JIDDATUL KHAIR 43

6ararraka…. Karfe tara da yan mintuna Jiddah ta fito daga dakinsu sanye da kayan bacci dogo har kasa sai hula a kanta xata shiga kitchen, ita kadai ce a gidan sai Umma da Aunty Nafisah, su ma kuma basu tashi ba, Huraira na can gidansu Ummi bata dawo ba sbda aiki, tun asuba ta tashi ta gyara gidan gaba daya tayi wanke wanke ta share har balcony, ta tafasa ruwan Lipton da ta cika ma kayan kamshi ta juye a flask snn ta koma daki wajen karfe takwas amma bata yi bacci ba, yanxun ma yunwan da take ji ya sa ta fito xata hada shayi, bude kofar parlon taji anyi ta juya da sauri don tun da ta share waje ta shigo bata kulle kofar ba, da d’an mamaki take kallonsa, ya shigo parlon ya kulle kofar, sai da taga ya karaso
cikin parlon ya xauna snn ta duka nan kasan carpet tana kallonsa tace “Ina kwana” har lkcn kayan jiya ne a jikinsa, ta mike don bata san ko ya amsa gaisuwar ko bai amsa ba ta koma daki ta saka hijab dinta snn ta fito ta wuce kitchen, mamakin abinda ya kawosa da sassafe ta dinga yi, ta dai hada shayi ta dau bread slice uku a kan glass plate snn ta fito har xata wuce dakinsu ta juyo taga kallonta yake, ta d’an tsaya tace “Xa a kawo maka shayi ne? Su Umma basu tashi ba” Maimakon ya bata amsa sai taga ya tashi yayi hanyar dakin Ahmad, ita kuma ta wuce dakinsu ta kulle kofar.
Aunty ta rasa me ke mata dadi, ta rasa wanda xata kira tace ga abinda Abuturrab yayi, gashi El-Basheer ma wayarsa a kashe, to ko dai suna tare ne, ita Ahmad ba shiri take da shi ba balle ta kirasa, can dai daga karshe ganin har kusan goma wayar Abuturrab a kashe Kuma bata son Aneesah
ta kira mutan gidansu tace xata sanar masu yasa ta yanke shawaran kiran Ahmad, luckily nasa ya shiga, sai da ya kusa katsewa Ahmad ya mike xaune daga kwancen da yake ya dau wayar mamaki ya kamasa ganin wai Aunty ke kiransa ya daga ya kai kunne, Aunty tace “Ahmad ya gajiya?” Yace “Ina kwana?” Tace “Lafiya lau, Aliyu fa?” Ahmad yace “Aliyu kuma? Ba yana can gidansa ba” Aunty tace “Bai can, kuma ba can ya kwana ba” Bude baki Ahmad yayi, Aunty tace “Kar ka min karya Ahmad, yanxu da gaske bakwa tare?” Ahmad yace “Wllh ni ina gidana, jiya tun karfe takwas muka rabu da shi ina jin” Aunty tace “Toh Shikenan” daga haka ta katse wayar, Ramlah dake gefensa ta kallesa tace “Me ya Aliyun yayi” Ahmad ya daga kafada yace
“Ban san meke damunsa ba, wai bai kwana gidansa ba jiya” Ramlah ta xaro ido tace “Aneesar fa?” Ahmad yace “Tana can gidan i guess” Ramlah ta ma rasa abun cewa, Ahmad yace “Ko aurensa na farko da yaje yayi bai k’i kwana a gidan ba ranan da suka tare balle wannan” Ramlah tace “Toh ko dai Aneesan sun masa wani abu ne” Ahmad yyi dariya bai ce komai ba yana
kokarin kiran layin Abuturrab shi ma ya ji a kashe. Karfe goma Jiddah ta fito ta ajiye cup da ta sha shayi a kitchen sannan ta dau wani cup din ta hada wani shayin, ta ajiye kan tray, kwai kwara uku ta soya da albasa shi ma ta daura a tray din, ta dau ledan slice bread din ta ajiye saman tray, sannan ta dau tray din ta fito, a hankali take tafiya xuwa dakin Ahmad, ta fi minti daya tsaye bakin kofar kamar me contemplating kafin tayi knocking a hankali, jin shiru ta sake kwankwasawa gently, bude kofar dakin aka yi ta koma baya tana kallonsa kamar yanda shi ma yake kallonta…..