ya xuba ido” Godiya tace “Gaskiya kam, to yanxu ranan juma’ahn da munafukar kanwar Hauwan xa ku je kai kayan??” Aunty tace “Aa Alhaji yace in bar masu kawai suje su kai kayan ba sai naje ba, kuma ina ga da wannan takadiriyar tsohuwar xa a,
kinga gwara ai inyi xamana, abu dai namu, ta wani bangaren fa uwa nake a gun amaryar, iyaka kawai ki shirya ki bi su don ki kwaso min rahotu” Godiya tace “Aa gwara kam kiyi xamanki ni inje, don na lura da take takensu so suke wani abu ya billo daga bangarenki a sa yaron ya fasa auren Aneesar tunda ai an san uwar Aneesar aminiyarki ce” Aunty tace “Yauwaaa ashe kin gano godiya, haka suke so ni kuma ba shashasha bace duk xan bi su a nutse ayi auren, shi sa kika ga na fara ja baya, ayi komai a gama su ga ko xasu sake iko da Aliyu kuma a rayuwar nan, ba uwarsa ba,
wllh har ubansa sai ya nuna baya yinsa, balle wata kanwar uwarsa can, don tun farko ma shi bai dauketa mutum ba, su da Aliyu kuma sai dai hange daga nisa al-qur’an” Godiya tace “Shkkn kuwa Hafsah” Aunty ta d’an yi dariya tace “Allah dai ya kai mu lokacin lafiya, ai ni yanxu ido xan xuba ma kowa in ta binsu a samu a daura auren cikin aminci Aneesah ta tare” Godiya tace “Amma fa hankalina bai kwanta da xaman wannan yar hayin ba tsakaninku, tunda kinga dole dai Ramlah xata dinga xuwa da ita wajen yayarta…” Aunty tace “Toh sai me idan tana tahowa da ita, shi fa Aliyu bayan auren nan ko gidan ba xuwa xai dinga yi ba, tsaf xan masa iyaka da gidan wllh, kawai dai idan ina bukatar wani abu in shirya in tafi gidansa amma shi da gidan nan sai hange daga nesa..” Godiya tace “To da kyau hakan, Allah ya nuna mana auren nan lafiya” Aunty tace “Ameen, satu biyu kamar gobe ne ai in sha Allah” Godiya tace “Haka ne, bari in dubo mana