JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 42

motarsa ta karasa gun motar da ladabi tace “Ina yini?” Yace “When did u leave the event center yesterday?” Tace “Ni ban duba agogo ba” Yace “Na kira Maimoon tace baku tare, where were u?” A hankali tace “Ba waje daya muka xauna ba” Yace “Toh wa ya dawo da ke gida” D’an murmushi tayi tace “Masu dawo da jama’a gida mana” Da ido suka bi motar da ya wuce su, motar yayi parking d’an gaba da nasu, Ahmad ne ya sauko sannan El-Basheer, Abuturrab ya bude back seat ya sauka shi ma, kallo daya yyi ma Jiddah ya nufi gate, El-Basheer ma ya bi bayansa, Ahmad ya karasa ya mika ma Yousuf hannu yana murmushi bayan sun gaisa yace “Ba mu ganka wajen Dinner dinmu

ba jiya” Yousuf yace “Yeah naje amma ban dade ba” Ahmad yace “To madallah” sallama suka yi Ahmad ya shiga gidan, Yousuf ya jingina da mota yace “Guys din gidan nan i think suna da karancin ilimin mu’amalah da mutane” Jiddah ta kallesa kawai tayi murmushi yace “Yahhh, that pilot… i don’t know but i wont call him an introvert, kawai dai bai san mutuncin d’an Adam bane, and i guess shi ma farin d’an uwansa ne ko?” Jiddah tace “Ehh” yace “Bird of the same feathers” Jiddah dai bata ce masa komai ba, Yousuf yace “Yaushe xaku koma gida da su Umma?” Jiddah tace “Kilan idan an kai amarya da yamma” Yace “Toh Allah ya kai mu, xa mu yi waya with

Maimoon’s phone” ta gyada masa kai kawai, yace “Take care Jiddah” Ta yi murmushi tace “Nagode” daga haka ya xaga xuwa driver seat ita kuma ta shiga cikin gidan, dakin Hajja ta nufa don dama aiki take mata Yousuf ya kira, tana shiga dakin Hajja dake xuba ma su Ahmad abinci ta daga kai tana kallonta tace “Toh wai saurayinki ne ya xo halan, naji shiru shiru” Jiddah ta nufi kayan da take linke mata don ta karasa, Hajja ta kalli Maimoon dake dakin tace “Halan dai saurayinta ne?” Maimoon tayi dariya tace “Ehh” Hajja tace “Atoh shi kuma baya gaida mutane ne, ai da sai ya shigo ya gaishemu yayi mana Allah ya sanya alkhairi haka ake yi” Jiddah ta ci gaba da linkinta, Hajja ta gama xuba abincin ta mike tace “Toh a kai masu can dakin, idan ba ni ba babu wanda xai masu haka, kowa na ta

kansa a gidan” Maimoon ta mike ba tare da ta tsaya gyara plates din abincin kai ba ta dau tray din sai ga plate daya ya rikito kasa, Hajja ta amshe tray din da sauri tace “Je ki Allah ya isa” Wani kallo Maimoon tayi mata tace “Toh na sani ne?” Hajja tace “Nace maki wani abu ne, cewa nayi kije ke da Allah kawai” Maimoon ta fice daga dakin kamar xata tashi sama, Hajja tace “Algunguma kawai, wllh da gangan ta kifar, dama bata yi niyyar xuwa ba, yar mummuna da ita kawai, uban me na hada da ita banda dai uwarta kanwar matar d’a na ne, gayyar tsiya kawai, da a Masar ne dama babu wani dangantaka tsakanina da ita nan ne dai komai sai anyi karere” Ita dai Jiddah linkinta kawai take, Hajja ta sake xuba wani shinkafar tana ta mita, har ta gama sannan ta kalli Jiddah tace “Ki dauka ke ki kai

masu, nima na so raina ya baci ne, banda haka ga ki, er arxiki irin albarka” Jiddah ta ajiye xanin hannunta ta karasa ta durkusa a hankali ta dau tray din ta nufi kofa, sai a sannan ta juya tace “A ina xan kai masu?” Hajja tace “Suna can parlon Usman” Jiddah ta fita dakin ta kama hanyar parlon Abba, sai da ta fara ajiye tray din ta murda kofar a hankali hade da sallama sannan ta dau tray din ta shiga ciki, waya na kare kunnen Abuturrab yana magana, El-Basheer kuma na xaune saman kujera idonsa a kan phone dinsa, karasawa ciki tayi ta ajiye tray din tana kallonsu tace “Ina yini” El-Basheer na kallonta da murmushi yace “How are u?” Tace “Lafiya lau” Daga haka ta mike ta nufi kofa El-Basheer yace “Who were u speaking with outside Jiddah” ta juyo tace “Yaya Yousuf ne” El-Basheer yace “Who is he?” Ta d’an yi shiru kafin tace “Family frnd din su Yaya Ahmad” El-Basheer bai kuma cewa komai ba, ta d’an kalli Abuturrab

