JIDDATUL KHAIR 42
Jin yanda take kuka Abuturrab yayi kasa da murya still holding onto her yace “Gaya min abinda aka maki kike kuka….” Ganin ba amsa xata basa ba sai shessheka take, ya rufe idonsa ya bude cikin tsawa yace “Ya isa haka nan” kokarin kwatar kanta ta fara yi da karfi amma ta kasa… hakan yasa tayi lamo jikinsa tana kukan a hankali, gaba daya scent dinsa ya cikata, hannunsa taji a idonta ya goge mata hawayen sannan ya bude mota xai
shigar da ita ta fara turjewa, ya d’an hade rai yace “Baxa ki shiga ba??” turasa tayi da duk strength dinta bata ankara ba kawai taji ya dauketa kamar ya dau yar shekara biyar, ta hadiye kukan da take tana xaro ido tace “Na shiga uku, meye haka…” Cikin motar ya shigar da ita ya xaunar ta kamo hannunsa tana sake fashewa da kuka hankali tashe tace “Don girman Allah kayi hakuri kar ka sake kulleni a nan, ina hada ka da Allah kayi hakuri….” Ya daure fuska yace “To rufe min baki” Hadiye kukan tayi da
sauri ta rufe bakinta tana gyada masa kai, don har ranta take tsoron kada ya sake kulleta cikin motar, sai da ya ga tayi shiru snn ya shiga bayan motar shi ma ya kulle yana kallonta, ta sunkuyar da kanta yana kallon yanda kirjinta ke sama da kasa, yace “Yanxu tun daga gida kika taho a haka babu mayafi?” Ita dai bata ce komai ba xuciyarta na bugawa, a fusace yace “Tambayarki nake” Ta jawo jakarta a hankali tana nuna masa tace
“Yana ciki” Yace “Amma ke baki ji kunyan tahowa a hakan ba maxa na kallonki a hanya?” ita dai bata ce komai ba, gaba daya a tsorace take fatan ta kawai kar ya sake kulleta cikin mota yayi tafiyarsa, yace “Tambayarki nake…” ta marairaice tace “Ai a mota muka taho, ni ba wanda ya gan ni” Yace “Wa ya kawo ku a motar?” Tsoron ce masa Yousuf take bata san dalili ba, yace “Baxa ki bani amsa ba?” Ganin yanda take kallon kirjinsa ya sunkuyar da kansa yana kallo shi ma, da sauri ta dauke kanta, xaro ido yyi ganin yanda farin rigarsa ya bace da powder da janbaki, ya kalleta yace “Kinga abinda kika min ko??” Ta kallesa tayi narai narai da ido tace “Kayi hakuri” Ya d’an hade rai yace “Inyi hakuri? Sai in ce ma matata me idan ta gani?” Ta kallesa amma bata ce komai ba, handkerchief ya ciro aljihunsa ya mika mata yace “Maida min rigata yanda take” Tana kallon handkerchief din tace “Xai goge kuma?” Yace “Oho” karba tayi ta
fara goge shaddar a hankali, ya jinginar da kansa jikin motar yana kallonta babu ko kiftawa, ita dai taga sai kara bajewa powdern yake, bata san lkcn da wani dariya ya taho mata ba ta rufe bakinta da sauri ya dinga kallonta, ta marairaice tace “Allah baxai fita ba” Yace “Ba ruwana” Bata kuma cewa komai ba tana ta gurje wajen da handki din hannunta tana kuma jin yanda xuciyarsa ke bugawa, daga kai tayi a hankali suka hada ido, fuxgota yyi ta kusa fadawa jikinsa cikin husky voice dinsa yace “Daga yau kika sake fita da gyale xan sa6a maki, sannan karatu kike yi yanxu babu ruwanki da ko wani namiji ko waye shi” wayarsa ne ya fara vibrate a aljihunsa ya saketa ya ciro yana duba screen din wayar, lkci daya ya bude motar ya sauka ta bi sa da ido kafin ya rufe ta riko hannunsa da sauri cikin rawar murya tace “Don girman Allah kar ka sake kulleni” kulle motar yayi ya xaga ya bude driver seat ya shiga, sai a sannan taji hankalinta
