JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 31

Mîkyããj_Sããdy Beauty Soap

Hy my beautiful people ina gaisuwa????????♀️ku karka’de kunnuwanku da kyau ku ji????????ina mai sanar muku da cewa akwai gara6asa me kyau ta musamman ga wanda suka saba sayen sabulunmu da ma wanda zasu fara saya????, akwai ragin kaso 20% bisa dari 100% ga wanda suka saba saye, sannan akwai ragin 10% bisa ga masu sha’awar fara saye????, akwai farashi mai sauki ga ‘yan sari, me yapi wannan dadi kam????ki sayi guda 4 kanana a baki kyautar daya, ki sayi guda uku manya a baki kyautar karami daya, ki sayi bucket biyu a baki kyautar babban rubber daya???? kema da kike da burin saya ku’dinki bai kai ba????to ga naki, ki kawo customers uku ki karbi naki kyautar Sabulun????????

Kawata ‘yar ‘kwalisa me kike jira,ita mace fa kullum cikim yin ado da ‘kãwa take???? ya kamata ki yunkuro wajen ganin kin rabu da wannan kurajen da tabo tabon fuskan nan haka????, kinga kema sai a saka ki a layin masu ‘kwalisa da bajakolin ado????????????uwar gida a daure ayi gyaran jiki, sbd karbar goron a wajen me gida????,, ina amaren bayan sallah ku pito ku sayi naku Sabulun kuje kuyi ta wanaka hmmm ????kamshi kawai zaku yi tayi kaca kaca????????, laushin fata Baja baja????????????a yunkuro azo a karbi kayan gyaran jiki tare da sabulun gyaran fata a wurin Mîkyããj_Sããdy????

Duk wanda suka gwada Sabulun mu sun san babu ‘karanta a ciki????in dai fannin gyaran jiki ne to sabulunmu shine amsarku,, shi ke mai da fata ta zama babu Pimples, Acne, Spot, Stretch Mark, da Duk wata matsala da ta shafi fata,, akwai lightening, nd glowing????

In kina son jikinki yai su6ul da shi, fata tai santsi da sul6i, ki yi haske me aji, ‘kamshi kaca kaca ko ta Ina, ki ta fresh abunki hankali kwance ki zama Wankan madara yauqin zuma????????????Anty madam????To ki mallaki 3d (Extra Whitening Soap, Ko da kudinki sai da rabonki hajiyata)????????????????????????????????

Akwai hadin:
Mai da tsohuwa yarinya
Uwargida ta koma amarya
Amarya ta koma tamkar ‘yanmata
‘Yan mata su koma ‘yan dagwai²

Ga masu bu’kata sai su tuntu6emu ta kafar sadarwa kamar haka;
Call/WhatsApp:08061570778
IG@mik_yaaj_saady

Aunty ce ta shigo parlon Ummi duk da mutane da ke parlon ta ra6a xuwa cikin daki, Ummi na ciki tana bada sako, Aunty ta ja gefe ta jira har ta gama bada sakon sannan tace “Jiya kaina ya dau xafi kika xo kina tambayar Jiddah, to kin dai ganta ko?” Ummi tace “Mijinta ne ya dauketa” Still Aunty tayi tana kallon Ummi, trying to assimilate tace “Abuturrab din?” Ummi tace “Eh” Juyawa Aunty tayi ta fita daga dakin xuciyarta na tafarfasa, lallai Abuturrab ya gama rainata… Through out ranan da ya kasance mothers eve Jiddah na gida ita kadai, kuma ko a jikinta, sai yanxu ta gane xaman gidan da take ita kadai ma gata ne ashe, xamanta 24/7 a gida babban Rahama ne gareta, tun da Abuturrab ya ajiyeta ya tabbatar ta shiga ciki ya tafi bata sake ganinsa ba. Karfe shiddah saura na yamma bayan sun dawo daga babban event center din da suka yi booking against tomorrow’s dinner, su biyar ne a motar, wani abokinsu Umar ne ke driving motar, Abuturrab na kallon Umar kafin su isa hanyar da xai kai sa gidansa yace “Umar ka samu waje ka ajiye ni a restaurant din gaba…” Ahmad ya kallesa da sauri, kamar baxai ce komai ba, sai kuma yace “Me xaka yi a

restaurant bayan abincin da muka ci yanxu?” Abuturrab ya gyara xamansa babu yabo babu fallasa yace “Eh xan amshi abinci in wuce gida” Ahmad yace “Me xaka je kayi a gida?” Abuturrab yace “Kamar ya me xanyi a gida? Naga it’s almost magrib yanxu ko kana nufin saboda gobe daurin aurenka sai in bar gidana in kwana a wajenka?” Murmushi Ahmad yyi yace “Kai dai ka fadi gaskiya, dama Ummi ta shaida min abinda kayi masu, kawai dai baka son ka bar matarka ta kwana ita daya a gidan, shine xaka amsar mata abinci yanxu ka wuce gida” Abuturrab ya d’an yi shiru idonsa a kan titi yana sake comprehending abinda Ahmad ke ce masa, Umar yace “Ni kuwa yau sai naje gidan Captain naga matar nan tasa mun gaisa” Najeeb ma yace “Same with me… matar da har yau ba wanda ya santa” Da sauri Abuturrab yace “To ai tana gidan biki, sai dai idan can xa mu je” Dariya Ahmad yayi yace “Tana gida bata wani gidan biki, mu je kawai Umar ai nasan gidan” Lkci daya mood din Abuturrab ya canxa amma ya kasa cewa komai, Ahmad na nuna ma Umar hanyar gidan har suka isa, horn Umar yayi mai gadi ya bude gate di

