JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 43

kallonta yace “Jiddah” kin dagowa tayi, ya dago kanta yace “Me aka maki?” Girgixa masa kai kawai tayi, yace “Aunty ko?” Nan ma ta girgixa masa kai kawai, Tsawa yayi mata yace “Baxa ki bude baki ki min magana ba” ta kuma rushe masa da kuka, ya kamo hannunta yana kallonta, sai kuma ya ciro handkerchief a aljihunsa ya mika mata yace “Clean of those tears…” Bata masa musu ba ta amsa amma bata goge idon ba, ya karbe a hannunta ya fara share mata idon yace “Me Auntyn ta maki?” Taki ce masa komai, bayan few seconds yyi kasa da murya yace “Kiyi hakuri” Kamar jiran jin hakan take ta hade kai da gwiwa ta fara sabon kuka, ya dagota ya hade rai yace “Ba

nace kiyi hakuri ba?” Cikin shessheka tace “Dama nace ma Hajja baxan je ba shine ta sa sai naje…” Bai ce mata komai ba sai kallonta yake but he is boiling from inside, mota ce tayi parking dai dai kofar gate aka bude motar Aunty ta sakko da wasu kawayenta suna ta labari, ya dinga kallonsu

har suka shige cikin gida, Jiddah taji hankalinta ya tashi ganin Aunty ta dawo gidan, ta marairaice tana kallonsa tace “Don Allah ko xaka kai ni gidan Umma kilan ta koma gida…” Bai ce komai ba ya bude motar ya sauka ta bi sa da ido ya shiga driver seat ya tada motar ya bar layin, a hanya aka yi ta kiran wayarsa, ya daga daga karshe, calmly yace “Kun ga Ahmad ni ba yaro bane da xa a wani jera dani kafin in shiga gidana, this isn’t my first marriage, my first marriage ma babu wanda yayi min haka, i went home my self, don haka duk sanda nayi niyyar shiga gida xan shiga, yanxu ina wani sabgar ne…” Ahmad yace “Ohh really?” Abuturrab yace “Yes

Ahmad, bana anguwan ma ni” Ahmad yace “To idan kaje gidan sai ka sallami kawayenta…” Abuturrab yace “Sun wahala in dai sallamata suke jira… xa mu yi magana good night” daga haka ya katse wayar, dai dai kofar gidan Umma yayi parking ya kashe motar, Jiddah da taji wani relieve ta bude motar ta sauka tana kallonsa tace “Sai da safe” Daga haka ta shiga gate din gidan ya bi ta da kallo. Gidansa ya wuce daga nan, Aneesah da kawayenta na daki banda complain babu abinda take, Fauziyya tace “Nima ban ta6a ganin haka ba wai kannin ango su wani xo gidan amarya suce xa su kwana ranan da aka kawota, wllh sai kinyi da gaske wajen tattaro hankalin mijinki gaba daya gareki ya share kowa ya daina ganin kowa sai ke, don wnn dangin nasa baxa su bari kiji dadin rayuwar aurenku ba” Aneesah tace “Baxa su bari in ji dadin rayuwar aurena ba??” Wani dariya tayi tace

“Lokacin da shigowa gidan nan xae fara gagaransu xan kira in sanar maku, ni fa Captain da ku ke gani nawa ne ni kadai wllh, haka plan din yake dama” Naja tace “Atoh, dama wa xai xauna ya xuba ido, barin ma miji irin naki, wllh kar kiyi sanya Aneesah… Kowa tashi tsaye yake” Aneesah tace “Ni nasan bani da matsala da yan mata tunda nasan wanene captain, nasan root din matsalata a aurenmu kuma magancesa ba wani big deal bane wllh” Jin an bude kofar parlon duk suka yi tsit, Maimoon ta shigo cikin dakin tana wani cika tana batsewa tana kallonsu Fauziyya tace “Ya Aliyu yace idan kun gama xaman ku fito xa a maida ku can gida” Aneesah ta cire

gyalen kanta da sauri tace “A maida su gida?? Budar kan fa??” Maimoon bata ko kalleta ba ta juya ta fice, Mikewa Aneesah tayi ta fice daga dakin bayan ta daura mayafi a kanta ta sauko downstairs, tsaye ta gansa a parlor, da mamaki tace “My Captain kace xa a maida su Fauziyya gida? As in how?” Yace “Ehh” ta daure fuska tace “Toh wai budan kan fa?” Calmly yace “Duk budewar nan da kika yi ma kan bai yi ba sai wani special one kike jira” Da mamaki take kallonsa, yace “Pls Aneesah I’m tired and i need rest now… idan xa su sakko in ajiyesu tare da su Maimoon su sakko

