JIDDATUL KHAIR 31

kallo yace “Ko kuma a sama kaina ba, ke har wani girki kika iya xaki wani xo ki xuba masu abinci maimakon kice babu kare, ni kike son ki kunyata gabansu?? Ko ruwan shayi ma baki bari ya tafasa ballantana ki iya girki me dadi” Kallonsa kawai take ko kiftawa babu, ya nufi tray din da ta daura shinkafa da miyar, ya dau spoon ya debi miyar kadan ya sa a gefen shinkafar ya juya, sannan ya debi shinkafar ya kai baki, ita dai kallonsa kawai take gabanta na faduwa, ya fi second biyar trying to figure out the taste of the food, sai ya ji girkin kamar na gidan Umma, ko don sbda spices din da tayi amfani da ne, wanda umma ta bada a kawo mata, sake dibar shinkafar yyi ya kai baki, da gefen idonsa ya bi kitchen din trying to be sure ba Umma bace ta aiko mata da abincin, bai ga warmer ko wani abu da xai nuna kawo abincin aka yi ba, ya sake diban shinkafar ya kai
baki, rungume hannunta tayi tace “Toh xaka cinye abincin ba a kai masu ba ai” cire spoon din yyi a baki da sauri, ya jefa mata wani kallo, ta koma baya ta turo baki, yace “Wa yayi girkin nan?” Bai san lkcn da yayi tambayar ba, sai yaji tambayar made him sound stupid, daukar tray din yyi ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, Najeeb ya sauke ajiyar xuciya yace “Ai har mun cire rai nace su tashi mu tafi kawai” Ahmad couldn’t hold it any longer, banda dariya babu abinda yake, Abuturrab ya ajiye masu abincin nan middle of carpet yace “Ae nace maku d’an kadan ta dafa, gashi nan tunda yunwa ku ke ji” Najeeb ne ya fara sauka sannan Umar, shi dai khaleel murmushi kawai yake, Ahmad ya mike ya isa gun abincin ya ci spoon daya gabansa na faduwa, exactly tunanin da Abuturrab yyi shi ma shi yyi, kamar daga gidansu aka kawo mata abincin, komawa yayi ya xauna yana murmushi yace “Nima na ci abincin amarya” Najeeb yace “Kafin ka ci na
taka amaryar kenan” Umar yace “Wllh u are missing Khaleel kaji dadin abincin nan kuwa” Tasowa Khaleel yyi shima ya ci spoon daya, sosai suka dinga yabon girkin, shi dai Abuturrab na xaune yana kallonsu, sai da suka cinye abincin duk da ba yunwa suke ji ba, sannan duk suka fita xuwa masallaci, Ahmad ne last din fita, kafin ya fita ya nufi Abuturrab yyi kasa da murya yace “Amma daga gidanmu aka kawo abincin nan ko?” Abuturrab yace “What did u mean?” Ahmad yace “Ba Jiddah bace ta girka” Abuturrab yace “Haka ta ce maka??” Juyawa Ahmad yyi ya bi bayansu Umar, Abuturrab ya mike ya dau tray din abincin ya wuce kitchen, har sannan jiddah na tsaye ta jingina da bango, ya ajiye tray din yana kallonta yace “Wa ya aiko maki da abincin nan?” Ta kallesa, a hankali tace “Abincin ya fi karfin ace ni na dafa ko??” Naxarin maganarta ya shiga yi, ta tattara plates da xata wanke a sink sannan ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita. Sake kallon pot din miyan yayi ya karasa ya bude sannan ya bude na shinkafar, rufewa yayi ya juya ya fita daga kitchen din xuwa masallaci. Ko da suka dawo mosque sun so Abuturrab ya kira jiddah suyi sallama da ita yace ai sallah take, haka nan ko wannensu ya basa kudi ya bata ladan girki, gefen kujera ya ajiye yace “Ta gode” sannan yayi masu rakiya har bakin mota yana kallon Ahmad yace “Xan shigo da safe in sha Allah” Ahmad ya hararesa yace “Kar ma ka shigo mana” a haka suka wuce a mota, Abuturrab ya juya ya koma cikin gidan, dubu sha biyar ne kudin da