n bayan ya hango Abuturrab da ya sha kunu cikin motar, Umar na parking Ahmad ya fara sauka, sannan Abuturrab, sauran frnds din nasu uku ma duk suka sauka, tafiya kawai Abuturrab ke yi xuwa entrance din gidan, Ahmad na leading din frnds din nasu yana cewa “Wannan ai ba adalci bane ba a sanar maku biki ba kuma a ki kawo ku gidan amarya” Har wani nishadi yake suna dariya da frnds din suna biye da Abuturrab, Abuturrab na shiga parlon ya dinga bin ko ina da kallo, kamshin girki ne ke tashi a parlon wanda ko ina fess alamar har goge goge tayi bayan dawowarta, kitchen ya nufa ya ganta tsaye kusa da gas, ga miya tana yi a gas din, daga sama har kasa yake kallonta, wanda riga da skirt ne na atamfa jikinta amma ba

ankon da ta saka da safe ba, har xai juya ya fita sai kuma ya sake juyawa yana kallonta babu yabo babu fallasa yace “Dama kar ki kuskura ki fito daga kitchen din nan” Bai jira cewarta ba ya fita parlor, su Ahmad na xaxxaune parlon har da kunna TV, Najeeb yace “Duk girkin amarya ne ya cika gidan nan haka, ashe yau xa mu kwashi girki” Ahmad ya hadiye dariyar da ke damunsa ganin fuskar Abuturrab, Abuturrab dai bai ce komai ba ya wuce sama, sai gashi ya sauko rike da folded hijab dinta ya wuce kitchen, mika mata yayi yace “Ki fito ki gaishesu, kuna gaisawa kuma ki wuce sama har su tafi kada ki kuskura ki sakko, saura kuma idan kin xo gaishesu ki xube kasa kamar kina neman gafara” amsan Hijab din tayi tace “Toh” ya juya ya fita, bayan ta saka hijab din ta bi bayansa, kanta a kasa har ta karaso cikin parlon, gaba dayansu kallonta suke, ta tsaya nan bayan

kujera, sai kuma ta kasa gaishesu a tsaye don bata saba ba, xagayowa tayi ta xauna saman lallausan carpet din ta gaishesu ba tare da ta kalli kowa a cikinsu ba, amsawa suka yi gaba daya Umar yace “Yau Allah yayi xa mu ga amaryar captain, ashe shi yasan me yasa bai ta6a gayyatomu mu ganta ba” Ita dai kanta na kasa, Abuturrab sai danna wayarsa yake bai ce masa komai ba, Ahmad yace “Toh a kawo mana ruwa matar captain” Kallonsa tayi jin muryarsa, ta d’an yi murmushi sannan ta mike ta nufi kitchen, tray ta dauka ta daura ruwan gora uku da glasses hudu sannan ta fito ta ajiye nan tsakiyar parlon, daga kai Abuturrab yyi ya kalleta ganin tayi abun hankali, he was thinking a hannu xata rike goran ruwan ta kawo, Najeeb yace “Toh ni kuma girkin amarya xan ci” Sosai gaban Abuturrab ya fadi, don ko shi bai ta6a cin abinda jiddah ta girka ba, har Ahmad sai da ya ji faduwar gaba, can dai yace “Bayan wanda muka ci yanxu?” Umar yace “Wanda muka ci daban, wannan kuma na amarya ne” Jiddah dai tayi shiru, Najeeb yace “Ko baxa a bamu ba amarya?” Mikewa tayi tana murmushi ta nufi

kitchen, Abuturrab ya kalli Najeeb yace “Yanxu fa ka ci abinci bawan Allah, sannan gwangwani daya ta dafa… ba daga kitchen din na fito ba yanxu, ai bata san xa ku xo ba” Dariya Najeeb yyi yace “Sai ta tsam mana a gwangwani dayan, duk wannan kamshin mu tafi bamu ci abincin amarya ba” Ahmad dai bai sake cewa komai ba, Abuturrab ya d’an saci kallon hanyar kitchen din, bai san lkcn da ya mike ya bi bayanta ba, plate ta dauka ta xuba shinkafar, tana tunanin ko a kai xata sa miyan, amma gidan umma taga waje daban ake sa miya idan an xuba ma baki abinci, hakan yasa ta dau wani bowl din me xurfi ta xuba miyan, tunda ta xo gidan bata ta6a girki da nama ba sai ranan, duk da ba wani girki ma take yi ba tun xuwanta, ganin Abuturrab ya shigo kitchen din ya kulle kofa ta juya da sauri tana kallonsa tace “a saman shinkafar xan xuba miyar?” Ya watsa mata wani

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button