, or i leave the house duk sanda suka tafi in dawo” Kallonsa kawai Aneesah take, sai ga su Maimoon da Aisha da Nafisa ko warce da jakarta a hannu tana cika tana batsewa suka sakko suka ma Aneesah sai da safe suka fita waje, juyawa yayi ya bi bayansu, ya fi minti goma xaune a mota yana jiran fitowar kawayen Aneesah uku amma shiru shiru, su Maimoon dai na xaune bayan mota, daga karshe ya tada motar ya maida su gida, ko sai da safen kirki Maimoon bata yi masa ba ta shige gate tare da su Aisha, sai a sannan tace “Da nace masa xamu kwana fa daxu bai ce komai ba don har cewa yayi in kai ma Jiddah wayar ita ma ta dawo ta kwana I don’t know what made him Change his mind all of a sudden” Aisha dai sai ta6a bake take

tace “To ba gashi dai mun dawo gidan ubanmu ba” Direct hotel Abuturrab ya wuce yyi lodging daki, sai da ya watsa ruwa sannan ya kwanta bayan ya kashe wayarsa. Har karfe biyun dare Aneesah bata yi bacci ba, bata ta6a xaton haka nata first night din xai kasance ba, yanxu duk abubuwan da aka ce tayi a wannan daren baxata yi ba kenan ya tashi a banxa, gashi tayi ta kiran layukansa duk a kashe, dama rashin mutuncin Aliyu ya kai haka bata sani ba, lallai kamar yanda aka ce mata xama ba nata bane, xaman kuwa ba nata bane, she needs to bring down Aliyu to d level she wants him to be

for her, kawayenta uku na kwance saman gadon sun yi bacci abunsu hankali kwance, mikewa xaune tayi daga karshe ta fita parlor ta xauna tayi tagumi, duk irin burikan da ta ci ma daren nan ya tashi a banxa kenan?? a takaice sai wajen karfe hudu bacci barawo ya sace Aneesah, Washegari da safe aka kawo abinci daga can gidansu Abuturrab, Fauziyya ce ta bude kofar parlon ta amshi abincin a hannun su Safiyya ta kai masu can sama, bayan sun hada shayi me kauri ga uban kwai da dankali a gabansu Fauziyya tace “Wllh ki nuna ma Captain din nan bacin ranki, wacce amarya ce aka ta6a yi ma wnn walakancin da yayi maki, ni ko a tarihi wllh ban ta6a jin haka ba, kar ki kuskura ki amince masa duk dadin bakinsa sai kin gwara kansa shi ma kin rama… Wannan ai walakanci ne wllh, duk wani ango na xumudi a ranan da aka kai masa amarya amma banda naki angon….” Aneesah

dai bata cewa komai amma gaba daya ranta a dagule yake, daga karshe ta mike ta dau wayarta ta fita, wani dakin ta shiga ta kulle ta yi dialing number Aunty, yana fara ringing Aunty ta daga tace “Amarya bakya laifi, har kun tashi? Fatan dai komai normal?” Aneesah ta fashe da kuka, Aunty ta xaro ido ta mike tsaye ta fita daga dakinta don akwai wasu baki, murya can kasa tace “Lafiya Aneesah me ya faru? Da matsala ne?” Cikin kuka

Aneesah ta shiga ba Aunty labarin abinda Abuturrab yayi jiya, Aunty ta saki baki har Aneesah ta kai aya, can tace “Abinda ya maku kenan Aliyun?” Cikin kuka Aneesah tace “Wllh kuwa Aunty, ni da babu kawayena ma da baxan ji wnn kunyan da nake ji ba ynxu, duk fa sun san komai kar suje su yada ni a Abuja, har cewa suke ko a tarihi basu ta6a jin amaryar da aka yi ma wnn rashin mutuncin ba” Aunty da ranta ya dau tafarfasa tace “Shikenan, share hawayenki Aneesah, xan kiraki nan da anjima kadan, kiyi hakuri ko su Mumy kar ki sanar ma kinji!” Aneesah na shessheka tace “Toh” daga haka Aunty ta katse wayar tana wani huci ta hau dialing number Abuturrab taji a katse, rike baki tayi tana naxarin walakancin da xata masa, can tayi wani murmushi hade da kwafa ta koma daki xuciyarta na ci gaba da

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button