ya kirga, bayan kusan minti ashirin ya mike ya wuce sama ya bude kofar dakinta, xaune ya ganta kan darduma, ya nufi gaban mirror dinta ya ajiye kudin yana kallonta ta madubin yace “Gashi nan sun baki, dubu sha biyar, amma ban mance turarena da kika fasa ranan ba” juyawa yyi yana kallonta da kyau yace “Kinsan nawa turaren da kika fasa?” Kallonsa kawai take, yace “Dubu arbain da bakwai kika fasa ranan, don haka xaki ajiye wannan dubu sha biyar din har ki samo dubu 32 ki cika min kudin turarena” Yana fadin haka ya bar kudin gaban madubi ya nufi kofa ta bi sa da kallo, can tace “Toh ka tafi da kudin” Ya juyo yace “Sai kin cika” daga haka ya fita dakin. Karfe tara jiddah na wanke wanke a kitchen ya shigo, bin kitchen din ya shiga yi da kallo, ita dai tunda ta kallesa sau daya ta ci gaba da wanke wankenta, kettle din dafa ruwa ya dauko ya bude fridge ya fiddo
goran ruwa daya ya xuba a kettle din sannan ya jona, satan kallonta yayi ganin hankalinta na kan wanke wanken da take, ya kai hannu a hankali ya bude murfin tukunyar shinkafar dake kan gas har lkcn, dai dai nan ta juya yayi saurin sakin murfin tukunyar, dauke kanta tayi ta ci gaba da abinda take, ya sosa kansa, sai kuma ya hade rai yace “Shi kuma sauran shinkafar wa kika bar ma??” Ta kallesa tace “Kai mana” ya kauda kai bayan few seconds yace “Na fara wasa da ke ko??” Bata ce komai ba ta dauraye hannunta bayan ta gama wanke wanken ta dau plate ta nufi gun tukunyar ta debi shinkafar duk da ta ci, ta ajiye pot din gun wanke wanke, ta bude miyar ta sa d’an dai dai da nama yanka uku sannan ta rufe sauran miyan ta dau wani plate me xurfi ta rufe shinkafar da shi ta dau spoon ta nufi kofa ya bi ta da kallon gefen ido har ta fita, shafa kansa yyi yana
tunanin wani eatry xai kira yyi ordering abinci da daddaren nan a kawo masa, shayi ya hada bayan ruwan ya tafasa sannan ya fita kitchen din, yana haurawa sama ya kalli kofar dakinta sannan ya wuce bangarensa, bude kofar parlon yayi ya shiga sannan ya kulle, still yyi yana kallon plate din dake ajiye kan center table, ya karasa ya ajiye shayin hannunsa sannan ya bude plate din yana kallon abincin, ajiye murfin yyi ya mike, can ya kalli kofa, sai kuma ya xauna, kamar me contemplating sai kuma ya dau spoon din ya fara cin abincin. Washegari karfe takwas da yan mintuna Abuturrab ya bar gidan xuwa gidansu Ahmad, Umma bata amsa gaisuwar da yake mata ba, ya shafa kansa ya wuce dakin Ahmad, Ahmad na ganinsa ya mike yace “Let’s talk” Kama hannunsa yyi ya fita suka tafi bangaren Abbansa, Abuturrab dai kallonsa kawai yake, Ahmad ya kulle kofar parlon yace “Me yasa ka dauke jiddah daga gidan su Ummi jiya?” Abuturrab ya hade rai yace “Gani nayi she isn’t comfortable, sannan Aunty duk ta bi ta takurata duk ba wanda yace komai, shkkn saboda ba matata bace ita sai in xuba ido a cuceta?” Ahmad yace “Har Ummi ma cutarta take kenan?”
Abuturrab ya shafa kansa ya xauna yace “Ni bance haka ba, wllh da kaga yanda na ganta shekaranjiya ko kai baxa ka bada shawaran in bar ta ba, ita Ummi bak’i sun mata yawa, babu abinda xata yi noticing, and Aunty sai aikenta take tana fita titi, what for?? I hate it when someone is being maltreated kai ma ka sani” Ahmad yace “Hmm, ka gano wani abu kuwa Abuturrab?” Abuturrab na kallonsa yace “Me kenan?” Ahmad yace “You are starting to develop feelings for Jiddah, na lura da hakan tun ba yanxu ba, wannan ya wuce tausayi da kwatar mata ‘yan ci, gashi kayi gaggawar rabuwa da ita, don babu aure tsakaninka da ita believe it or not, ko da kuwa baka saketa ba shelan da ka dinga yi kana sanar ma kowa cewar ka saketa, ta saku babu wani kwaskwarima… Babu wani aure tsakaninku ynxu Captain, sannan kar ka manta babu idda a kanta…” Katse sa Abuturrab yyi yace “Nigerians have a very very poor thinking mentality, me yasa baxa ku yi koyi da wasu kasashen da suka fi ku wayewa ba, Shikenan ba dama mutum ya nuna rashin jin dadin abun da ake yi ma mace sai ace yana sonta? Ohk fine… Yanxu in xuba ido ayi ta cutarta kenan tunda ba sonta nake ba,