ya kwanta… Har suka iso gida bai ce mata komai ba, can nesa da gate din gidansu yayi parking, kashe mota yyi ya juyo yana kallonta cikin duhun motar yace “Dama kar ki kuskura ki ambato ni idan aka tambayeki daga inda kike” ita dai bata ce komai ba sai kallonsa take, yace “Fito da mayafinki” A hankali ta bude zip din jakarta ta ciro mayafinta, yace “Sauka” Bude motar tayi ta sauka ya bi ta da kallo har ta isa gate ta shiga cikin gidan, Umma ce ke kokarin fitowa parlor da wata kawar Ummi da Aunty Nafisah, Umma na ganinta tace “Daga ina kike Jiddah?” Jiddah da gabanta ya fadi tace “Umma ni ban ga su Maimoon ba kuma baxan gane gida ba” Umma tace “Wa ya dawo da ke yanxu?” Jiddah ta sunkuyar da kanta tace
“Ya Aliyu” Da mamaki Umma tace “Aliyu?? A ina kika ga Aliyu kuma?” Cikin sanyin murya tace “Aa kawai nagansa ne ya koma can wajen shine muka hadu ya taho da ni gida” ita kanta Aunty Nafisah kallon mamaki take ma Jiddah, Umma dai ta juya bata ce komai ba ta koma ciki, Kawar Ummi ta bi bayanta, Aunty Nafisah tace “Toh shigo” A sanyaye Jiddah ta shiga parlon, babu
kowa parlon sai few guess da yaransu, Aunty Nafisah ta wuce dakin Hajja, ita kuma ta wuce dakin da ta san su Maimoon suke, Tana shiga dakin Maimoon ta mike da sauri tace “Jiddah ina kika je, ko wajen dinner ban ganki ba” Jiddah ta cire gyalen jikinta ta ajiye jakar hannunta tace “Toh ai baki nemeni ba” bandaki ta wuce don yin alwala… Washegari tun asuba aka tashi gidan aka fara girke girken breakfast, su Maimoon da su Jiddah kuma duk aka hadasu da gyaran gida, Safiyya da Nafisah parlorn gidan suke gyarawa, Tun da Jiddah taga sun gama gyaran part din Ummi xa su na Aunty taji hankalinta ya tashi, tana kallon Maimoon tace “Ko dai inje in dinga gyara dakin Hajja don mu yi sauri” Maimoon tace “Aa wllh muje mu gyara na
Aunty tare, Na hajjan ma muyi tare” Jiddah bata kuma cewa komai ba ta bi bayan Maimoon xuwa part din Aunty, yawanci duk yan uwan Aneesah ne a parlonta, Aneesah da kawayenta kuma na can bedroom dinta, Jiddah ta gaishe da manyan da ta gani a parlor suka wani amsa da kyar kamar dai sun santa, Maimoon dama bedroom ta wuce direct bata ko kallesu ba Jiddah ta bi bayanta, Aneesah da kawayenta suka daga kai suna kallonsu, Maimoon tace “Xa mu yi gyaran daki” wani kallo Aneesah tayi masu daga sama har kasa tace “Da mutane a ciki xa ku yi gyaran?” Maimoon tace “Atoh saka mu aka yi mu ma ai” Aneesah tace “Toh sai ku koma kuje kuce ma duk wanda ya aiko ku da akwai mutane a ciki” Jiddah dai bata ce komai ba tana tsaye, Maimoon ta wani ta6e baki tace “Toh mutane” Daga haka ta juya tayi ficewarta daga dakin, Jiddah suka hada ido da Aneesah da ta wani murtuke
fuska kamar ta ga mugun abu, juyawa Jiddah tayi ta fita daga dakin ita ma, kawar Aneesah Naja tace “Wai wacece wnn da tsohuwar can na jiya ta dage sai mai make up dinki ta mata make up, sannan sai in ga tana ta wani shan kamshi tana daga kai ko kanwar Captain din ce ita ma” Aneesah ta jefa mata wani kallo tace “Kanwar Captain? Tab… Amma kin so neman magana, wa ya bata matsayin kanwarsa? Ke baki ga yanda take dari dari ba kice wani daga kai da shan kamshi, ai karere ce ita a gidan Awara da doya fa take soyawa a hayin rigasa inda train station yake, cin arxiki fa take
kawai a gidan, ya talakawa ce nan ku ke gani mara galihu” Naja tace “Ke Aneesah, wllh na xata yar gidan ce yanda na ga an dage sai me kwalliyanki tayi mata” Aneesah ta ja wani dogon tsaki tace “Ni ki bar ma xancen raina baci yake wllh” Fauziyya tace “Toh Allah ya kyauta, nima dai ban xata karere bace a gidan, kuma na ganta fara kamar dai…” A fusace Aneesah tace “Don Allah ku bar xancen nan haka nan, nace maku yar Hayi ce, doya da dankali take siyarwa, kuma yar talakawa ce” tana fadin haka ta mike ta shige bandaki. Bayan azahar Jiddah ta fito sanye da Hijab dinta har kasa ta dalilin kiran da Yousuf yyi mata ta wayar Maimoon, yana tsaye jikin