JIDDAHTUL KHAIR 38

girkin ko ya nuna” Daga haka ta mike ta fita dakin. Ranan Juma’ah Umma da frnds din Ummi biyu sai wasu yan uwan Abba da Godiya suka tafi kai lefen Aneesah garin Abuja, Hajja ta so xuwa amma Abba ya hanata don kar ya kullaceta ya sa ta hakura kawai suka tafi, sai ta 6ige da cewa su Jiddah ai ita ba yarinya bace dama da xa aje kai lefe da ita, banda ma an rainata ai bai kamata ayi mata xancen kai lefe ba tunda dai ita ba yarinya bace, iyayen Aneesah sun amshi su Umma da mutunci ganin uban kaya na gani na fada da aka yo ma yar su, ga zobunan gwal manya har biyu a ciki, Godiya dai na ta kwashe rahotun kai ma Aunty, aka yi komai cikin mutunci da girmama juna sannan su Umma suka juyo xuwa Kaduna…..
Abuturrab na kwance dakin hotel dake cikin garin Lagos idonsa a lumshe kafin lkcn da xa su yi piloting jirgi xuwa kano yayi wayarsa dake gefensa ya fara ring, ya bude idanuwansa ya dau wayar ganin Aneesah ce ya daga ya kai kunne yayi shiru, cikin wani salo tace “Mijinaaa” Calmly yace “Ya aka yi?” Ta lumshe ido tace “I love you my Captain… Ina sonka fiye da yanda kake xato a ranka, I can’t wait in ga na mallakeka a matsayin mijina” Shi dai sauraronta kawai yake, ta kanainaiye murya tace “I can’t wait a daura in 2 weeks time, I can’t wait to be ur wife officially My captain” Yace “Amma kin san wajen aiki nake Aneesah, i tot it’s something serious u
want to say” Tace “Ban gane something serious ba, wannan da nake gaya maka ba something serious bane?” Yace “Amma ba da rana ina wajen aiki ba” Tace “Ohk haka xaka ce min captain?” Yace “Ohk, i love you, idan na sauka kano xan kiraki…” Katse wayar yayi ya sa flight mode yayi rub da ciki ya lumshe ido.