JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDAHTUL KHAIR 39

yan na saka sai in samu me xagina ma tunda ba isasshen tarbiya garesu ba” Jiddah tayi duk yanda Hajja ta ce mata, tray biyu tayi ta daura kayan shayin da bread din a daya, dayan kuma ta daura cups da spoon sai flask din a kai, na flask din da cup ta fara dauka ta fito kitchen din suka kusa cin karo da Aunty ta koma gefe da sauri, Aunty ta hade rai ta ja

gefe, Jiddah ta sunkuyar da kai ta bi gefe ta fita don tun sassafe ta gaisheta bata amsa mata ba, Jiddah na shiga dakin Hajja, Hajja ta mike ta shimfida rug da sauri tana cewa “Yauwa yar albarka, sannu kin ji, taho ki ajiye” Jiddah ta sunkuya ta ajiye tray din tace xanje in dauko dayan, Hajja tace “Toh yi maxa” Shi dai El-Basheer kallonta kawai yake, ta juya ta fita, Hajja tace “Wllh ba sawa ba hanawa, tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin nutsattsiya me tarbiya irin wannan yarinyar ba, gashi bata fushi ko kadan yanda ka san ni ce ina karama” El-Basheer yyi murmushi yana shafa kansa yace “Toh ko dai canje xaki min da sakin wawan da kika

ce” Hajja tace “Aa kai dai kayi shiru kawai ka kyaleni yanda ka gan ni, ban fiye son surutu ba gaira ba dalili ba….” Abuturrab kallon wayar hannunsa kawai yake amma babu abinda yake da wayar, Jiddah ta dawo da tray din kayan shayin ta ajiye, Hajja tace “Yauwa er albarka, sannu” Sai kuma ta kalli El-Basheer tace “Ko ta soya maka kwai, naga ta iya, jiya da uwar rikonta ta sa ta soya mata naga tayi sa da kyau snn bbu karni ga

albasa ta yankasa rimi rimi a kai abun zar sha’awa, ni dai har Ramlah ta gama cin kwan nan banji karni ba” El-Basheer yace “Aa ba sai na bata wahala ba ta bari kawai” Hajja tace “O’o Allah ina ruwanka da wannan batun, kai dai ba a soya maka kwai ba ka hada da burodi ka ci, da tana da son jikinta ai baxan ma fara sa ta ba, kaga na bi ta kan yaran gidan nan” Jiddah ta kalli El-Basheer tace “Xan iya” Yace “Toh je ki soya” kofa ta nufa ta fita, Hajja ta kalli El-Basheer murya can kasa tace “Ga tsafta

kamar tsatsonmu wllh, ko kai baka gani ba?” Shafa kansa kawai yake yana murmushi, tace “To ni dai ba ruwana, kawai a barni yanda aka gan ni ba banxa nake ba” Bayan kusan minti goma jiddah ta dawo da kwai rufe a plate da fork biyu a kai ta dora, ta sunkuya ta ajiye plate din kan carpet, Hajja tace “Allah yayi maki albarka kinji” Jiddah tayi murmushi ta mike suka hada ido da Abuturrab da ya dago kansa, sunkuyar da kai tayi ta nufi kofa ta fita, El-Basheer ya sauko ya fara hada shayin yana kallon

Abuturrab yace “Hey dude come let breakfast” Abuturrab ya mike yace “Alhmdlh” Daga haka ya nufi kofa ya fice. Da yamma Jiddah na dakin Hajja ita da Nafeesah, El-Basheer ya shigo da sallama yace “Hajja xa mu je dauko su Maman Farida” Hajja ta washe baki tace “Ehh wllh yanxu mijin ya kirani wai sun sauka ashe” yace “Toh dama xance maki sai gobe ne, don ni daga can baxan dawo ba” Hajja ta xare ido tace “Saboda mene?” Yace “Aliyu

xai karaso da su ni xan sauka gida in huta ne” Hajja tace “Aa ba ruwana ba haka Kabiru yace min ba, bai ce min xaka sauka a wani waje ba nan ba, nan din ba gidanku bane, sannan ba ga dakin Aliyu ba idan ma bak’in hali Aliyun ke maka ba ga dakin wancan yaron da ya gantale ba Salem yake kowa, ni tunda na xo har yau ban dora ido a kansa ba idan anyi magana sai uwar tace yana benue, tsafin suke koya masa a can din oho mu dai ga mu ga Allah, bikin d’an uwansa guda ma gashi babu alamar xai xo, ni dama a tsorace nake da yaron tun asali” El-Basheer yace “Toh xan dawo” Nafisah

tace “Yaya don Allah in bi ka?” Yace “Airport din?” Hajja tace “Ehh mana ku tafi da ita ai yar makaranta ce” El-Basheer yace “Toh idan da mijin Nafisan xamu dauko fa” Hajja tace “Toh ai mijin tun da muka dawo da shi bai koma ba, Nafisar ce kadai ta taho ko yaro daya bata xo da shi ba ta bar ma wata makociyarta balarabiya me kirki, mijinta kuma na Habuja” El-Basheer yace “Ohk” Nafisah na jin dadi ta dau mayafinta, Hajja tace “Toh gaskiya ni bana son kai, idan har xa aje dake sai dai a tafi da wannan yarinya Jiddah itama tunda tare kuke, ita ma kuma ba 6are bace” El-

