JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDAHTUL KHAIR 40

compound suka hadu da Safiyya, Safiyya tace “Ke ina kika sa wayarki ya Aliyu na ta kiranki a kashe” Maimoon ta turo baki tace “Toh wai ma a ina ya samu numberta kuma me yake nemana xan masa?” Daga haka ta kara gaba su Jiddah na ta biye da ita, gud’a da ake ta yi a ciki ne ya tabbatar masu Amarya ta iso, don bayan daurin aure da awa uku aka kawota via flight tunda a kaduna xa ayi dinner din, Mutane ne cike gidan ba masaka tsinke, Maimoon tace “Mu tafi dakin Hajja kawai, kar ma a wani ya aikeni bayan nayi make up” a kulle suka ji kofar an sa makulli, wai ashe amarya na ciki, ga mutane cike bakin kofar dakin, Hajja ta bude kofar duk ta hada

xufa cikin ubansun lace din jikinta ga dankunnenta na gwal dake ta sheki a kunnenta, cike da masifa take cewa “Wallahi ba a haka a Masar, mu bama haka a masar, bamu san haka ba a Masar, ita fa wannan amaryar ba ta gwal bace kowa xai ganta idan lokaci yayi, an wani xo an cika min kofar daki kamar ina bada sadaka, ni wllh idan xuciya ta debeni sai in mayar da amaryar tsakar gida yanxun nan, wannan fitina har ina” Maimoon ta dinga rabawa ta gefenta xata shige dakin Hajja ta fincikota tace “Kun ga bala’i

ko, wacece wannan kuma” Maimoon tace “Hajja nice fa da su Jiddah don Allah ki bar mu mu shiga yanxu muka dawo” Hajja ta kankance ido tana kare ma Jiddah da Nafisah kallo tace “Shampoo aka ma fuskar ko me?” Maimoon ta shige ciki ta fixgo hannun Jiddah Nafisah ma ta shige dakin sai a sannan Hajja ta kulle kofar da makulli, Aneesah na can karshen dakin saman lallausan rug duk jikinta a lullube har fuskarta, daga gefenta kawayenta hudu ne, Hajja tace “Haba mutanen kasar nan kamar mayu ni Dijee, wllh har na yi adadin shekaruna a Masar ban taba ganin kwatankwancin haka ba,

komai a nutse cikin tsari ake yin sa, duk fa rubabbu yan kauye ne suka cika bakin kofar, wani me kudin ne xai wani xo ya tsaya bakin kofa ya tsaya yace sai ya ga amarya kamar wata amaryar gwal, ba gata can na ganta ba sai hasken fata kawai malam, kawayen nata kuma duk bakake ne, kwalliya su ma ni ban gane kanta ba, Ai da sun sani su bari idan sun xo nan sai ku kai su inda aka maku kwalliyan Maimuna, naku yayi kyau sosai har ma ba na jiddah ba, wani ba sai yace ita ce amaryar ba” Maimoon ta dinga kunshe dariyarta, Aunty Nafisah tayi tagumi tana salati a xuciyarta, Ta cikin mayafi Aneesah da ta hade rai take leko Hajja, kawayenta kuwa sai danna

waya suke ko wacce fuska a murtuke, Caraf idon Aneesah ya sauka kan Jiddah da ta durkusa jikin kujera, ita bata ma san ita ce jiddar da Hajja ke fadi ba don bata san sunanta ba, amma lkci daya ta gane ta, sosai gabanta ya fadi ta dinga kallonta, Aunty Nafisah ta dau wayarta dake ring ganin Aliyu ke kiranta ta daga, yayi kasa da murya yace “Aunty su Maimunan sun dawo?” Aunty tace “Ehh yanxu suka shigo” Yace “Toh ki turo min su gaba daya yanxu ina mota a kofar gida” Aunty tace “Toh” katse wayar tayi tana kallonsu Maimoon da cikinta ya kada jin ance eh sun dawo, Aunty tace “Wai ku je Aliyu na kiranku kofar gida” Aneesah dai sai binsu take da kallo ta cikin mayafinta, Maimoon ta mike kamar xata yi kuka,

Nafisah ma ta tashi suka nufi kofa, ganin Jiddah bata taso ba Maimoon tace “Aunty banda Jiddah yace ne?” Tace “Aa ya dai ce ku je ban san da wa da wa ba” Hajja dake ta fifita duk da fankan dake aiki a dakin tace “Toh me xa su masa har su uku haka, su dai su je, ina ruwansa da wata Jiddah da bata kula kowa a gidan, kilan wani laifin suka masa… Ita dai nasan ba ruwanta tayi xamanta su suje, bata shiga sabgar kowa” Maimoon tace “Laifi kuma Hajja, mu ba abinda muka masa wllh, ko ganinsa ma ban yi ba yau gaba daya” Daga haka ta fice daga dakin tare da Nafisah, ta cikin mutane suka dinga kutsawa har suka fita kofar gida, can suka hango

motarsa nesa da gidan, suka nufi motar, ya sauke glass yana kallonsu, suna isa motar Maimoon tace “Yaya ga mu, daxu wayana ya mutu ne sai da na dawo yanxu na jona a dakin Hajja” Yace “Ku nawa ku ka je make up din?” Maimoon tace “Ni da Nafisah da Jiddah” Yace “Ita tafi karfin ta fito ne?” Maimoon tace “Hajja ce ta hanata ta fito wllh” yace “To koma ki kira min ita kuma kar ki fada mata gaban Hajjan” Maimoon tace “Toh” daga haka ta

juya da Nafisah suka bar wajen tana sauke ajiyar xuciyar relieve, suna komawa dakin Hajja, Hajja tace “Kiran me yake maku?” Maimoon tace “Aa kawai dai tambaya yayi min” Tana fadin haka ta xauna kusa da Jiddah murya can kasa tace “Yaya Aliyu yace kije” Jidda ta xaro ido tace “Ni kuma?”

Maimoon ta cunkuleta tace “Don’t allow this old woman to know” Jiddah tayi kasa da murya tace “Tare xa mu je da ku?” Maimoon tace “Aa ni kaya xan sa yanxu, ya gama magana da mu, ke kadai xa ki je” Lkci daya jikin

Jiddah yayi sanyi, bata dai ce komai ba ta mike har xata dau gyalen da ta saka yau ta tuna sai yayi mata fada, Hijab din Nafisah dake kan kujeran Hajja ta dauka ta fita daga dakin, tana fita gate sae ga motar Ahmad tare da El-Basheer da wasu abokansu…..

Da babu dai gwara babu dadi ayi hakuri da ni yau, kun san mun haihu a group din mu jiya kuma duk da ni aka yi labor, Mrs Jay Allah ya raya baby Ameen????

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button