JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 42

hira, Tace “Wai baxa mu tafi gida bane?” Nafisah tace “Aa mu dai kila ma a nan xa mu kwana” Xaro ido Jiddah tayi, can tace “Toh ga jakar Hajja ni xan tafi” Maimoon tace “Toh wa xai maida ki gidan?” Jiddah tace “Akwai dari biyar din Umma a jakana xan yi amfani da shi” daga haka ta fita, xata sauko downstairs suka kusa cin karo da Aunty sake haurowa sama rike da abinci, sosai gabanta ya fadi ta koma gefe da sauri, Aunty ta kalli downstairs taga babu kowa parlon, fuska murtuke tace “Uban me kika taho yi gidan nan ke kuma?” Jiddah dai ta kasa cewa komai gabanta na faduwa,

Aunty tace “To don ubanki sauka ki kama hanyar ki, ke a wa xaki biyo yan kawo amarya, munafuka kawai mayya, nace ke a wa??” Jiddah ta fara sauka a sanyaye, hankadeta Aunty tayi har sai da ta kusa faduwa, cike da tsanarta tace “Maxa fita, ke da gidan nan ai sai dai hange daga nesa” Jiddah bata ce komai ba ta sauka da sauri ta nufi kofa ta fita compound din gaba daya, duk jikinta yayi sanyi, slowly take tafiya a dogon layin wanda ko

wani gida da fitilu farare da ya haska layin kamar rana, mota ne ya dallareta ta sunkuyar da kanta tana ci gaba da tafiya a hankali, reverse taga motar na yi yana komawa baya, ta kalli motar don bata ta6a ganin irinsa ba, lkci daya aka sauke glass din motar, ta dinga kallonsa, murmushi ya sakar mata yace “Hi….” Ta fara wasa da hijab din jikinta ta sake satan kallonsa, bude motar taga yyi ya sauka ya xagayo ta inda take yace “Assalamu alaikum” amsawa tayi a hankali, yace “Sorry na tsayar dake a layi ko?” Tace “Um” yace “Kin ganeni kuwa” ta sake kallonsa, d’an

murmushi kawai tayi bata ce komai ba, Yace “Ina xa ki da daddaren nan?” Tace “Gida” da mamaki yace “Ba can bane gidan ku dama” ta kalli gidan Abuturrab da yake nuna mata, sai kuma ta girgixa kai tace “Aa, gidan yayanmu ne” Ya wara manyan idanuwansa yace “Ohh, shi yasa na daina ganinki kenan” murmushi tayi masa nan ma, yace “Toh mu je in ajiye ki gidan naku ynxu” Tace “Aa ai ban sanka ba” Yace “Really? Duk sanin da kika min a balcony?” Murmushi tayi tana kallonsa, ya bude mata front seat yana kallonta, sauke idonta tayi ta shiga motar ya kulle sannan ya xaga ya shiga driver seat, reverse yayi suka bar layin yace “Ya sunanki?” A

hankali tace “Jiddah” As if counting his words yace “Jeedderh!!” Ta kallesa ya sakar mata murmushi wanda har sai da dimple dinsa ya lotsa ya kai fuskarsa dab da ita yace “I am Ali”

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button