JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDAHTUL KHAIR 39

Shirye shirye kawai ake babu kama kafar yaro a gidansu Abuturrab kasancewar kwana uku kacal ya rage daurin aurensa da Aneesah, kai kana ganin wannan shirin da ake kasan ba karamin biki xa ayi ba na first child of the family, tuni Umma ta dawo gidan da yan matan ta har da Huraira mai aikinta, yan uwa da abokan arxiki kuwa duk sun fara tahowa daga garurruka daban daban, Kamar yanda Aunty ta sanar ma yar uwarta godiya haka tayi a wannan period din, don sosai ta kwantar da kanta komai sai dai taje ta samu Umma taji yanda xa ayi, duk kuma yanda aka ce bata musu, har hakan ya ba Umma mamaki hatta idan wani shawara tayi da Abba sai taje ta

tattago Umma ta xo taji ko shawaran yayi, ganin haka Umma ta sake gaba daya don da farko ko sakar mata fuska ta ki yi, ashe hakan ba karamin kona ma Hajja dake ta lura da su rai yake ba, ranan laraba wanda ya rage saura kwana biyu daurin aure Umma ta shigo dakin Hajja rike da babban cooler din soyayyan nama xata ajiye Hajja tace “Meye haka?? Aa ba ruwana da tarkace Ramlah, fita da shi gaskiya ki kai dakin Hafsah tunda naga dai ku ke aurar da yaro ke da ita” Umma ta tsaya tana kallonta, Hajja ta ci gaba da kakka6e gadonta fuska daure tace “Haka kawai kya shigo min da wani katon rubabben cooler daki kamar wata rubabbiyar tsohuwa, a ina xan

sa shi? Kinga da ruwana da sha’anin bikin ku ne, ba dai kawai nasan ni na haifi uban Aliyun ba” Umma ta juya ta fita da naman, Hajja ta bi ta da wani shegen kallo tace “Idan ba gulma ba sai ki kama Hafsah ki rike hannu bibbiyu kuna abu gaban kanku bakwa sako kowa, in dai Hafsah ce ni nasan tana da wani mugun kudurin a ranta ne… Ahaf mu je dai xuwa, ni dai ba Allah ya so ‘ya ta na hanya gobe ba, duk ita xan sa kan komai na bikin nan ai tafi ku kusanci da Aliyun tunda kanwar ubansa ce ita, sannan matan

Kabiru duk suna hanya su ma gobe kwa sha mamaki ke da Hafsar, idan ma barbadensu na yan garin Benue tayi ta baki mu dai mun fi karfinta sai dai ke din da yayarki tunda naga ba a tsaye kuke ba” Tun da Jiddah suka xo gidan ko kallon inda take Aunty bata yi balle har tayi abinda xai sa ta 6ata likimon da tayi ma kowa, Jiddah ma bata yarda hanya ta hadasu, da ta ga Aunty a waje take barin wajen, duk Aunty na lura da hakan, sai dai tayi kwafa a hankali tayi murmushi, ita dai babban damuwarta yanxu a

daura auren nan ran friday Aneesah ta xama mallakin Abuturrab tukun, yawanci Jiddah na gun Hajja tun xuwansu, don Hajja bata sa kowa aiki sai ita, a dakinta ma take kwana, da taga bata ji motsinta ba xa ta sa a kira mata ita ko a nemota, sauran yan matan kuma dama ta ce babu abinda ya hadata da su sun ma rainata. Washegari Thursday da safe Jiddah da Nafisa kanwar Abuturrab da ke boarding suna sharan parlor kamar yanda Umma ta saka su, Maimoon kuma na goge goge aka bude kofar parlon, duk suka daga kai El-Basheer ne ya fara shigowa sannan Abuturrab dake biye da shi a baya, Jiddah dai ta ci gaba da sharan da take, Nafisa ta gaida El-Basheer cike da murnan ganinsa yace “Ashe kin girma da yawa Feenah” Rungume

Abuturrab tayi tace “Yaya sannunku da xuwa” Ya ja hancinta yace “Yaushe kika dawo” Tace “Tun ran Tuesday fa yaya” yace “To ya karatu?” Tace “Alhmdlh” Maimoon ta gaida El-Basheer ya amsa mata with smile, sannan ta gaida Abuturrab ya amsa a takaice, Jiddah ta dago tana kallonsu tace “Ina kwanan ku” El-Basheer yace “Lafiya lau, ya kike?” Tace “Lafiya lau” Dama Abuturrab bai amsa ba banda wayarsa da ya hau dannawa, Jiddah ta ci gaba da sharanta, kallon El-Basheer Abuturrab yayi ganin yanda yake kallon