taga yanda ya sha kunu, juyawa tayi ta fice daga parlon. Bayan la’asar aka fara shirye shiryen kai amarya, gidan cike yake dam da jama’a yan kai amarya, motoci sun fi ashirin a compound da kofar gida duk na yan kai amarya, wajen Hajja aka fara kai Aneesah dake sanye da alkyabba fuskarta a rufe, aka xaunar da ita saman carpet Hajja na daga xaune kan tabarma ta daura kafa daya kan daya, tana kallon Aneesah tace “Ni dai bani da abinda xance, amma da a Masar ne kawai ce maki xa ayi ki bi yan uwansa da

iyayensa sau da kafa, to sai ki ji dadin xama da shi, duk abinda yake so shine abun sonki…. Kinga dai shi me yan uwane barkatai kuma duk baxa su ki xuwa gidansa ba don haka kika iya allonki ki wanke, ko ni nan duk sanda na ga dama xanje gidansa tunda ni na haifi ubansa kuma a hannuna ya taso daga bisanni ya fita waje koyon tukin jirgin sama…” Aunty dake tsaye daga bakin kofa sai hararan Hajja take kamar ta kifa mata Mari, Aneesah dai sai satan mutanen dake dakin take da kallo duk da fuskarta a rufe yake, Jiddah ta gani xaune gefen gado rike da jakar da Hajja ta bata, ganin kallonta Jiddah ke ta yi ta wani tsuke fuska kamar tana ganinta, ita dai har ranta taji ta tsani jiddah, bata ta6a jin tsanar

mutum yanda take ma Jiddah ba, she just hate her with passion, Hajja ta gama surutanta mara tushe aka daga Aneesah dake ta kallon Jiddah har lkcn, aka fitar da ita daga dakin, next aka kai ta gun Ummi, Ummi ma tayi mata duk nasihar da ya kamata, Umma ta daura da nata, daga karshe aka kai ta gun Abba da Uncles din Abuturrab, sai wajen hudu da rabi aka kai amarya mota, Hajja ta saka ma kofarta makulli ta mika ma Jiddah tace “Jefa min a jaka sai Allah ya mana dawowa kuma, mu xa mu kai ta” Saurayin Safiyya ne ya tafi da su Maimoon da Jiddah da safiyyar sai Nafisah gidan Abuturrab, tun da yayi parking out side gate Jiddah ke kallon gidan, kamar bata ra6a rayuwa a gidan nan ba, kofar gidan cike yake da motocin kawo amarya, Maimoon da su Jiddah suka samu suka shiga compound din,

Jiddah dai na biye da su a baya har suka shiga parlon, taji gabanta ya fadi, komai na parlon an sauyasa xuwa sabo, jama’a ne cike parlon ana ta gud’a, Maimoon ta ja su Jiddah suka wuce sama, dakin da Jiddah ta xauna ta bude taga few mutane a ciki, kayan dakin ma duk an canza suka fito suka bude sauran dakunan da duk aka xuba ma furnitures, duk da Abuturrab ya sanar ma Aneesah ta gaya ma iyayenta ba a bangarensa xa a xuba mata furnitures din daki ba, taki sanar masu, can kuma suka kai kayan dakinta, Jiddah dai sai kallon parlon Abuturrab take, har sannan hotonsa na kayan pilot na parlon, ta rasa me yasa memory ke ta dawo mata, ba karamin kudi iyayen Aneesah suka kashe mata na kayan daki ba, don duk dakuna hudun dake gidan sun xuba kaya, can karshen gado ta xauna fuskarta a lullube

Jiddah dai kallo daya tayi mata ta fita daga dakin ta bar su Maimoon a can ta koma downstairs ta xauna a parlor tana bin ko ina da kallo. Sai kusan karfe shidda aka fara watsewa daga gidan amarya shi ma Hajja ce ta fara sallaman mutane su tafi kada a 6ata ma yarinya gida, gidan ya rage daga Umma, Aunty, Aunty Nafisah da frnds din Ummi, sai wasu family, Jiddah dai sai jiran lkcn da Hajja xata tafi ta bi ta take don taga alamar su Maimoon basu da niyyar tafiya don har Saurayin Safiyya ya wuce, tana ta xaune parlor har magrib hakan yasa ta mike ta shiga bandakin dake parlor tayi alwala ta fito tayi sallah, bayan ta idar ta tafi sama ta bude dakin da take tunanin su Maimoon ke ciki xaune ta gansu suna ta

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button