Basheer yace “Toh ta dau mayafinta mu je” Nafisah tace “Amma Hajja kar ya Abuturrab ya koro mu fa” Hajja tace “Xai ko aika, ku mu je gun motar gaba daya” A tare suka fita, suka tadda Aliyu xaune cikin mota yana jiran El-Basheer, ganinsu gaba daya ya daure fuska, Hajja ta bude ma su Nafisah bayan mota, Ita dai Jiddah gabanta sai faduwa yake don mayafi ne ita ma jikinta, kallon mamaki Abuturrab ke masu gaba daya, can yace “Ina xa a kai wa ennnan?” Hajja tace “Usman ne yace a tafi da Nafisah su hadu da

takwararta a Iyapot, ni kuma nace a tafi da Jiddah tunda a kan kunnenta aka yi xancen kuma mu bama nuna banbanci a xuri’armu” Abuturrab yace “Aa ni baxanje da kowa ba sai dai El-Basheer yaje ya dauko Aunty Nafisar a Airport” Hajja tace “Amma kasan ina lura da yanda ka raina ubanka, shi fa ya fada bani ba, albarkacin daga bakinsa hakan ya fito ai sai kayi masa biyayya ko ba ta dadin rai ba kayi abinda yace, ba fa goyasu xaka yi ba balle kace aiki aka hadaka da, ko wacce xaunawa xata yi a bayan mota har

kuje ku dawo, gaskiya ka sake hali Aliyu, wllh Bashir ba haka yake ba kai dai bar shi da tsokana da mugunta, amma kai wllh kana da bakin hali” Abuturrab yace “Duk naji su sauka kawai” Hajja tace “Allah ya tsine min idan sun sauka, a kira min Usman” El-Basheer dake dariya kasa kasa bayan ya shiga front seat ya kalli Abuturrab yace “Plss let them, it’s Abba’s instruction” Dama Hajja ko sake kallon Abuturrab bata yi ba tana kallonsu Nafisah tace “Ku shiga kawai” Nafisah ta turo baki ta shiga motar tana kallon yayanta, Jiddah tace “Hajja ni ai kince xan wanke maki bandaki

ko?” Hajja tace “Aa wancan me fuskar uwar tata xata wanke min, wato Aisha” Jiddah ta girgixa kai tace “Hajja ni xan wanke kawai su tafi” A fusace Hajja tace “Oo Allah ya ana yabonki sallah sai ki kasa alwala, bayan nabi duk na barbada ma duniya cewar baki da musu kuma yanxu ki nemi karyatani gaban yaran nan??” Jiddah ta sunkuyar da kanta tace “Toh kiyi hakuri” Daga haka ta shiga motar, Hajja tace “Yauwa, ku je Allah ya

tsare, idan kinga yalo a hanya ki tuna masu idan sun ga dama sun siya min to” Daga nan ta kulle motar tayi wucewarta ciki tana cewa “Da ban masa haka ba koran min ‘ya yan xai yi, gwara ma yayi aure kowa ya huta wllh yaje can su ci kansu da matar ni dai xan dinga kai masu ziyara kawai da d’an rakiya” Tada motar Abuturrab yyi fuska daure ya danna horn mai gadi na bude motar ya fita compound din ya dau hanyar titi, ta madubi El-

Basheer ke kallon Jiddah da ya lura she is uncomfortable yace “How is ur studies going Jiddah?” Nafisah ta kalli Jiddah dake gefenta, Tana wasa da gyalenta tace “Alhmdlh” Ya dinga kallonta kafin yace “Hope u are assimilating what u are being taught?” Ta d’an yi murmushi tace “Ehh” ya langwabar da kai yace “Ni ai ba da Hausa na maki ba ko” sake kallonsa tayi suka hada ido, sai kuma tayi murmushi, yace “Do you have any idea of where we are heading to now?” Ta kalli Nafisah dake ta kallonta tana murmushi, Nafisah ta gyada mata kai alamar tayi magana, Shi dai El-Basheer na ta jiran respond dinta, ta d’an kallesa tace “Ka sake fadan

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button