Jiddar, ya maida wayarsa aljihu ya nufi dakin Hajja, El-Basheer ya kallesa sannan ya maida dubansa gun Jiddah yace “Are you Asthmatic?” Ta daga kai ta kallesa amma bata ce komai ba, Maimoon tace “Aa bata da Asthma” yace “Ohk” daga haka ya bi bayan Abuturrab xuwa dakin Hajja. Hajja na ganin El-Basheer tace “Kai ma kaje kayi ma kanka fada Bashir, ba wai ka dinga yawo kana bin sabbin angwaye xalo xalo a baya ba, da ka san ciwon kanka yanxu ba cewa xaka yi a hadaku da wannan mutumi Aliyu ba, balle duka duka da watanni nawa ya girmeka? Amma ka tsaya shashanci kai a dole d’an sarki, to ko ni da nake uwar sarki bana abinda kake yi wllh”

El-Basheer yace “Toh kin samar min matar ne nace maki bana so Hajja? Ni na xata Masar da kika je xaki samo min mata daga can fa” Ta marairaice tace “Wllh nayi niyya Bashir, Nafisah ce ta hanani wai su ba a haka a can, toh kaga kuwa ai sai inyi shiru in koma gefe tunda idan na botsare masu suka maido ni Najeriya sai inyi yaya, amma yanxu tunda har ka bani wuka da nama idan Allah ya yarda baxan baka kunya ba, yanxun ma na fara maka sha’awar wata yarinya wllh, baka ganta ba kyakkyawa doguwa jazur da ita kamar balarabiya, da ta bude min gashinta kuwa sai da na gigice, ga

ladabi da biyayya sannan bata da kiwiya, komai aka sata yi take cikin dadin rai ga shegen hakuri, ai ni tuni na fara maka sha’awarta sai gashi ashe kai ma ni kake jira” El-Basheer yace “Toh fah, a ina kika samo min ita Hajja” Hajja tace “Sakin wawa ce…” Abuturrab dake danna wayarsa ya daga kai ya kalli Hajja, El-Basheer yayi dariya yace “Sakin wawa kuma Hajja, bazawara kika samo min kenan?” Hajja tace “ka ji ka da wani xance Bashir, wllh babu wanda xai ce ta ta6a aure, yarinya ce fa yar karama bata wuce Nafisah kanwar mutumin nan dake xaune ba, kuma ai ni na samu labarin wannan auren da tayi ba aure bane don babu abinda ya ta6a shiga tsakaninta da mijin, a gantale aka yi auren kuma a gantale aka yi sakin,

yar yarinya ce karama fa nake gaya maka wllh, sannan kakan Aliyu nima ai a bazawarar ya aureni tunda sai da na auri kakanka aka haifi Kabiru da Aisha sannan kishiyoyi suka fiddani, Allah ya hadani da kakan Aliyu ya aureni sannan na haifi su Usman da Nafisah” Shi dai El-Basheer murmushi kawai yake yace “Toh shkkn ai ni nasan baxa ki min xabin da xai cutar da ni ba Hajjaju” Hajja tace “Haba haba ai na cuci kaina kenan idan na cuceka, in sha Allahu xabi ne har xabi na maka, kar ka ji komai a ranka, bari dai mu gama da bikin wannan mutumin tukun” Abuturrab dai bai daina kallon Hajja ba, El-Basheer yace “Toh baxa mu samu ko d’an ruwan shayi

ba, ni yunwa nake ji fa” Hajja tace “Kaji ka, ai magana xaka yi, har abincin ma akwai naga sun dafa idan kuna so a xubo maku” El-Basheer yace “Aa shayin dai, bamu yi breakfast ba” Hajja ta mike tace “Toh bari in sa a kawo maku” Fita tayi dakin xuwa parlor, har sannan su Jiddah na parlor, Hajja tace “Yar nan ajiye masu sharan su ki xo in sa ki aiki kinji” Jiddah ta ajiye broom din hannunta ta karaso gun Hajja, Hajja tace “Xuwa xaki yi kitchen ki wanke hannu da kyau, don baya son kazanta Bashir,

bayan kin wanke hannunki ki dau babban faranti da naga suke fafa da shi a gidan nan ki daura masa flask da cokali da kopi daya sannan ki ajiye kayan shayi a gefe, to shi kuma dayan mutumin ban san ko xai sha ba don ko gaisheni ma bai yi ba, amma dai baxa a biye ta halinsa ba, shi ma ki dora masa kofi da cokali daya mu mayar masa da aniyarsa, ki tabbatar duk ki dauraye kofunan don kinsan sarakan tsafta ne su, kuma duk a wajena suka gado, bayan nan idan akwai burodi ki daura kan tray din duk ki kawo masu” Jiddah tace “Toh” sannan ta juya ta wuce kitchen, Hajja ta koma daki tace “Toh ba shikenan ba bakina alekum, da wannan gantalallun ‘ya

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button