JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDAHTUL KHAIR 39

abinda kace” Yace “Ohk.. Did u have any idea of where we are heading to now?” Ta d’an kalli Abuturrab da fuskarsa babu yabo bbu fallasa yana kallon titi yana driving, cikin sanyin murya tace “Yes i have” El-Basheer yace “So where are we going to now?” Tace “Hajja said we are going to take Aunty at the….” Sai kuma tayi shiru, ya gyada kai yace “Yess good, ci gaba” Tace “Airport?” Murmushi El-Basheer yayi sosai yace “Ohh yes, Hajja said we are going to pick Aunty Nafisa from the Airport” Ta sunkuyar da kai ita ma tana murmushi, Nafisah dai sai kallonta take, El-Basheer yace “So can you brief me about ur self?” Ta d’an yi shiru sai

kuma ta kallesa yace “I am all ears” Tace “My name is Hauwa Jiddah yusuf, i was born and brought up in kaduna hayin rigasa, i lived with my step mum not until…” Da sauri Abuturrab ya kauce ma mai mashin da ya kusa bugewa, Nafisah da taga yanda abun ya faru tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Da mamaki El-Basheer yace “How manage?” Abuturrab ya sauke glass ya ba ma mai mashin din hakuri ya ja motarsa ya kara gaba ba tare da ya tanka kowa ba, El-Basheer yace “Are u sure hankalinka na kan tukin nan Aliyu?” Abuturrab bai tanka sa ba still yana driving din, El-Basheer yace “Toh Allah ya tsare” Maida dubansa yayi kan Jiddah ta

madubin gaba yace “Go on Jiddah” tace “I am currently living with Umma at Unguwar Dosa…” Sai kuma tayi shiru, kallonta kawai El-Basheer yake, tayi murmushi tace “Shikenan” Yace “Yea, kinyi kokari sosai Jiddatul Khair, maa sha Allah” Ita ma murmushin tayi tana daga kai suka yi ido hudu da Abuturrab dake kallonta ta madubi, ta sunkuyar da kanta, Nafisah ma duk tana lura da kallon da yake ma Jiddah ta dinga fatan Allah ya sa kada yaje ya sake buge wani kuma. Aunty Nafisah ta rungume takwararta cike da murnan ganinta tace “Haka kika girma Nafisah” Nafisah dake ta washe baki tace “Aunty me yasa baki taho da su Farida ba?” Aunty Nafisah

tace “Suna makaranta ne amma in sha Allah xa su xo wani lokacin” Sai a sannan ta kalli Jiddah, Jiddah ta gaisheta da ladabi, Aunty Nafisa ta amsa da fara’a tana kallonsu El-Basheer tace “Wacece?” El-Basheer yace “Yarinyar Umma ce” Aunty Nafisa tace “To madallah” Tuni Abuturrab ya wuce da trolley dinta, duk suka bi bayansa xuwa mota, bayan ya saka jakan a booth ya shiga driver seat, Su ma suka shiga motar sannan ya bar airport din, hira kawai El-Basheer ke yi tare da Aunty Nafisah da ta fita harkan

Abuturrab ganin yanda ya tarbeta a airport, shi dai driving dinsa kawai yake, suna fara shigowa gari, Jiddah na kallonsa tunda ita ce setin kujeransa ta d’an matsa, El-Basheer ya kalleta ta gefen ido, a hankali tace “Yaya… Hajja tace a taho mata da Yalo wai” Abuturrab da ya ji ta sarai don setin ears dinsa tayi maganan yyi shiru yana driving dinsa, El-Basheer yace “Kina son wani abu ne Jiddah?” Ta kallesa tace “Aa Hajja ce tace a siyo mata yalo” El-Basheer yace “Ohk idan an gani sai a siya mata” Luckily suka samu yalon El-Basheer yace “Oga ka samu waje kayi parking a siya ma Hajja yalo” Abuturrab yace “Wa ennan rubabbun abubuwan” Daga haka

ya ja motarsa ya ki tsayawa, Aunty Nafisah dai bata ce masu komai ba, El-Basheer yayi wani murmushi shi ma bai ce komai ba, sai da suka kusa gida Abuturrab yace “Aunty ya baki taho da zee ba?” Tace “Ban sani ba” Murmushi kawai yayi ya shiga layinsu, a kofar gida yayi parking, El-Basheer ne ya fara sauka, Aunty Nafisah ta sauka, snn Nafisah, Jiddah xata sauka Abuturrab yace “Tsaya” kallonsa tayi, ya hade rai yace “Ke har wani nishadi kike kiyi ta hira da kattin maza kina washe baki don baki da kamun kai koh? To daga yau na sake jin kin wani bude baki kina ma wani

turanci xan baki mamaki, sannan ki ci gaba da yawo da kananun gyale” Ita dai kallonsa kawai take, yace “Saukar min a mota” bude motar tayi ta sauka ta wuce cikin gida ya bi ta da kallo…..

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button